KALAMAN HIKIMA BA KOWANE ZAI FAHIMCESU BA SAI MAI HIKIMA.:_
.
Tunda Ake Mutuwa a Duniya Mutum Biyu(2) Ne Kawai Suka Mutu. Daga Wanda Ya Mutu Ya HUTA Sai Wanda Ya Mutu aka HUTA!
.
Duk Haihuwar da Ake a Duniya MutumBiyu (2) Ne Kawai Ake Haihuwa.
DagaWanda Aka Haifa Ya Zama Alkhairi Sai Wanda Aka Haifa Ya Zama Sharri!
.
Duk Yawan Mutanen Duniyar Nan Abinci Kala Biyu (2) Muke Ci. Ko Dai Kaci Abinci ta Hanyar Halal Ko Kuma Kaci Shi Ta Hanyar Haram!
.
Idan Ka Tuna Mutum A Zuciyarka Dole ACikin Abu Biyu (2) Kayi Guda (1). Ko Dai Ka Tuna Alkhairinsa Ko kuma Ka Tuna Sharrinsa!
.
Duk Mutanen Duniya Kowannen Mu Yana Gina daya Daga Cikin Wadannan Gidaje Guda Biyu (2). Daga Wanda Zaiyi Gini a Aljanna Sai Wanda Zaiyi Gini a Cikin wuta!
.
Ya Allah Kasa mu gina namu Gida a cikin Aljanna Firdaus, Ameen.
Monday, 31 October 2016
Kalaman hikima ba kowane zai fahimcesu ba sai mai hikima
Aqidar shi'a dangane da makka da madina
*AQIDAR SHI'A DANGANE DA MAKKA DA MADINA*
الحمد لله والصلاة والسلام على محمد وعلى آله وصحبه وسلم،
Aqidar shi'a dangane da makka da madina aqidace wacce kafirai ma sunfisu saukakawa akai, dan duk kafircin kafiri yasan wadannan gurare suna da falala da daraja,ruwaya daka littafinsu wanda babban malaminsu kuma hujja a'adinin nasu yaruwaito acikin littafinsa
Daka abu baseer daka daya daga cikinsu, yace ((Mutanan makkah sun kafircewa Allah afili, Mutanan madina sunfi mutanen makkah kafirci da lalacewa, sau saba'in wannan magana tana cikin usul kafiy 2/410
Yace dangane da "sham" siriya kenen (( kar kuce ma'abota "sham" sai dai kuce ma'abota zalunci, ma'ana bazaka ce mutanan "sham" ba saidai kace mutanan "zalunci da danniyi, saboda tsabar kiyayyyarsu da sahabbai, sukace Wai Allah yatsine musu tahanyar Annabinsa Dauda, ya maida su birai da aladu, Biharul Anwar 60/208
Sukace tahanyar Ja'afaru ssadeq, Allah yakara masa yarda, karyane yafadi wannan magana, kawai sun jinginata gareshine, (( Mutanan "shaam" sunfi rumawa arna sharri, mutanen madina sunfi mutanen makka sharri, mutanan makka sun kafircewa Allah afili, Usul kahfy 2/409.
Wannan shine dalilin da yasa Iran ta hada kai amunafunce da America da sauran kafurai suke yakar musulunci musamman akasashen Iraqi da Afganistan.
والله أعلم،
***********************************
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.
_*Tambayoyin*_ _*Musulunci*_
_*WhatsApp*_ _*Group*_
Matsalar saurin kawowa (wato rashin dadewa lokacin jima'i)
*MATSALAR SAURIN KAWOWA ( WATO RASHIN DADEWA LOKACIN JIMA'I)*
Rashin sanin hakikanin gaskiyar magana dangane da lokacinda namiji yake iya dauka kafin yayi inzali (wato irin tsawon lokacin) ya kasance abu mai matukar damuwar da yawa daga cikin ma'aurata a wannan zamani. Ya kasance yana saka mazaje da yawa cikin damuwa da rashin walwala sosai gun iyalansu wanda hakan yasa suke ta neman magunguna haukace daga masu bayarda irin wadannan magungunan na gargajiya; ba kadan yake laqumewa mazaje kudi ba. Wannan matsalar tana kasancewa silar son kashe aure ga wasu matan da sunan suje su auri masu daukar tsawon lokaci domin biya musu bukatarsu, wasu matan kuma har yakan zamo silar sabon Allah garesu ta hanyar neman maza a waje wai duk da sunan mazansu basa biya musu bukata. Kuma duk wannan damuwar da wahalolin suna faruwa ne saboda irin yadda mutane suke karantawa a mujallu, social media, littafai e.t.c cewa maza suna daukar tsawon mintuna talatin (30) zuwa sama suna jima'i kafin suyi inzali( kafin maniyyi ya fito musu) wasu kuma suna jin labarai ko gani ne a irin bidiyoyin batsa da Yahudawa maqiya Allah suke shiryawa.
To dan uwa mai cike da damuwa ganin cewa baka daukar tsawon lokaci yayin saduwa da matarka ko kuma malama mai ganin cewa mijinki baya da lafiya kike damuwa duk ku kwantarda hankulanku wancan bayanin dake a sama na mintuna talatin zuwa sama ba gaskiya bane, bayani zaizo daga baya. Abinda bincike daga masana kwararru a wannan fannin ya tabbatar shine:
1. *Mafi yawan maza suna daukar tsawon mintuna 4 zuwa 5 ne ko kuma 5 zuwa 7*. Kuma wadannan mazajen lafiyayyu ne daram.
2. Qalilan sosai ne daga cikin maza *suke iya daukar mintuna 12 zuwa sama suna saduwa da matansu bayan shigarsu*.
3. Su kuma wadanda wannan cutar ta saurin kawowa ke damu to *suna kawowa ne irin seconds 15 zuwa seconds 30 wato dai kasa ga minti 1 kacal bayan sun shigi mace. Wasu ma suna inzali ne tun kafin su shigi matan nasu*. Kuma da zaran sunyi inzali kafin su sake mayarda karfinsu (kafin gabansu ya qara mikewa) wani aiki ne babba.
Sai kuma maganar cewa mazaje suna daukar mintuna 30 zuwa sama ba za'a ce ba'a rasawa ba amma dai mafi yawancin hakan ciwo ne. Sai kuma wadanda suke ji daga masu tallar magunguna, su kuma wadannan suna yi ne dan tallar maganinsu. Wadanda kuma suke kalla a bidiyoyin batsa irin wadanda yahudawa maqiya Allah suke yadawa shi kuma wannan abinda wani fasiqi wanda shi Mai shirya irin wannan batsar ne ya gayawa masu wannan binciken shine *Yadda mutane suke ganin bidiyoyin ba haka abin yake ba. Suna iya daukar watanni suna hada bidiyon. Yace ya kan yiwu shi fasikin wanda ake nunowa yana fasikanci da macen yayi inzali kusan sau biyar ko goma duk a cikin bidiyo guda amma sai su dinga katse wuraren sai subar na karshen kawai. Misali suna iya suzo idan suka fara fasikancin nasu idan yayi inzali sai su tsaya sai kuma wani lokaci idan zasu ci gaba sai su sake dorawa daidai wurinda suka tsaya; kalar kwanciya (position), wurinda suke fasikancin, kalar kaya da komai dai duk iri daya kamar yadda ake hada fim, haka kuma idan ya qara inzali sai su dakatarda daukar sai kuma lokacinda zasu ci gaba hardai sukai tsawon lokacinda suke bukatar kaiwa, sa'annan kuma muna ba jarumman namu kwayoyin kara kuzari*. Kunga kenan indai hakane to suna iya nuna bidiyo mai tsawon awoyi amma shi mai kallon fasikancin sai yaga kamar duk tun lokacinda suka fara fasikancin yine suke bai kawo ba. *Ku kura da kyau wannan fa bincike ne kuma ni na kawo wannan bayanin ne domin wayarda kai tare da kwantarwa da yawa daga cikin yan uwa maza masu ganin cewa kamar basu da lafiya da mata masu ganin cewa mazansu basu da lafiya hankulansu saboda irin yadda suke karantawa ko gani a irin wadannan hanyoyin dake a sama. To kunji yadda suke shirya wannan fasikancin.*
To wasu daga cikin masu rubuce-rubuce akan wannan matsalar wadanda mafi yawancinsu masu tallar magunguna ne suna amfani da irin wannan bayanin ne ba tare da sanin hakikanin gaskiyar lamarin ba domin tallar hajojinsu. Wasu ma sun sani kawai dai dan su tallata kayansu ne ta yadda mutum zai ga lallai baida lafiya bari ya siya maganinsu.
Saboda haka dan uwa mai ganin tamkar baka da lafiya ko wadda take ganin mijinta baya da lafiya har take kokarin rabuwa dashi ko neman wani a waje saboda irin wancan bayanin na karya to ku kwantarda hankalinku karya ne. Haka kuma wanda ma yake fama da wannan rashin lafiyar wato saurin inzali din (rashin dadewa ana saduwa) wato baya iya daukar ko minti daya kacal yana saduwa da iyalinsa to sai ya garzaya asibiti ko wajen masu islamic medicine akwai magunguna kuma suna dan tasiri sa'annan kuma ga wasu 'yan hanyoyi masu taimakawa sosai ga masu wannan rashin lafiyar, harda ma wadanda ke irin mintuna 2 ko 3 haka to duk wannan bincike ya nuna zasu samu ci gaba su haura hakan idan suna bin wadannan hanyoyin. Ga hanyoyin kamar haka:
1. Mutum ya yawaita motsa jiki (exercise)
2. Cin lafiyayyen abinci mai gina jiki da qara lafiyar jiki da kuma yawan cin 'ya'yan itatuwa (Kawai dai aje asibiti domin samun gamsasshen bayani)
3. Yin wasa da gaba a fitarda maniyyi aqallah awa daya kafin fara jima'i da matarka ( *A lura wannan bincike ne a kimiyyance to kuma munsan cewa a musulunce yin wasa da gaba har a fitarda maniyyi haramunne. To amma mafita itace sai ka saka matarka tai maka wannan aikin aqallah awa daya kafin ku fara kaga zaka iya sanyata tai maka bayan kayi inzalin sai ku shiga wanka tare ta yadda dai zaku iya bata lokaci har ayi awar kuna tare kafin fara jima'in, kaga wannan ma duk karin soyayya ne*)
4. Matarka ta dinga yi maka wasa da azzakarinka har sai kaji ka kusan kawowa sai ta dakata, sai gabanka ya tafi kwantawa sai kuma taci gaba ku yawaita yin haka, shima masana sunce yana taimakawa sosai wajen qara tsawon lokaci yayin saduwa.
5 Ku dinga yin wasa sosai da matarka gabanin ka shigeta ta yadda koda kayi saurin inzalin to ita matar zata iya samun biyan bukatarta daga wadannan wasannin.
6. Haka kuma akwai irin taimakawar da ita macen zata dinga yi yayin saduwar. Kamar lokacinda kuke jima'i idan kaji ka kusa kawowa sai ka cire ita matar tayi sauri ta dan matse kan azzakarinka ta yadda sha'awarka zata dan gushe. Haka kuma kasancewar matarka a samanka shima wannan yana taimakawa sosai. (Wannan dai idan mai fama da rashin lafiyar yaje asibiti duk zai samu cikakken bayani)
To da yardar Allah masana wannan fannin sunce idan mai fama da wannan rashin lafiyar yana yin haka zai samu canji sosai. Haka kuma wadanda suke yin irin mintuna 2 ko 3 haka suma idan suna bin wadannan matakan to lokacinsu zai karu sosai kamar zuwa 4 zuwa 5 haka. Allah ya kara mana lafiya da abinda lafiya ke bukata.
+2348164884055.
+2347068043652.
*Tambayoyin Musulunci*
*WhatsApp Group*
Sunday, 30 October 2016
Ya hukuncin wanda yake sallah wasu raka'o'i yayi qabdu wasu kuma yayi sadalu??
YA HUKUNCIN WANDA YAKE SALLAH WASU RAKA'O'I YAYI QABDU WASU KUMA YAYI SADALU
الحمد لله على المبعوث رحمة للعالمين صلى الله عليه وعلى آله وصحبه ومن سار على نهجهم إلى يوم الدين
Alal hakika yasabawa koyarwar manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam, domin Allah ya umarcemu dakoyi da Annabin tsira muhammad salallahu Alaihi wasallam, cikin dukkan al'amuranmu narayuwa da addini da zamantakewa inda yace:
(لقد كان لكم في رسول الله أسوة حسنة لمن كان يرجوالله واليوم الآخر) الأية
Hakika abun koyi kyakkyawa yakasance agareku cikin al'amuran manzan Allah, ga wanda yake fatan samun yardar Allah da kuma tsira ranar alkiyama.
Shi kuma manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam ya umarcemu da muyi sallah kamar yanda aka ruwaito mana yana yi inda yace:
(صلوا كما رأيتموني أصلي).
Kuyi sallah kamar yanda ku kaga inayi.
Acikin bayanin yanda manzan Allah yake sallah babu inda yake qablu awasu raka'o'in wasu kuma yayi sadalu.
Dan haka wannan kuskurene wanda baidace musulmi yake aikatawa ba Annabi sallallahu Alaihi wasallam yace:
(إنا معشر الأنبياء أمرنا بتأجيل فطرنا وتأخير سحورنا وأن نضع أيمننا على شمائلنا في الصلاة.
Mu taran Annabawa Allah ya umarcemu da gaggauta buda baki in munyi azumi dazarar rana tafadi, mukuma jinkirta sahur dinmu daf da fitowar alfijir, mu kuma dunga sanya hannayenmu nadama akan hagu dinmu acikin sallah.
Danhaka Qabdu a sallah gaba dayanta farillah, dana fila ta idi da ta jana'iza, data rokon ruwa dama duk wata sallah shine dora dama akan hagu bawai chakudawa ba.
والله أعلم،
***********************************
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.
_*Tambayoyin*_ _*Musulunci*_
_*WhatsApp*_ _*Group*_
Saturday, 29 October 2016
Menene hukuncin daura laya shin ta dace
MENENE HUKUNCIN DAURA LAYA SHIN TA DACE.
الحمد لله وحده والعاقبة للمتقين ولا عدوان إلا على الظالمين.
AMSA: Daka Abdullahi dan mas'ud Allah kara yarda dashi yace: Annabi sallallahu Alaihi wasallam ya kasance yana kin abubuwa guda goma, wani turare mai launin fatsi fasti, da chanza furfura, da zantufafi akasa, da sanya zoben zinare, da dukan kunci, mari, da bayyana ado ga mata a inda ba wajan bayyana shiba, dayin ruqya inba da falaqi da nasi ba, da sanya maniyyi a inda bai kamata ba, zina kenan, da saduwa da mai shayarwa,.
Wannan hadisi shaik albany ya raunana shi acikin za'ifan hadisin sunan nisa'i (3075).
Daka zainab matar Abdullahi dan mas'ud daka Abdullahi yace: Naji manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam yana cewa Lallai ruqya irin ta jahiliyya da kuma layu da tiwala "shine buda kaulasan ko takuri kowani harafi na kalmar alqur,ani asanya sunayen wadan za'a mallake, shirkane, sai tace : sai nace: saboda me kafadi haka,? wallahi idona yakasance ya naimin ciwo ina zuwa wajan wani mutum bayahude yaimun ruqya idan yamin ruqya sai yadena ciwo, sai Abdullahi yace: Wannan aikin shaidan ne shine yake tsone miki idan da hannunsa idan bayahuden yai miki ruqya sai yadena tsone miki, ya isheki kifadi irin abunda Annabi sallallahu Alaihi wasallam yakasance yana fada, " Allah katafiyar da cuta ya ubangijin mutane kawarkar dani, kaine mai warkarwa, warkarwar da babu sauran cuta.
Abu dauda (3883) da ibnu majah (3530).
Albany ya ingantashi acikin silsila sahiha (331) da (2972).
Daka uqubata dan Amir yace: Naji manzan Allah sallallahu alaihi wasallam yace: " Duk wanda ya rataya laya kada Allah yacika masa burinsa, duk wanda ya rataya daga kada Allah yacika masa burinsa " imamu Ahmad ya ruwaito (16951).
Shaik Albani rahimahullah ya raunana hadisin acikin Za'iful jami'i (50703).
Daka uqubata bin amir aljuhany yace manzan Allah sallallahu alaihi wasallam wasu mutane goma sunzo wajansa sai yai muba'aya da mutane tara yaki mubaya'a da dayan, sai sukace: ya manzan Allah kaiwa mutum tara mubaya'a ka kyale daya sai yace: akwai laya atare dashi, sai yasa hannunsa ya cirota ya tsinkata, sai yayi masa mubaya'a sai yace: Duk wanda ya rataya laya hakika yayi shirka. Imamu Ahmad (16969).
Shaik Albany rahimahullah ya inganta shi, acikin littafinsa silsila sahiha (492).
Laya itace abunda ake ratayawa yara ko manya su sanya ajikinsu ko asanya agida ko mota ko rumfar sana'a wata ta itatuwa da wasu ababe wata kuma dakashi ake hadasu dan kare sharri ko janyo amfani.
Malamai daka sahabbai databi'ai sunyi sabani wajan rataya layar da aka rubuta ayar alqu'ani kawai, wasu sukace indai ta qur'ani ce kawai ta halatta, wasu kuma sukace koda ta qur'ani ce bata halattaba saboda hadisin daya ce " duk wanda ya rataya laya yayi shirka" baice banda ta qur'ani ba.
Wannan magana kuma itace tafi karfi tafi fitowa fili saboda toshe hanyar barna, itace kuma mafiya yawan sahabbai suke akanta kamar Abdullahi dan Abbas da Abdullahi dan mas'ud da sauran malaman tabi'ai dama na wannan zamanin.
Malaman majaslisar ilmi da fatawa na kasar saudiyya sukace:" Malamai sunyi ittifaqi akan haramcin sanya laya da guru idan dai bata ayar qur'ani bace, sunyi sabani akan wacce akai da ayar alqur'ani kawai, daka cikinsu akwai wadanda suka halatta ta qur'ani zallah, daka cikinsu kuma akwai wadanda suka haramta harta alqur'anin, Amma fatawar haramcin harta alqur'ani itace mai rinjayen dalilai saboda gamewar da hadisai sukazo da ita na fadin kowacce laya basu kebe wacce take ta alqur'ani ba, da kuma to she hanyar barna.
Fatawa lajnatul da'imah (1/212).
والله أعلم،
***********************************
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.
_*Tambayoyin*_ _*Musulunci*_
_*WhatsApp*_ _*Group*_
Shin ya matsayin sadaka da akeyi wajen mutuwa misali uku bakwai arba'in
SHIN YA MATSAYIN SADAQA DA AKEYI WAJEN MUTUWA MISALI UKU BAKWAI ARBA'IN
الحمد لله والصلاة والسلام على محمد وعلى آله وصحبه وسلم
AMSA: Malamai sunyi ittifaqi akan cewa sadaqa da nemawa mamaci gafara da hajji duk suna isa zuwa ga mamaci.
Dalili akan addu'a da istigfari shine fadin Allah madaukakin sarki
(والذين جاؤوا من بعدهم يقولون ربنااغفرلنا ولإخواننا الذين سبقون بالإيمان)
Wadanda sukazo abayansu zasu dunga cewa ya ubangijinmu kagafarta mana damu da 'yan'uwanmu dasuka rigayemu da imani.
Manzan Allah sallahu Alaihi wasallam yace: ( kunemawa dan'uwanku gafara, ku roka masa tabbatuwa domin yanzu za'a tambayeshi)
yasake cewa : ( Idan zakuyiwa mamaci sallah ku kyautata addu'a gareshi)
Amma sadaka ya tabbata acikin bukhari daka ubadah bin sabit yardar Allah takara tabbata agareshi, mahaifiyarsa ta rasu baya gari yace: ya manzan Allah mahaifiyata ta rasu bana nan shin innai mata sadaka zata amfaneta, sai manzan Allah yace: eh, sai ubada bin sabit yace: ina shaida maka gonata mai 'ya'yan kayan marmari na badashi sadaka agareta. bukhary (2756).
Amma aikin hajji kuwa Manzan Allah sallalllahu Alaihi wasallam yace: da matar data tambayeshi shin zan iya yiwa mahaifiyata aikin hajji bayan ta mutu? sai yace; shin inda bashine akanta zaki biya mata, sai tace : eh sai Annabi yace bashin Allah shine yafi cancanta abiya.) Bukhary 6699 muslim 1148.
Wadannan dalilai sun nuna sadaqa tana amfanar wanda ya mutu kuma ladanta zai isa gareshi.
Ansamu hadisi mai rauni wanda yake nuna ya halatta cewa idan kaiwa mamaci sallah ladan zaije gareshi, sai dai imamu muslim yace hadisine mai rauni acikin mukaddimar littafinsa ingantacce daka Abdullahi bin mubarak, sannan imamu muslima yace babu sabani akan sadaka.
Amma azumi da sallah amazhabar shafi'iyyah da jamhur din malamai ladansu baya kaiwa ga wanda ya mutu, sai dai idan azumin nawajibine mamaci ya mutu ana binsa to waliyyinsa zai rama masa ko kuma wanda mamacin yaiwa izinin ya rama masa kafin rasuwarasa.
Imamun nawawy acikin tuhfatul muhtaaj yace: " mamaci zai amfana da sadakar da akai masa daka ciki akwai kana iya sayen alqur'ani kakai masallacin daza'a dunga karantasu ko makaranta amtsayin wakafi ga mamacin, ko ka haka rijiya inda ake bukatar ta amatsayin wakafi ga mamaci, koya dasa bishiya zaidunga samun ladanta matukar ana amfana da ita, ko kuma wani yadasa bishiyar amatsayin wakafi ga mamacin.
Amma mafificiyar hanyar da mamaci zai amfana da wani abu dazakai mar shine kayawaita masa addu'ar Allah yagafarta masa, ko ka gina masallatai a inda ake bukatarsu da rayasu da ilmi, ko taimakawa dalibai tahanyar biya musu kudin makaranta ko buga littattafai dansu amfani dasu.
Amma taruwa da'ake bayan kwana uku da mutuwar mamaci a karanta alqur'ani ko adauki dukiyar marayu ayi abunci da sunan sadaka ga mamaci, wannan bidi'ane kuma cin dukiyar marayuce batare da hakki ba, Allah kuma yaharamta cin dukiyar marayu, haka ta arba'in haka ta shekara wadannan duk bidi'o'ine Allah bai saukar dawata hujja akai ba.
Kawai kai kadai kaiwa mamaci addu'a kadauki dukiyarka ta kanka halaliyarka kayi sadaqa da ita da nufin Allah yakai ladan ga mamaci wannan shine zai isa ga mamaci kamar yanda dalilai suka gabata, shima kuma batara mutane akace kaiba, zakayi batare ma dakowa ya sani ba wannan shine sunnah.
والله أعلم،
***********************************
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.
_*Tambayoyin*_ _*Musulunci*_
_*WhatsApp*_ _*Group*_
Friday, 28 October 2016
Hukuncin yan kasuwa masu qarin farashi
HUKUNCIN 'YAN KASUWA MASU QARIN FARASHI
TAMBAYA TA 2011
********************
As-salamu Alaikum malam mai zauren fiqhu godiya da Fatan Alkhairi A gareka Allah yakara daukaka ga wannan zauren Naka,
Malam ina son nayi tambaya ce Akan yanayi ta kasuwanci domin ni ina kasuwanci ne ina saye da sayarwa sai Naji ance abinda Nike sayarwa ya samu karin kudi Daga kasuwa ko Daga kamfani shin ya halitta nima nayiwa nawa ababan da Nike sayarwar karin kudi domin in zanje kasuwa sai nayi cikon kudi ba zan tsameshi kamar yadda Nike sayarwa in banyi karin kudin ba, Allah yabada ikon amsa
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Irin wannan abinda kake tambaya akansa, bai halatta ba. Abinda ake so ga dan kasuwa shine ya zamanto Mai gaskiya mai son gaskiya, kuma mai aiki da gaskiya acikin dukkan harkokinsa.
Abu Sa'eed Alkhudriy (rta) yace Manzon Allah (saww) yace : "DAN KASUWA MAI GASKIYA, MAI AMANA, YANA TARE DA ANNABAWA DA SIDDIQAI DA SHAHIDAI (ARANAR ALQIYAMAH KENAN).
(Imam Tirmidhiy ne ya ruwaitoshi acikin kitabul buyu'i kuma ya ingantashi).
Wani hadisin kuma daga Isma'il bn Ubaid bn Rifa'ah, daga babansa daga Kakansa (rta) yace Ya fita zuwa wajen Sallah tare da Manzon Allah (saww) sai Manzon Allah (saww) yaga mutane suna ta cinikayya atsakaninsu.
Sai yace "YA KU TARON ATTAJIRAI!!". Sai suka amsa kiransa, suka 'daga kayuwansu da idanuwansu gareshi. Sai yace :
"HAKIKA SU 'YAN KASUWA ZA'A TASHESU NE ARANAR ALQIYAMAH AMATSAYIN FAJIRAI. SAI DAI WANDA YAJI TSORON ALLAH, YAYI BIYAYYA, KUMA YAYI GASKIYA".
(Tirmidhiy ne ya ruwaitoshi).
Don haka abinda yafi gareka shine ka saukaka ka bayyanar da gaskiya. Duk lokacin da ka koma domin sayowa, idan ka samu anyi Qarin kudi kaima sai ka Qara. Amma idan ka tarar anyi ragi kaima sai ka rage.
Annabi (saww) yayi addu'a yace : "ALLAH YAJI QAN MUTUM MAI SAUKAKAWA IDAN ZAI SAYI ABU, MAI SAUKAKAWA IDAN ZAI SAYAR.... ".
Idan kayi haka in sha Allah zaka shiga cikin addu'ar Manzon Allah (saww). Kuma zaka samu albarka mai yawa acikin kasuwancinka.
WALLAHU A'ALAM.
ZAUREN FIQHU
Ka/ki kiyaye raka'o'i 12 domin samun gida a aljannah
KA/KI KIYAYE RAKA'O'I 12 DOMIN SAMUN GIDA A ALJANNAH..
Assalamu alaikum malam dan allah ina son ayimin bayanin yadda nafilolin da ake yi kafin sallah da kuma bayan sallah suke da kuma falalarsu wslm?
Amsa:
الحمد لله
Malaman fiqhu sunyi bayanin cewa sallolin nafila na rana a asirce ake yinsu, su kuma sallolin nafila na dare a bayyane ake yinsu. Amma sallar bayan maghrib (ba'ad maghrib) da kuma raka'atanil fajr kana iyayi a bayyane ko a asirce. Hujja kuwa itace; Hadisin da Ibn Majah da Tirmizi suka ruwaito daga Abdullahi Dan Mas'ud (Allah ya yarda dashi) yace yaji abinda Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam yake karantawa a sallar bayan Maghrib da kuma nafilar sallar al-fijr. Kenan wannan ya nuna manzon Allah sallallahu alaihi wasallam yana yi a bayyane shi yasa har Dan Mas'ud yaji abinda yake karantawa.
Haka kuma akwai hadisi wanda Uwar muminai A'isha (Radiyallahu anha) ta ruwaito cewa Annabi (sallallahu alaihi wasallam) ya kasance yana karanta Fatiha ne kadai acikin raka'atanil fajr, kuma yana yinta ne a asirce.
Saboda haka dai su sallolin Ba'ad maghrib wato sallar bayan maghrib da kuma raka'atanil fajr kana iya yinsu a bayyane ko asirce, kuma yana da kyau ma ka rinka yi kana canzawa; yau kayi asirce gobe kayi a bayyane.
Sai kuma dangane da fafalarsu; to kowace daga cikin sallolin nafilolin tana da nata falala wadda ita kadai take da ita kuma. Amma kuma akwai hadisi wanda ya nuna mana falalarsu a jimlace. Imam Muslim ya ruwaito hadisi daga Ummu Habeebah (Allah ya yarda da ita), matar Annabi (sallallahu alaihi wasallam) tace: Naji manzon Allah (sallallahu alaihi wasallam), yace: " Ba wani Musulmi wanda zai kiyaye yin raka'o'i 12 na nafila kowace rana, bayan yayi na farillah face Allah bai gina masa gida a aljannah ba"...
A wata ruwayar hadisin kuma wanda Tirmizi (415) ya ruwaito daga ita din Ummu Habeebah(Allah ya yarda da ita) tace: Manzon Allah (sallallahu alaihi wasallam) yace: " Duk wanda ya kiyaye yin raka'o'i goma sha biyu (12) a dare da rana, to za'a gina masa gida a cikin Aljannah: raka'a hudu kafin zuhr da kuma raka'a biyu bayanta, raka 2 bayan maghrib da kuma raka'a biyu bayan Isha'i sai kuma raka'a biyu kafin sallar subhi" Sheikh Albani ya ingantarda hadisin a cikin Saheeh Sunan at- Tirmizi.
Saboda haka dan uwa ko yar uwa da fatan zamu kiyaye yin wadannan sallolin nafilolin domin samun gida a Aljannah. Allah yasa muna cikin wadanda zasu tsinci kansu a aljannah Firdaus.
Wallahu a'alam
سبحانك اللهم وبحمد ك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.
Tambayoyin Musulunci
WhatsApp group
+2348164884055
+2347068043652
Wednesday, 26 October 2016
Rayuwarmu a yau kenan
*RAYUWARMU A YAU KENAN*
Ko ka taba karanta _*English Version*_ na irin wannan labari, ka dan daure karanta wannan akwai wani dan qarin bayani a ciki....
Wata rana wata malamar Lissafi (Mathematics Teacher) ta shigo aji sai ta rubuta wannan rubutun dake a qasa akan allo..
_*9×1=7*_
_*9×2=18*_
_*9×3=27*_
_*9×4=36*_
_*9×5=45*_
_*9×6=54*_
_*9×7=63*_
_*9×8=72*_
_*9×9=81*_
_*9×10=90*_
Bayan ta kammala rubutunta, koda ta juyo ta kalli dalibanta tuni aji ya kacame da dariya suna nuna mata hannu akan allo saboda wancan kuskuren da tayi na farkon wanda ta sanya _*9×1=7*_ a maimakon _*9×1=9*_ wanda yake shine daidai.
Sai malamar tayi murmushi tana mai gaya musu cewa:
_*" Ai dama nayi haka ne da gangan ( a sane ) saboda inason ku koyi darasi daga wannan kuskuren nawa"*_
Wannan zai zamo darasi gareku kusan cewa haka mutane ke biye daku. Yanzu ku duba ba tare da duba da irin wahalar da nake yi daku ba wajen koya muku wannan lissafi har kuka iya, ban taba yi muku kuskure ba sa'annan kuma a wannan rubutun kadai na rubuta amsoshi guda tara *_9*_ gaba dayansu daidai, sa'annan kuma baku yi la'akari da cewa wadannan amsoshin guda tara gaba dayansu sunfi waccan amsar ta farko wuya ba kuma duka nayi su daidai amma a cikinku ba wanda ya jinjina min sai wannan kuskuren shi kawai kuka gani kuma kuke dariya da tuhumata akansa.
Lallai ina mai qara jaddada muku ku sani wannan babban qalubale ne zuwa gare ku, haka rayuwar take.......
Mutane ba zasu taba gode ko jinjina maka ba a duk dimbin miliyoyin ayukan alkhairi da kayi, amma kuma zasu saka maka ido tare da zargin/tuhuma akan kuskure qwaya daya kacal da kayi. _*AMMA FA KADA KU KARAYA SABODA WANNAN*_
_*SABODA HAKA A KULLUM IDAN KA MIQE ZUWA AIKATA ALKHAIRI TO KA KAUDA KAI DAGA DARIYA, ZARGI DA KUMA TUHUMAR MUTANE. KADA KA NEMI GODIYA, JINJINAWA KO SAKAYYAR MUTANE. KAWAI DUK ABINDA ZAKA YI TO KAYI DAN ALLAH. KUMA KA NEMI TSARI DA GAFARA DAGA GARE SHI SABODA SHI YANA GANIN DAIDANKA KUMA YANA GANIN KUSKURENKA.*_
_*Idan kuma kace kana jiran godiya da sakayya daga mutane babu shakka za ka sha mamaki kuma idan aikin lada ne kake yi zaka rasa ladar, kaga ka tashi a tutar babu kenan.*_
_*YA ALLAH KA QARA KYAUTATA MANA NIYYOYINMU*_
_*YA ALLAH KA KARBI AYUKANMU NA ALKHAIRI KA YAFE MANA KURA-KURANMU*_
*Tambayoyin*_ _*Musulunci*_
_*WhatsApp*_ _*Group*_
Ya mutun zayyi ramuwar sallar daya manta bayan lokacin wata ya shigo??
*YA MUTUM ZAYYI RAMUWAR SALLAR DA YA MANTA BAYAN LOKACIN WATA YA SHIGO??*
Aslamu alaikum warahamatull lahi taala wabara katuhu malan ya mutum zaiyi ramuwar sallah wadda baiyi bah a baya
الحمد لله والصلاة والسلام على محمد وآله وصحبه وسلم.
AMSA:Dafarko kafin mu amsa tambayar zamuyi wani bayani dazai bada haske akan ramuwar sallar da mutum yamanta ko kuma takubuce masa baiyiba.
Hukuncin jeranta sallolin dasuka riga suka wuce mutum bai yiba.
Malaman mazahabobi guda uku Abu hanifa, Ahmad, Malik. suntafi akan wajabcin jeranta sallolin da suka wuce, yayin ramasu, dalili akan haka shine manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam ya rama wasu sallar data wuce masa ajere alokacin yakin kandaq.
Imamul bukhari ya ruwaito hadisi(641) da muslim(631). daka jabir dan Abdullahi manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam ya rama sallar la'asar data wuce baiyi taba aranar yakin kandaq, bayan rana tafadi, sannan sai yayi magriba bayan ya rama la'asar,
haka kuma bukhary ya ruwaito (631) Manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam yace ( kuyi sallah kamar yadda kukaga inayi. Almugny(2/336).
Idan mutum ya manta jerantawar wajan ramuwa shin jerantawar tafadi akansa?
Na'am idan mutum ya manta jeranta salloli wajan ramasu jerantawar tafadi akansa, saboda fadin manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam yace:(Allah madaukakin sarki yadaukewa al'ummata abunda suka aikata bisa kuskure bada niyyah ba, dakuma abunda suka aikata bisa mantuwa da kuma abunda aka tursasau akai) Ibnu majah (2043) Albany ya ingantashi acikin sahihu ibnu majah (1662) kuma wannan itace mazhabar limamai biyu Abu hanifa da Ahmad Allah yai musu rahama.fat hul qadeer(1/424). da Almugny (2/340).
Duk wanda yamanta sallah har lokacin wata ya shigo,yana da halaye guda uku
1-ya tuna sallar data wuce masa kafin ya shiga wacce lokacin tane, awannan lokacin wajibine yafara yin wacce ta wuce kafin yin wacce lokacin tane.
2-Ya tuna ana binsa sallar data kubuce masa bayan ya kammala wacce take alokacin ta, to sallar dayayi wacce take alokacin ta tayi, sai yarama wacce ake binsa abayanta, saboda yana da uzurin rashin jerantawa da mantuwa
3-Ya tuna ana binsa sallar data wuce akansa yana cikin yin wacce lokacinta yake, awannan hali zai cika wacce lokacinta yake nan saita zamto masa amatsayin nafila, sannan sai yayi wacce ake binsa, sai yasake wacce take alokacinta saboda kiyaye jerantawa, wannan itace mazhabar imamu Ahmad Rahimahullah Almugny (340-2/336).
itace maganar Abdullahi bin umar Yardar Allah takara tabbata agaresu.
Imamu malik ya ruwaito acikin muwaddah, daka nafi'u cewa Abdullahi dan umar yana cewa: wanda ya manta sallah bai tuna ana binsa sallah ba saida yana cikin bin liman a wata sallar, idan liman yayi sallama, sai yayi sallar data wuce masa yasake wacce yayi tare da liman.
Shaikul islam ibnu taimiyyah Rahimahullahu yace:( Duk lokacin da mutum ya tuna ana binsa wata sallah yana cikin yin wata zai kasance kamar baifara yin wacce take alokacinta ba, Amma dazai tuna ana binsa sallah bayan yagama wacce take alokacinta, to wacce yayi alokacinta ta isar masa awajan mafiya yawan malamai kamar Abu hanifah, da shafi'i da Ahmad.)Fatawal kubra (1/112).
Cewa da akayi zai cika wacce yake alokacinta mustahabbine ba wajibiba da zai yanke wacce yake alokacinta, yayi wacce ake binsa sannan yayi wacce take alokacinta hakan ya isar masa.
Wasu malaman suntafi akan cewa zai karasa wacce yake alokacinta bazai sake maimaita taba, sannan sai yayi wacce ake binsa, wannan shine mazhabar imamul shafi'i, kamar yanda yazo Acikin Al majmu'u (3/70).
kuma shine zabin uthaimeen rahimahullah, kamar yanda yazo acikin fatawarsa(12/221). Maganar farko ita tafi daidai.
Idan mun fahimci yanda ake rama sallar data kubucewa mutum da mantuwa ko wani dalili karbabbe ashari'a, to ga yanda zai rama din kuma shine muka dan fadada bayani asama.
والله أعلم،
***********************************
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.
_*Tambayoyin*_ _*Musulunci*_
_*WhatsApp*_ _*Group*_
Dalilan dake sa a hade salloli
DALILAN DAKE SA A HADE SALLOLI...
assalamu alaiku malan ya halatta wusu lokutta ahade magariba da isha to malan wadanni lokuttane allah ya kara sani.
AMSA:
الحمد لله
Wa'alaikumus salam..
Ana hade salloli azzahar da Asr, da kuma maghrib da Isha'i saboda dalilai kamar haka
Lokacin hajji: A arafah mutum zai hade zuhr da asr a yayi su lokacin zuhr. Haka kuma zai hade maghrib da isha'i yayi su a lokacin isha'i a Muzdalifah. #Hadis
Matafiyi: Idan akwai wahala ga matafiyi idan yace zai yi kowace sallah a lokacinta to zai iya hadewa. #Hadisai masu dama sun nuna haka sa'annan kuma
ﻳُﺮِﻳﺪُ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺑِﻜُﻢُ ﺍﻟْﻴُﺴْﺮَ ﻭَﻟَﺎ ﻳُﺮِﻳﺪُ ﺑِﻜُﻢُ ﺍﻟْﻌُﺴْﺮَ
[al-Baqarah 2:185]
Idan ana ruwan sama.. Sunnah ce a hade salloli; zuhr da la'asar, maghrib da isha'i #Hadis
Rashin lafiya mai tsanani: Ya halatta idan yin sallah kowace lokacinta ga majinyaci akwai wahalarwa to ya hade sallolin. #Hadis da kuma ayar qur'ani
ﻳُﺮِﻳﺪُ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺑِﻜُﻢُ ﺍﻟْﻴُﺴْﺮَ ﻭَﻟَﺎ ﻳُﺮِﻳﺪُ ﺑِﻜُﻢُ ﺍﻟْﻌُﺴْﺮَ
[al-Baqarah 2:185]
Sai kuma sallah a cikin jirgin ruwa ko jirgin sama, tarago etc... #Hadis kuma
ﻳُﺮِﻳﺪُ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺑِﻜُﻢُ ﺍﻟْﻴُﺴْﺮَ ﻭَﻟَﺎ ﻳُﺮِﻳﺪُ ﺑِﻜُﻢُ ﺍﻟْﻌُﺴْﺮَ
[al-Baqarah 2:185]
6. Sa'annan mutane suna iya hade sallolin a duk wani lokaci na tsanani, rudani ko wahala idan har yinsu kowace lokacinta zai saka su cikin tsanani ko wahala.
ﻻَ ﻳُﻜَﻠِّﻒُ ﺍﻟﻠّﻪُ ﻧَﻔْﺴًﺎ ﺇِﻻَّ ﻭُﺳْﻌَﻬَﺎ
[al-Baqarah, 2: 286]
ﻳُﺮِﻳﺪُ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺑِﻜُﻢُ ﺍﻟْﻴُﺴْﺮَ ﻭَﻟَﺎ ﻳُﺮِﻳﺪُ ﺑِﻜُﻢُ ﺍﻟْﻌُﺴْﺮَ
[al-Baqarah 2:185].
Wallahu a'alam
سبحانك اللهم وبحمد ك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.
Tambayoyin Musulunci
WhatsApp group
+2348164884055
+2347068043652
Abinda ake so wanda yaji kiran sallah yayi daga lokacinda yaji kiran sallah har izuwa iqamah
*ABINDA AKE SO WANDA YAJI KIRAN SALLAH YAYI DAGA LOKACINDA YAJI KIRAN SALLAH HAR I ZUWA IQAMAH*
Assalamu alaikum
Malam dan Allah ina so amin bayani akan yanda ake amsa kiran Sallah
Nagode
وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ
_*AMSA:*_
*******
Da farko dai abinda ake son wanda yaji kiran sallah yayi shine: Maimata wato fadin irin abinda duk ladan ya fada. Amma wajenda ladan ke cewa:
*ﺣﻲ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺼﻼﺓ*
*"Hayya alal Salah"*
da
*ﺣﻲ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻔﻼﺡ*
*"Hayya alal falah"*
Anan sai ace
*ﻻ ﺣﻮﻝ ﻭﻻ ﻗﻮﺓ ﺇﻻ ﺑﺎﻟﻠﻪ*
*"La haula wala quwwata illa billah"*
[Bukhari da Muslim 385]
Idan kuma mai kiran sallah ya kammala kiran sallah sai kace:
*"Ashhadu an la'ilaha illallah wahdahu la sharika lahu, wa anna Muhammadan abduhu wa rasuluhu, raditu billahi rabban, wa bi Muhammadin rasulah, wa bil islami dinan"* [Muslim]
Bayan wannan sai mutum yayi wa Annabi sallallahu alaihi wasallam salati:
Daga Jabir (Allah ya yarda dashi) yace: Annabi (sallallahu alaihi wasallam) yace: "Dukkan wanda yace a lokacinda yaji kiran sallah:
*ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺭﺏ ﻫﺬﻩ ﺍﻟﺪﻋﻮﺓ ﺍﻟﺘﺎﻣﺔ ﻭﺍﻟﺼﻼﺓ ﺍﻟﻘﺎﺋﻤﺔ ﺁﺕ ﻣﺤﻤﺪﺍ ﺍﻟﻮﺳﻴﻠﺔ ﻭﺍﻟﻔﻀﻴﻠﺔ ﻭﺍﺑﻌﺜﻪ ﻣﻘﺎﻣﺎ ﻣﺤﻤﻮﺩﺍ ﺍﻟﺬﻱ ﻭﻋﺪﺗﻪ*
*"Allahumma Rabba hazihid da'watit tammat wassalatil qaimati, ati Muhammadan waseelata wal fadeelata, wab'athhu maqaman mahmoodal lazi wa'adtahu"*
Cetona ya halatta akansa ranar alqiyamah". [Bukhari, 589]
Wato duk wanda aka gama kiran sallah yayi wannan addu'ar zuwa ga Annabi (sallallahu alaihi wasallam) dake a sama to cetonsa ya halatta a gare shi ranar qiyamah. Allah yasa muna daga cikin wadanda zai ceta.
Sai kuma tsakanin kiran sallah zuwa tada iqamah ana son mutum yayi addu'a saboda ana amsar addu'a a wannan tsakanin. Daga Anas (Allah ya yarda dashi) yace: Annabi (sallallahu alaihi wasallam) yace:
*Haqiqa ba'a mayarda addu'a tsakanin kiran sallah da iqamah, saboda haka kuyi addu'a*. [Tirmizi 212, Abu Dawud 437, Ahmad 12174]
والله أعلم،
***********************************
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.
_*Tambayoyin*_ _*Musulunci*_
_*WhatsApp*_ _*Group*_
Friday, 21 October 2016
Maganin waswasin fitsari
MAGANIN WASWASIN FITSARI
TAMBAYA TA 2003
********************
Asaalamu Alaikum malam Allah saka da Alkhairi a bisa taimakon da kake mana kullum Allah saka da Alkhairi malam ina fama da matsalar dake damuna idan nayi tsarkin fitsari zan tsaya in matse in karkade kamar dai yanda malaman fiqhu sukai bayani toh Amma malam duk da haka wani lokaci sai inji kamar wani ya biyo mani cikin wando kuma sai in koma kewaye idan na koma kewaye kuma sai inga gaka din nasha maganin baturen amma dai baiyi ba shine nake so ka taimaka mani da maganin da zanyi Amfani dashi
Wassalamu Alaikum.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Shi irin wannan waswasin ana iya maganceshi ne ta hanyoyi da dama kamar haka :
1. Ka tabbatar kayi addu'ar shiga bandaki tun kafin ka shiga. Sannan ka shiga da Qafar Haggu.
2. Ka tabbatar ka gama biyan bukatarka kafin ka tashi.
3. Ka tabbatar kayi nishi sosai domin fitar da sauran abinda ke cikinka na najasa.
4. Ka tabbatar ka karkade, kuma ka matse cikin tausasawa. Kada ka chutar da kanka.
5. Idan kuma kana da larurar da fitsari ba ya gama fita daga jikinka cikin hanzari, to zaka iya mikewa tsaye kadan, sannan ka sake tsugunnawa ka sake matsewa.
6. Daga cikin Maluman Fiqhu, akwai wadanda suke ganin cewar zaka iya mikewa har kayi tattaki kamar taku daya zuwa biyu sannan ka sake dawowa ka tsugunna.
7. Daga karshe ina baka shawarar cewa ka yawaita amfani da shayin Na'a-na'a wanda aka matsa lemon tsami acikinsa. In sha Allahu zaka samu lafiya daga wannan matsalar.
Allah ya sawwake. Allah shi baka lafiya.
WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU
Ya hukuncin wanda yai magana ko danna waya a lokacin da liman ke huduba ranar jumu'a??
*YA HUKUNCIN WANDA YAI MAGANA KO DANNA WAYA A LOKACIN DA LIMAN KE HUDUBA RANAR JUMA'A.??*
AMSA:Wanda yai magana ranar juma,a ko wasa, ko danna waya, ahalin liman yana huduba, babu shakka yayi laifi wato yayi lagawu wato yashasshen zance na wargi.
Domin shi sauraren huduba ranar juma,a ibada ne yana cikin hukunce hukuncen da juma,a ta kebanta dasu da sauran ranaku,
kuma hadisi ingantacce ya razanar dangane da masu zance ko wasa da wani abu wanda zai dauke hankalinsu daka sauraren huduba lokacin da liman ke huduba, kuma basu da ladan juma,a kawai dai sunyi azahar ne.
Maganar nan kuwa koda ta nusar wace koda wani dan,uwanka ne yake wani abu da bai daceba kace yabari ko yai shiru to kayi lagawu, kuma baka da ladan sallar juma,a.
Allah kayi salati da sallama abisa Annabi muhammad da alayensa da sahabbansa.
Wallahu a'alam
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك.
*TAMBAYOYIN MUSULUNCI*
Thursday, 20 October 2016
Hanyoyi 10 na samun kariya daga sihiri da sammu da baki
HANYOYI GUDA GOMA NA SAMUN KARIYA DAGA SIHIRI DA SAMMU DA BAKI.
1-Kiyaye sallolin Farilla akan lokaci kuma acikin Jam'i. Wannan wajibine akan dukkan baligi sai wanda baya Lafiya ko matafiye sune yake faduwa akansu.
2-Yawaita karatun alqurani mai girma tare da bibiyar ma'anoninsa da kuma kokarin aiki da abinda yaye umarni da hani.
3-Kwadaituwa akan Yawaita ambaton Allah Akowane lokacin.
Allah yana cewa
( الَّذِينَ آمَنُوا وَتَطْمَئِنُّ قُلُوبُهُم بِذِكْرِ اللَّهِ ۗ أَلَا بِذِكْرِ اللَّهِ تَطْمَئِنُّ الْقُلُوبُ )
(Waɗanda suka yi ĩmãni kuma zukãtansu sukan natsu da ambaton Allah. To, da ambaton Allah zukãta suke natsuwa).
الرعد (28) Ar-Ra'd
Acikin zikirai da suke nada kariya daga SIHIRI da Baki da Sammu akwi:-
-Zikirai bayan Sallar Magriba:-
-Ayatul Kursiyyu
-Falaqi da Nas da Qulhuwa☆3.
-ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺬﻱ ﻻ ﻳﻀﺮ ﻣﻊ ﺍﺳﻤﻪ ﺷﻲﺀ ﻓﻲ ﺍﻷﺭﺽ ﻭﻻ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﻤﺎﺀ ﻭﻫﻮ ﺍﻟﺴﻤﻴﻊ ﺍﻟﻌﻠﻴﻢ. Sau ukku-3
-ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ، ﻟﻪ
ﺍﻟﻤﻠﻚ ﻭﻟﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻭﻫﻮ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﺷﻲﺀ ﻗﺪﻳﺮ .
Sau 100 bayan sallar magariba da Assuba.
-Karanta Suratul Baqra a gidan saboda Annabi s.a.w yana cewa:
Kada ku mayar da gidajen ku kamar maqabarta,Domin shaidhan yana gudu ya bar gidan da ake karanta Suratul Baqra.
-Yawaita Addu'a
-Yin alwala kafin kwanciya barci.
-Karanta ayoyi guda biyu na karshen suratul Baqra lokacin kwanciya barci.
-Yin tofi a hannu sannnan a karanta Qulhuwa Falaqi da Nas sannnan a shafe jiki lokacin kwanciya barci, ayi hakan sau ukku.
-Yawaita yin sadaka saboda Annabi s.a.w yana cewa:
(Kuyiwa marar lafiyar ku magani ta hanyar yin sadaka).
-Yin azkar lokacin shiga bandaki:
ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻲ ﺃﻋﻮﺫ ﺑﻚ ﻣﻦ ﺍﻟﺨﺒﺚ
-Kamewa daga yin magana a bandaki
-Addu'a lokacin Saduwa da Iyali.
ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺟﻨﺒﻨﺎ ﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ ﻭﺟﻨﺐ ﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ ﻣﺎ ﺭﺯﻗﺘﻨﺎ.
-Addu'ar shiga shiga
ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻲ ﺃﺳﺄﻟﻚ ﺧﻴﺮ ﺍﻟﻤﻮﻟﺞ، ﻭﺧﻴﺮ ﺍﻟﻤﺨﺮﺝ، ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻟﺠﻨﺎ، ﻭﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ
ﺧﺮﺟﻨﺎ، ﻭﻋﻠﻰ ﺭﺑﻨﺎ ﺗﻮﻛﻠﻨﺎ.
-Addu'ar fita daga gida
ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻮﻛﻠﺖ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻻ ﺣﻮﻝ ﻭﻻ ﻗﻮﺓ ﺇﻻ ﺑﺎﻟﻠﻪ.
-Yawaita zama da mutanan kirki da majlisin Ilimi.
4-Nisantar sabon Allah da kuma yin nadama da tuba ingantace bayan kayi sabon Allah ko zunubai.
Allah yana cewa:
( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا تُوبُوا إِلَى اللَّهِ تَوْبَةً نَّصُوحًا عَسَىٰ رَبُّكُمْ أَن يُكَفِّرَ عَنكُمْ سَيِّئَاتِكُمْ وَيُدْخِلَكُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ يَوْمَ لَا يُخْزِي اللَّهُ النَّبِيَّ وَالَّذِينَ آمَنُوا مَعَهُ ۖ نُورُهُمْ يَسْعَىٰ بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَبِأَيْمَانِهِمْ يَقُولُونَ رَبَّنَا أَتْمِمْ لَنَا نُورَنَا وَاغْفِرْ لَنَا ۖ إِنَّكَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ )
(Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kõma zuwa ga Allah kõmawar gaskiya. Mai yiwuwa Ubangjinku Ya kankare muku miyãgun ayyukanku kuma Ya shigar da ku a gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu a rãnar da Allah bã Ya kunyatar da Annabi da wadanda suka yi ĩmãni tãre da shi. Haskensu yanã tafiya a gaba gare su da jihõhin dãmansu, sunã cẽwa, "Yã Ubangijiumu! Ka cika mana haskenmu, kuma Ka yi mana gãfara. Lalle Kai, a kan dukkan kõme, Yã kai Mai ikon yi ne).
التحريم (8) At-Tahrim
Zunubai da suke da Tasiri wajan taimakawa sihiri da aljanu wajan shiga jikin dan adam:-
-Jin Kade kade da wake wake.
-Halartar wajan sabon Allah.
-Rataya hotuna a gida ko abin hawa.
Annabi s.a.w yana:
(Mala'iku basu shiga gidan da yake da Hotuna ko kare).
-Yi da mutane wato giba.
-Zuwa wajan Masu sihiri da bokaye da malaman tsubbu.
5-Yin kwadayin kiyaye manyan Ibadun da Allah ya wajabtawa bawa.kamar:-
-Bada zakka akan lokacin
-Yawaita yin azumin nafila
-Yawaita sallar Nafila
-Yin aikin Hajji da Umara.
Mu hadu a darasi na gaba insha Allah.
Allah ya karemu daga Sharri mutane da aljannu .
Zaton ku Allah bazai jarabe mu ba??
*ZATON KU ALLAH BAZAI JARABE MU BA?*
*Dr. Isa Ali Pantami*
Akwai abun da 'Dan Adam baya magancewa Kansa balle ya magance maka. Amma maimakon mu duba laifin da muke wa Allah mu gyara, sai mu ce rayuwa ta yi kunci, shugaba wane ya gagara. Eh, kana iya cewa wani lokaci an gagara. Amma ka sani, akwai laifin da mu muke yiwa Allah, matukar kuma bamu gyara ba, ko duk Arzikin Jaziratul Arab za a tara mana, ba za mu fita cikin kuncin da muke ciki ba!
Ai yanzu, kuncin rayuwar ba wai babu kudin bane. Akwai, Albarkar Allah Ya debe. In ko ba mu tuba zuwa ga Allah ba, Allah ba zai dawo da shi ba.
Babu Al'ummar da ta sabawa Allah ta ji dadi a Duniya. Babu ita!
Mutanan Annabi Lut, Luwadi kadai suka yi Allah Ya dirkake su. Ba a Luwadi a yanzu?
Mutanan Annabi Shu'aibu, tauye mudu kadai sukayi, akan wannan Allah Ya halakar da su. Ba a tauye mudu a yanzu?
Mutanan Annabi Saleh, Dabba kadai suka kashe. Akan Taguwa Allah Ya halakar da su. A yau ana kashe mutane, kuma Allah ba zai jarrabe mu ba?
Duk laifin da 'Dai - 'Dai ake wa Allah Ya halakar da mutane, yau duk mun hada muna yin su.
Babu laifin da akai wa Allah a tarihin Duniya da yanzu bama yinsu. Kuma Allah ba zai Jarrabe mu ba?
Har muna zaton Akwai 'Dan Adam da zai cire mu in bamu koma ga Allah ba? Ba za mu duba abun da muke wa Allah mu gyara ba?
A duk Al-Qur'ani, Allah bai bamu tarihin wata al'umma da take yanke jikin mutum a yi sihiri ba. Amma mu a yau muna yi. Bai bamu labarin inda Namiji ke auren Namiji ba, sai dai ace suna luwadi. Amma a yau muna yi. Har a Nigeria anyi irin wannan auren.
Wallahi, ba za mu samu mafita ba har sai mun tuba mun koma ga Allah.
Domin Allah cewa yayi: "Lallai Allah baya canza halin da mutane suke ciki, (wallahi) sai dai in sun canza dakansu." Idan muka canza, Allah zai canza mana.
Kuma ai Al-Qur'ani ya fada mana, Mutanan Fir'auna ai Annabi Musa (as) suka karyata, Allah Ya saukar musu da fari, da bushewar 'ya'yan itatuwa.
Mutanan Saba', suna cikin jin dadi ko abinci ba sa saya, amma da suka kafircewa Ni'imar Allah, sai Ya janye dukkanin falalar da Ya musu na kayan marmari a Lambu. Ya canza musu da ta 'kaya! Allah Ya sanya su cikin 'kuncin rayuwa.
Idan za mu bi dokokin Allah, babu irin Ni'imar da ba zai mana ba. 'Dan Adam baya wa mutane maganin kuncin rayuwa. Wadannan al'amura da muke ciki, na kuncin rayuwa da tawayar tattalin Arziki, suna bukatar muyi wa kanmu wa'azi ne. Mu koma zuwa ga Allah Madaukakin Sarki.
Sheihk balalau yayi martani ga mal. Dahiru bauchi
SHEIKH BALA LAU YAYI MARTANI GA MAL DAHIRU BAUCHI
Sheikh Bala lau yace bayan godiya ga Allah da Salati ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W.
Yace ya saurari jawabin da sheikh dahiru bauchi yayi musamman akaina da kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa'iqamatis Sunnah yace da farko kalmar da sheikh yayi akaina nacewa ni dinnan azzalumi ne kuma makaryaci mai daukan mata ya saidasu a saudi arabia wannan kalma ta batanci da kuma zagi bazanyi raddi ga wannan dattijo ba inzage shi ko inci mutuncin sa kamar yadda yaci mutunci na
Ina lura da shekarun sa amatsayin sa na Uba kuma dattijo amma ina shaidawa sheikh da duk wanda ya saurari jawabin sa cewa niba makaryaci bane niba azzalumi bane kuma bantaba daukan wata mata naje na kaita kasar saudi Arabia ba Allah ya sheda
Kuma duk wanda yasan tarihi na abaya to ba haka nake ba idan sheikh dahir yayi amfani da wannan ne don yaci mutunci na to ni bazan mayar mishi da irin kalmar da yayi akaina ba lura da matsayin sa na malami don haka wannan kalma tashi ba haka nake ba
Sannan kuma kungiya ta da yace ta nemi hadin kai dasu 'yan dariku don mu yaki 'yan shi'a ina tabbatar da wannna babu inda muka taba yin haka da sheikh Dahiru Bauchi koda wani dan darika in akwai inda muka tabayin haka akawo shaida don a tabbatar
Kuma kungiya ta ta IZALA ba inda ta kaiwa kiristoci ko yan darika hari don kashe su ko don kaiwa 'yan shi'a hari babu wannan
Sannan haryanzu kungiya ta IZALA batada alaqa da boko haram .
'Yan'uwa musulmai wannan shine takaitaccen abinda zan'iya fadi ina fata ALLAH S.W.T. ya gafarta mana ALLAH ya tsare mu daga sharrin shaidan
Subhanakallahumma wabi hamdika ash hadu an la'ilaha illah anta astagfiruka wa'atubu ilaika .
Waazin kasa a jahar kano
WA'AZIN KASA A JIHAR KANO!!!
ShugabanKungiyar Izala ta kasa,
Ash'Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau
Shugaban Majalisar Malamai ta kasa, Sheikh
Dr. Ibrahim Jalo Jalingo
Daraktan 'Yan Agaji na kasa, Injiniya
Mustapha Imam Sitti
A madadin kungiyar Jama’atu Izalatil Bid'ah
Wa Iqamatis Sunna ta tarayyar Najeriya, Suna
gayyatar 'Yan uwa musulmi zuwa wajen
wa'azin kasa da za'a gabatar a garin Kano a
ranakun;
Asabar da Lahadi
22/23/10/2016
Malaman da Ake sa ran zasu gabatar da
wa'azi sune:
-Sheikh Usman Isah Taliyawa Gombe
-Sheikh Dr. Alhassan Sa'id Adam Jos
-Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina
-Sheikh Abbas Muhammad Jega
-Sheikh Habibu Yahaya Kaura
-Sheikh Rabi'u Aliyu Daura
-Sheikh Dr. Abdullahi Saleh Pakistan
-Sheikh Barr Ibrahim Sabi'u Jibia
-Sheikh Abubakar Giro Argungu
-Sheikh Khalid Usman Khalid Jos
-Sheikh Dr. Sani R/Lemo
-Sheikh Abdulwahhab Abdallah Kano
-Ustaz Albaniy Samaru Zariya
-Ustaz Imam Ibrahim Lawal Osama Abuja
-Ustaz Tajuddeen Ibadan
-Ustaz Dr. Ibrahim R/Lemo
-Ustaz Abubakar Baban Gwale
-Ustaz Dr. Rabi'u R/Lemo
-Ustaz Abdulmudallib
-Alaramma Abubakar Adam Katsina
-Alaramma Ahmad Suleiman Kano
-Alaramma Nasiru Salihu Gwandu
-Alaramma Isma'il Maiduguri
-Alaramma Bashir Abubakar Gombe
-Alaramma Suleiman Azare
-Alaramma Ilyasu Birnin Gwari
Sanarwan ta fito ne daga Jami'in ya'da
Labarai na kungiyar ta kasa, Malam Ali 'Dan
Abba.
Allah ya bada ikon Zuwa Amin.
Jibwis Nigeria
19/10/2016
Menene hukuncin yin salati ga annabi a tafiya ta farko??
*MENENE HUKUNCIN YIN SALATI GA ANNABI A TAHIYA TAFARKO.*
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ .
Amsa:Malamai sunyi sabani akan yin salati ga Annabi sallallahu Alaihi wasallam atahiya tafarko abisa zantuka guda biyu.
Maganata farko shine zaiyi salati ga Annabi sallallahu Alaihi wasallam wannan itace fatawar shafi'i rahimahullah yace wanda yabar salati ga Annabi atahiyar farko zaiyi sujjadar mantuwa asallah, ibnu hazam rahimahullah shima ya zabi wannan maganar acikin littfinsa almu hallah (2/302).
Al imamu shafi'i acikin littafinsa al'ummu (1/228) yace: " Tahiya da salati ga Annabi sallallahu Alaihi wasallam akowacce sallah banda ta asuba tahiya biyuce, tafarko data karshe, idan mutum yabar tahiya dayin salati ga Annabi sallallahu Alaihi wasallam atahiyar farko yana mai mantuwa bazai sake tahiyar ba da kuma salatin Amma zaiyi sujjadar rafkanwa saboda mantuwa.
Shaik Abdul'azeez bin baz rahimahullah yazabi wannan magana ta shafi'i acikin fatawa bin baz (11/201). Da sheik nasiruddeen Albany rahimahullah acikin littafinsa kitabul salati (145).
Magana ta biyu itace:mutum ya takaita tahiyarsa bazai karanta salati ga Annabi sallallahu Alaihi wasallam ba, wannan itace maganar jamhur din malamai shaik usaimin rahimahullah yazabi wannan magana.
Jamhur din malamai suna ganin mutum bazai karanta salati ga Annabi ba azaman tahiyarsa na farko, wannan itace maganar naka'i da saury, da ishaq,.
Mazhabar shafi'iyyah sun tafi akan mustahabbancin yin salati ga Annabi acikinta adaya daka ruwayoyinsu, sha'abi yana da ra'ayin wannan fatawa.
Amma yin salati ga Annabi sallallahu Alaihi wasallam atahiya takarshe babu sabani atsakanin malamai.
ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻋﻠﻢ ،
***********************************
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻧﺖ ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ .
A kowanne hali karka manta da abubuwan nan guda 9
A KOWANNE HALI KAR KA MANTA DA ABUBUWAN NAN GUDA TARA :
1. Duk lokacin da wata ni'ima ta sameka, ka gode ma Allah kafin ka gode ma kowa. Kace "ALHAMDULILLAH".
2. Duk lokacin da wata musibah ta sameka, Ka zargi kanka Kar ka zargi kowa. Kuma kace "INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN".
3. Duk lokacin da Qofofin samunk suka toshe, to lallai sai ka tuno da yawan zunubinka. Ka yawaita ASTAGHFIRULLAH".
4. Duk lokacin da al'amura suka rinchabe maka, ko kuma Makiya suka sawoka gaba, Komai girman abun bai fi Qarfin Allah ba. Don haka ka yawaita "LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BIL-LAAHIL ALIYYIL 'AZEEM".
5. Duk lokacin da Bakin ciki ya dameka, ko kuma bukatunka suka toshe, to ka yawaita Salati ga fiyayyen Halittu (S.A.W) domin salatinsa yana haskaka zuciya, yana yaye damuwa, yana kawar da bakin ciki.
6. Duk lokacin da kaji zuciyarka ta bushe ta kekashe, (Babu tsananin taushin nan na tsoron Allah) To ka yawaita karatun Alqur'ani. Domin shi karatun Alqur'ani tare da Tadabburi (zurfafa tunani) cikin Ma'anoninsa, shine fiyayyen Maganin chututtuka na fili da na boye.
7. Duk inda kaje zaka aikata Sa'bon Allah, to ka tuno da cewa yana nan tare dakai. Yana jin ka, yana kallonka. Kuma akwai ranar tsayuwarka agabansa domin karbar sakamako akan dukkan ayyukanka.
8. Duk lokacin da kazo yin addu'a, to kayi ma iyayenka kafin kayi ma kanka. Duk lokacin da ka samu wadata, to ka kyautata ma iyayenka kafin ka kyautata ma kanka. Domin su ma haka suka fifita bukatunka akan nasu bukatun lokacin kana Qarami.
9. Duk lokacin da zakayi magana da Malamai ko manyan mutane to ka sanya ladabi acikin furucinka. Duk da cewa kai baka riski Annabi ba, to sune magadan Annabawa (as). Wadannan su ke dauke da abinda aka aiko shi da shi. Allah ya datar da mu, Amin.
Shin zaka iya tsinewa azzalumin shugaba
SHIN ZAKA IYA TSINEWA AZZALUMIN SHUGABA.
الحمد لله رب العالمين ولا عدوان إلا على الظالمين، والصلاة والسلام على محمد وعلى آله وصحبه وسلم.
AMSA:La'anta tana nufin Allah yakori mutum daka rahmarsa, da nesantashi dashi, yana daka cikin la'anta zagi da cin mutunci da muguwar addu'a ga mutum.
Tsinuwa tana faruwane ta fuska biyu:
1-Mutum ya la'anci kafirai da masu sabo a dunkule, kamar mutum yace Allah yatsinewa kafirai, Allah yatsinewa mazinata, Allah yatsinewa barayi da fasikai, da azzalumai, irin wannan la'anta ta halatta, ibnu muflih yace: acikin adabul shari'a la'antar kafirai gaba daya ya halatta (1/203).
2-Tsinuwar takasance ka ayyana wani jinsi wajan la'antar taka, kamar kace Allah yatsinewa kafiri wane ko Allah yatsinewa wane ko Wane maiyin kaza Allah yatsine mar, wannan nau'i na tsinuwa shima kashi biyu ne
1-Yakasance ansamu nassi dayake nuni da la'antarsa kamar shaidan, ko kuma nassi ya tabbatar da cewa ya mutu akan kafirci, kamar fir'auna da Abu lahab, da abu jahal, la'antar wadannan ya halatta.
Ibnu muflih, yace: acikin adabul shari'a (1/214). ya halatta tsinewa kafirai wadanda nassi yatabbatar da la'antar su, babu laifi wajan kin tsine musu.
2-Tsinewa wanda nassi baizo akan la'antar saba, tahanyar ayyana shi shi kadai da sunansa kamar mai saida giya, da wanda yake la'antar iyayen sa, dawanda yake yanka ga wanin Allah, Wannan shikuma malamai sunyi sabani wajan halacci ko haramcin hakan, da maganganu guda uku.
1-Sukace bai halatta ayyana wani mai sabo ko kafiri shi kadai, ka tsinemar ba takowanne hali.
2-Sukace ya halatta akan kafiri amma banda musulmi mai sabo,
3-Sukace: yahalatta kai tsaye.
Adabul shari'a na ibnu muflih,(1/303).
Wadanda sukace ya halatta la'antar kafiri shi kadai sunkafa hujja da dalilai kamar haka.
1-Daka Abdullahi dan Umar yaji manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam idan yadago daka ruku'un sallar sa ta raka'ar karshe ta asuba yana cewa:Allah katsinewa wane da wane bayan yace Allah yaji mai gode masa, sai Allah yasaukar da yah
(ليس لك من الأمر شيء أو يتوب عليهم أو يعذبهم فإنهم ظالمون،)
Baka da wani al'amari na komi akansu, ko Allah yakarbi tubansu ko yai musu azaba lallaisu azzalumai ne, da wannan aya wasu malamai sukace bai halatta la'antar mutum shi kadai ba koda kafirine saboda da wannan aya ta sauka sai manzan Allah yadaina ambaton su daya bayan daya saidai a jam'i, saboda idan Allah yakaddara zai shiryu agaba kuma katsine mar to ka zalunceshi.
2-Daka umar wani mutum yakasance azamanin manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam ana masa lakabi da "Himaar" yanasa manzan Allah dariya, Annabi yanai masa bulala idan yasa giya sai wata rana akazo dashi yasha giya za ai masa bulala,sai wani daka cikin sahabbai yace: Allah ya tsinemar saboda yawan shan giya dayake anaimar bulala, sai manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam yace:(kada ku la'ance shi Na rantse da Allah ba'abunda nasani akansa face yanasan Allah da manzan sa.) Bukhary(6780)
Shaikul islam ibnu taimiyyah acikin majmu'ul fatwa (6/511)
Yace: la'anta ta halatta kai tsaye ga wanda Allah damanzan sa suka la'anta, amma la'antar wani ka ayyana shi ta halatta ne kadai ga wanda ya mutu kafiri, amma la'antar fasiki maisabo ka ayyana shi bata halatta ba, saboda hanin da manzan Allah yayi na la'antar Abdullahi bin himar, duk da cewa Manzan Allah yala'anci masu shan giya da mai taimakawa wajen kasuwancin ta adunkule, tare dacewa la'antar mai sabo ka ayyanashi akwai sabanin malamai.
Shaeik uthaimeen Rahimahullah acikin qaulul mufeed (1/226) yace:
Banbaci tsakanin la'antar masu sabo adunkule dakuma la'antar wani ka ayyana shi, nafarko la'antar wani ka ayyana shi anhana, nabiyu la'antar masu sabo adunkule ya halatta, idan kaga mai taimakawa barna bazakace Allah yatsine maka mabarnaci ba, a'a sai dai kace Allah yatsinewa mabarnata, dalili akan haka shine lokacin da manzan Allah yake tsinewa wasu mushirikai acikin qunuti, yana ambatarsu da sunayensu, Allah ya hana shi hakan da fadinsa madaukakin sarki
(ليس لك من الأمر شي ء أو يتوب عليهم أو يعذبهم فإنهم ظالمون)
Baka da wani al'amari na komai akansu kodai Allah yakarbi tubansu ko kuma yai musu azaba hakika su azzalumaine. Bukhary
Wallahu A'alam.
Saboda haka la'antar shugaba koda azzalumine kuma koda fasikine haramunne ba koyarwar musulunci bace, koda kafirine matukar bai hanaku yin addinin kuba tsinemar da zaginsa dayi masa muguwar addu'a haramunne, kamar yana hanaku azumi ko sallah ko wata ibada ko yada addininku, saboda hadisai dasukai hani da hakan.
Ankarbo daka Abu umamah daka Annabi sallallahu Alaihi wasallam yace: ( kada ku zagi shugabanni, ku roka musu shiriya da gyaruwa awajan Allah domin gyaruwarsu gyaruwarkuce.)
Kuma tsinuwa da aibantawa ba al'adar mutumin kirki bace wanda yakebin koyarwar Annabinsa sallallahu Alaihi wasallam, saboda hadisi ya inganta manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam yace: ba'asan musulmin kirki da tsinuwaba, ko sakin harshe yaita maganganu bakai bagindai, ko zancen banza,
Muna rokon Allah madaukakin sarki yatabbatar da dugadugnmu akan abunda yakeso kuma yayarda dashi.
Wallahu A'alamu.
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك.
*TAMBAYOYIN MUSULUNCI*
*WhatsApp Group*
Menene hukuncin magana a cikin bandaki
MENENE HUKUNCIN MAGANA ACIKIN BANDAKI
الحمد لله والصلاة والسلام على محمد وعلى آله وصحبه وسلم.
AMSA:Makaruhine ambaton Allah awajan biyan bukata, dan girmama sunan Allah madaukakin sarki bai kamata ka ambaceshi agurin najasaba, wanda kuma makwancin shaidanu ne.
Imamun nawawy rahimahullah yace: acikin littafin al'azkaar, [ makaruhine ambaton Allah alokacin da mutum yake biyan bukata, a sahara yake jeji kenan dajin Allah ko agurin da angina shi dan biyan bukata kawai, bawai Ambaton Allah kawai ba, dukkanin zikirai da zance na duniya inba da lalura ba, idan mutum yai attishawa abandaki bazai tahmidi ba kuma baza'a amsa masa ba, haka idan mutum yana biyan bukata bazai amsa sallama koya mayar ba, haka kuma bazai amsawa mai kiran sallah ba, zance a wadannan gurare makruhine, dan tsarkake sunan Allah madaukakin sarki amma ba haramun bane, idan mutum yai attishawa sai ya godewa Allah azuciyarsa, harshensa bai motsaba babu laifi, haka zai aikata ahalin dayake jima'i da matarsa.
Dalili shine hadisi daka Abdullahi dan umar Allah yakara yarda dasu yace: Wani mutum ya wuce manzan Allah yana fitsari sai yaiwa manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam sallama bai amsa masaba,) Muslim (370).
Sabida haka idan wajen alwala yakasance acikin bandaki ban dakin kuma bawajen wankane kawai ba, hukuncin karhancin ambaton Allah maganganun malamai sunci karo da juna awannan wajen tare da halaccin yin bismillah, wasu malaman suntafi akan zaiyi bismillar azuciyarsa batare daya furta da harshen saba.
Wasu malaman kuma sukace: zai yi bismillah da harshen sa ayayin alwala abandaki awannan lokacin babu karhancin.
Yazo afatawar lajnatul da'ima cewa:"makaruhine ambaton Allah agurin da ake biyan bukata dan tsarkake sunan Allah da girmama shi, amma ya halatta yayi bismillah yayin fara alwala domin wajibice awajen dayawa daka cikin malamai.
Idan wajen alwala yakasance wajen bandaki koda ajikin bandakin yake kamar katanga daya gurin yake data bandaki, yahalatta ga mai alwala yafurta bismillah awannan hali domin awajen bandaki ne.
Saboda haka zance abandaki makruhine koda ba ambaton Allah bane, amma idan bukata ta kama yahalatta kamar kana wanka ruwa yakare ma, zakai magana dakarfi akawo ma ruwa ka karasa, ko kana gidan wanka nakudi shaya tadauke ruwa zakai magana babu ruwa da makamantan uzuruka dazaka bukata aima kanada daka cikin bandaki, wallahu A'alam
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك.
Tambayoyin musulunci
Watsapp
Mu kyautatawa juna zato
*MU KYAUTATAWA JUNA ZATO*
*_WANI DAGA CIKIN SALAF (MAGABATAN FARKO NA KWARAI) YANA CEWA:_*
_*Idan naga ruwan giya suna diga daga gemun mutum, to zance wataqil giyar ta zubar masa ne*_ Wato abinda yake nufi anan tunda dai bai ganshi yana shan giyar ba a zahiri ba to lallai ba zaice ya ganshi yana shan giya ba.
*HAKA KUMA YA QARA DA CEWA:*
*_Haka kuma idan na ganshi a saman tsololuwar tsauni yana cewa_; " *NI NE UBANGIJINKU MAFI DAUKAKA* " ( *ANA RABBUKUMUL A'ALA* ). *_Anan kuma zance wannan yana karanta_* *AYA CE DAGA AL-QUR'ANI MAI GIRMA*
Kaji *swalihan* bayi kenan, duk fa wannan yana yine akan tsananin kyautatawa musulmi zato, yi masa uzuri da kuma gujewa yin shaidar zur.
Yanzu mutanen wannan zamanin wa zaiga giya na zuba daga gemun mutum yace wai ba giyar ce ya gama sha ba? Haka kuma wa zai ga mutum saman qololuwar tsauni yana kwala ihu yana fadar *_NI NE UBANGIJINKU MAFI DAUKAKA_* Har yace bawai kansa yake kira Allah ba, ai ayar qur'ani ce yake karantawa?
Kuma wannan itace dabi'ar da ake son musulmai su dabi'antu da ita ta kaucewa yin shaidar zur, kyautatawa juna zato da kuma gujewa munanawa musulmi zato kamar yanda dimbin ayoyin Al-qur'ani da ingantattun hadisai suka hore mu.
*Allah ya bamu ikon kyautatawa junanmu zato. Ameen*
*TAMBAYOYIN MUSULUNCI*
Wednesday, 19 October 2016
Hukuncin yin tsarki da ruwan wanka
HUKUNCIN YIN TSARKI DA RUWAN WANKA TAMBAYA TA 2002 ******************** Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah, Malam ya hidima da ake tayi damu dalibai, Allah ya saka da alkhairi. Allah ya albarkaci Zuri'a, Amin. Malam Nayi dahara da ruwan da nayi wanka dashi da niyyar idan na fito zan Kuma yi da wani ruwan daban. Dana fito sai na manta har nayi sallar azahar da laasar, Sai na tuna da magriba. Malam ya zanyi na gyara. Bissalam. AMSA ******* Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Hukuncin ya danganta da irin yanayin ruwan wankan. Idan ruwan wankan sabulu ne, Kuma ya riga ya chakude da sabulun, to lallai wannan tsarkin naka bai yiwu ba. Kuma zaka rama dukkan sallolin da kayi da wannan tsarkin. Amma idan wankan ibadah kayi, ko kuma wankan sanyaya jiki, to ya halatta kayi tsarki da irin ragowar ruwan wadannan wankan. Mutukar dai siffofinsa basu chanza ba. WALLAHU A'ALAM. DAGA ZAUREN FIQHU
Hukuncin amsa sallamar kifiri
HUKUNCIN AMSA SALLAMAR KAFIRI
TAMBAYA TA 2001
********************
Assalamu alaikum. Allah ya qarawa malam Eamani ya jiqan iyaye. Ameen, tambaya nake roqon a amsa min.
Yaya hukuncin Wanda ya shaaku da Wanda ba musulmi ba kuma ya dauke shi a matsayin aboki?
kuma shin ya kamata a mayar ma Wanda ba musulmi sallama idan yace ma Assalamu alaikum?.
Dafatan malam zai samu damar amsa tambayata.
daga dalibinka Ibraheem I g
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Allah Madaukakin Sarki ya umurcemu da cewa kada mu riki Yahudu da Nasaara amatsayin Masoya ko Majibinta garemu. Ba don komai ba, sai domin sharrin da irin hakan zai haifar ga rayuwarmu da addininmu.
Allah Madaukakin Sarki yace : "YA KU WADANDA SUKAYI IMANI! KADA KU RIKI YAHUDU DA NASAARA AMATSAYIN MAJIBINTA (WATO ABOKAI KO MASOYA) SASHENSU MAJIBINTA NE GA SASHE. DUK WANDA YA JIBINCESU DAGA CIKINKU TO HAKIKA SHIMA YANA CIKINSU. HAKIKA ALLAH BA YA SHIRIYAR DA MUTANE AZZALUMAI".
(Ma'idah ayah ta 51).
Ibnu Abi Hatam ya ruwaito cewa Watarana azamanin Khalifancin Sayyiduna Umar (rta) ya ce ma Sayyiduna Abu Musal Ash'ariy (rta) ya rubuto masa wani abu.
Shi kuma Abu Musal Ash'ariy sai ya sanya wani kirista (Nasaara) ya rubuta masa. Daga karshe da Sayyiduna Umar ya gane hakan sai da yayi masa fa'da sosai. Sannan ya tunasar dashi wannan ayar da muka kawo a sama.
Babu laifi ka kyautata alakar zamantakewa tare dasu awajen aiki ko kasuwa. Amma kar ka rikesu amatsayin abokai ko aminai gareka.
2. Dangane da amsa sallamarsu, akwai maganganun Malamai kala-kala. Amma magana mafi rinjaye ita ce wacce Ibnul Qayyim ya kawo acikin ZADUL MA'AD juzu'i na 2 shafi na 425-426, yace :
"Malamai sunyi sa'bani dangane da wajibcin amsa sallamar wanda ba Musulmi ba (idan yace maka Assalamau alaikum) amma Mafiya rinjayen Maluma sunce wajibi ne. Kuma wannan shine ra'ayi mafi Sahihanci.
Sannan Malaman sunce zaka mayar masa da cikakkiyar Sallama ne bisa gwargwadon yadda Allah yayi umurnin cewa :
"IDAN AKA GAISHEKU DA WATA GAISUWA, TO KU MAYAR DA IRIN WACCE TAFI KYAWU, KO KUMA KU MAYAR DA ITA (KAMAR YADDA AKA YI MUKU)".
WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU
Hukuncin hana daukar ciki wato family planning
الحمد لله والصلاة والسلام على محمد وعلى آله وصحبه وسلم.
AMSA:Abunda yakamata musani asali shine kowanne cikin ma'aurata yanada hakki wajan samuwar 'ya'ya, bai halatta ga miji yaiwa matarsa azlu ba, saida izininta, haka mata ma bata da iznin bin wata hanya dan hana daukar ciki saida iznin mijinta, Mausu'atul fiqhiyyah (3/156).
Yazo acikin baharul raã'uuq (3/215) ya kamata mace tasani kawar da abunda ke mahaifarta ko toshe samuwar ciki a mahaifarta haramunne inba da iznin mijin taba.
Ibnul muflih Alhambaly yace:" ya halatta ga mace tasha magani na halal danta yanke zuwan jini haila, Alqazy yace: " da izinin mijinta kamar azlu" yana karfafa maganar Ahmad bin hambal awani yanki na jawabinsa, mace zata nemi iznin mijinta, Alfuru'u (1/392) Marudy yace shine dai-dai.
Alqazy yace: bai halatta ba saida izinin miji domin yana da hakki akan dah, kashshaful qina'a (2/96).
Sai dai idan ansamu wani uzuri na bayyane akan mace cewar bazata iya daukar ciki ba, kamar daukan cikin yana sabbaba mata cuta bayyananniya tahanyar shaidar kwararrun likitoci, a wannan halin, hakkin miji yake gushewa wajen neman izninsa, domin maslahar mace wajen kiyaye lafiyarta itace abar gabatar wa, akan maslahar miji wajan samun cikin dah, Manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam yace: "Babu cuta ba cutarwa"" ibnu majah ya ruwaito shi (2340) Nawawy ya hassana shi acikin littafinsa Al'azkaar (502).
Balma malamai sun halatta zubda cikin dabai haura kwana arba'in ba matukar cigaba da zamansa zai shafi lafiyar mace.
Yazo afatawar sheik uthaimeen Rahimahullah Antambayeshi, Ni inada aure, mijina kuma bayasan na sha kwayoyin hana haihuwa, amma baisan wahalar danake haduwa da itaba, ina cutuwa akan hakan, nikuma nash kwayoyin hana haihuwa batare da snin miji naba, shin akwai laifi akan hakan?
Sai malam ya amsa: Idan zaki iya barin kwayoyin shi yafi,Amma idan cutar mai girma ce, kuma wahalar babba ce, babu laifi, amma barin kwayoyin shi yafi,sai idan cutar babbace, kuma yana wahalar dake, saboda fadin Allah madaukakin sarki (Kuji tsoran Allah dai-dai iyawarku)
Fatawa uthaimeen (21/184).
Shaeik uthaimeen yace : wajibine akan namiji yakula da matarsa idan yaga tana shan wahala, shan wahalar dabai saba ganin tanayi inta dau ciki abaya ba, yaimata izni wajan shan maganin dazai hana daukar cikin, koshi dakansa yai mata abunda dazata daina daukar cikin koya kawo mata, dan nuna tausasawa agareta, da jinkai agreta, harsai tasamu lafiya, ta kuma samu karfin jikinta. fatwa nurun alal darbi.
Amma munin halin miji, narashin iya zama da mace, da munanan dabi'unsa ba uzuri bane, ba hujja ba ce, ta hana daukar ciki, hakika Allah yana iya sanya canji da alkhairi mai yawa atare da dan, kamar yanda Allah madaukakin sarki yace:( Yana fitar da rayayye daka matacce yafitar da matacce daka rayayye).
Hakama yace:( Zaku iya kin wani abu, Alhalin alkhairine atare daku, haka kuma zaku iya san wani abu amma sharri ne atare daku).
Dan haka shan magani danyin family plannin haramunne, saida yardar dukkan bangarori biyu na ma'aurata kuma saida lalura babba wacce take barazana ga lafiyar mace, kuma da tabbatarwa likitoci amintattu kuma kwararru masana, duk da haka sai in cutar tagirmama tayanda daukar cikin na iya kaiwa ga halaka ga ita macen, duk dahaka dazarar wannan matsala ta wuce, babu wani dalili na yin family planning.
Wallahu a'alam
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك.
*🌙Tambayoyin Musulunci🌙*
*WhatsApp Group*