MAGANIN WASWASIN FITSARI
TAMBAYA TA 2003
********************
Asaalamu Alaikum malam Allah saka da Alkhairi a bisa taimakon da kake mana kullum Allah saka da Alkhairi malam ina fama da matsalar dake damuna idan nayi tsarkin fitsari zan tsaya in matse in karkade kamar dai yanda malaman fiqhu sukai bayani toh Amma malam duk da haka wani lokaci sai inji kamar wani ya biyo mani cikin wando kuma sai in koma kewaye idan na koma kewaye kuma sai inga gaka din nasha maganin baturen amma dai baiyi ba shine nake so ka taimaka mani da maganin da zanyi Amfani dashi
Wassalamu Alaikum.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Shi irin wannan waswasin ana iya maganceshi ne ta hanyoyi da dama kamar haka :
1. Ka tabbatar kayi addu'ar shiga bandaki tun kafin ka shiga. Sannan ka shiga da Qafar Haggu.
2. Ka tabbatar ka gama biyan bukatarka kafin ka tashi.
3. Ka tabbatar kayi nishi sosai domin fitar da sauran abinda ke cikinka na najasa.
4. Ka tabbatar ka karkade, kuma ka matse cikin tausasawa. Kada ka chutar da kanka.
5. Idan kuma kana da larurar da fitsari ba ya gama fita daga jikinka cikin hanzari, to zaka iya mikewa tsaye kadan, sannan ka sake tsugunnawa ka sake matsewa.
6. Daga cikin Maluman Fiqhu, akwai wadanda suke ganin cewar zaka iya mikewa har kayi tattaki kamar taku daya zuwa biyu sannan ka sake dawowa ka tsugunna.
7. Daga karshe ina baka shawarar cewa ka yawaita amfani da shayin Na'a-na'a wanda aka matsa lemon tsami acikinsa. In sha Allahu zaka samu lafiya daga wannan matsalar.
Allah ya sawwake. Allah shi baka lafiya.
WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU
Friday, 21 October 2016
Maganin waswasin fitsari
Ya hukuncin wanda yai magana ko danna waya a lokacin da liman ke huduba ranar jumu'a??
*YA HUKUNCIN WANDA YAI MAGANA KO DANNA WAYA A LOKACIN DA LIMAN KE HUDUBA RANAR JUMA'A.??*
AMSA:Wanda yai magana ranar juma,a ko wasa, ko danna waya, ahalin liman yana huduba, babu shakka yayi laifi wato yayi lagawu wato yashasshen zance na wargi.
Domin shi sauraren huduba ranar juma,a ibada ne yana cikin hukunce hukuncen da juma,a ta kebanta dasu da sauran ranaku,
kuma hadisi ingantacce ya razanar dangane da masu zance ko wasa da wani abu wanda zai dauke hankalinsu daka sauraren huduba lokacin da liman ke huduba, kuma basu da ladan juma,a kawai dai sunyi azahar ne.
Maganar nan kuwa koda ta nusar wace koda wani dan,uwanka ne yake wani abu da bai daceba kace yabari ko yai shiru to kayi lagawu, kuma baka da ladan sallar juma,a.
Allah kayi salati da sallama abisa Annabi muhammad da alayensa da sahabbansa.
Wallahu a'alam
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك.
*TAMBAYOYIN MUSULUNCI*
Thursday, 20 October 2016
Hanyoyi 10 na samun kariya daga sihiri da sammu da baki
HANYOYI GUDA GOMA NA SAMUN KARIYA DAGA SIHIRI DA SAMMU DA BAKI.
1-Kiyaye sallolin Farilla akan lokaci kuma acikin Jam'i. Wannan wajibine akan dukkan baligi sai wanda baya Lafiya ko matafiye sune yake faduwa akansu.
2-Yawaita karatun alqurani mai girma tare da bibiyar ma'anoninsa da kuma kokarin aiki da abinda yaye umarni da hani.
3-Kwadaituwa akan Yawaita ambaton Allah Akowane lokacin.
Allah yana cewa
( الَّذِينَ آمَنُوا وَتَطْمَئِنُّ قُلُوبُهُم بِذِكْرِ اللَّهِ ۗ أَلَا بِذِكْرِ اللَّهِ تَطْمَئِنُّ الْقُلُوبُ )
(Waɗanda suka yi ĩmãni kuma zukãtansu sukan natsu da ambaton Allah. To, da ambaton Allah zukãta suke natsuwa).
الرعد (28) Ar-Ra'd
Acikin zikirai da suke nada kariya daga SIHIRI da Baki da Sammu akwi:-
-Zikirai bayan Sallar Magriba:-
-Ayatul Kursiyyu
-Falaqi da Nas da Qulhuwa☆3.
-ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺬﻱ ﻻ ﻳﻀﺮ ﻣﻊ ﺍﺳﻤﻪ ﺷﻲﺀ ﻓﻲ ﺍﻷﺭﺽ ﻭﻻ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﻤﺎﺀ ﻭﻫﻮ ﺍﻟﺴﻤﻴﻊ ﺍﻟﻌﻠﻴﻢ. Sau ukku-3
-ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ، ﻟﻪ
ﺍﻟﻤﻠﻚ ﻭﻟﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻭﻫﻮ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﺷﻲﺀ ﻗﺪﻳﺮ .
Sau 100 bayan sallar magariba da Assuba.
-Karanta Suratul Baqra a gidan saboda Annabi s.a.w yana cewa:
Kada ku mayar da gidajen ku kamar maqabarta,Domin shaidhan yana gudu ya bar gidan da ake karanta Suratul Baqra.
-Yawaita Addu'a
-Yin alwala kafin kwanciya barci.
-Karanta ayoyi guda biyu na karshen suratul Baqra lokacin kwanciya barci.
-Yin tofi a hannu sannnan a karanta Qulhuwa Falaqi da Nas sannnan a shafe jiki lokacin kwanciya barci, ayi hakan sau ukku.
-Yawaita yin sadaka saboda Annabi s.a.w yana cewa:
(Kuyiwa marar lafiyar ku magani ta hanyar yin sadaka).
-Yin azkar lokacin shiga bandaki:
ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻲ ﺃﻋﻮﺫ ﺑﻚ ﻣﻦ ﺍﻟﺨﺒﺚ
-Kamewa daga yin magana a bandaki
-Addu'a lokacin Saduwa da Iyali.
ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺟﻨﺒﻨﺎ ﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ ﻭﺟﻨﺐ ﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ ﻣﺎ ﺭﺯﻗﺘﻨﺎ.
-Addu'ar shiga shiga
ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻲ ﺃﺳﺄﻟﻚ ﺧﻴﺮ ﺍﻟﻤﻮﻟﺞ، ﻭﺧﻴﺮ ﺍﻟﻤﺨﺮﺝ، ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻟﺠﻨﺎ، ﻭﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ
ﺧﺮﺟﻨﺎ، ﻭﻋﻠﻰ ﺭﺑﻨﺎ ﺗﻮﻛﻠﻨﺎ.
-Addu'ar fita daga gida
ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻮﻛﻠﺖ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻻ ﺣﻮﻝ ﻭﻻ ﻗﻮﺓ ﺇﻻ ﺑﺎﻟﻠﻪ.
-Yawaita zama da mutanan kirki da majlisin Ilimi.
4-Nisantar sabon Allah da kuma yin nadama da tuba ingantace bayan kayi sabon Allah ko zunubai.
Allah yana cewa:
( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا تُوبُوا إِلَى اللَّهِ تَوْبَةً نَّصُوحًا عَسَىٰ رَبُّكُمْ أَن يُكَفِّرَ عَنكُمْ سَيِّئَاتِكُمْ وَيُدْخِلَكُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ يَوْمَ لَا يُخْزِي اللَّهُ النَّبِيَّ وَالَّذِينَ آمَنُوا مَعَهُ ۖ نُورُهُمْ يَسْعَىٰ بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَبِأَيْمَانِهِمْ يَقُولُونَ رَبَّنَا أَتْمِمْ لَنَا نُورَنَا وَاغْفِرْ لَنَا ۖ إِنَّكَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ )
(Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kõma zuwa ga Allah kõmawar gaskiya. Mai yiwuwa Ubangjinku Ya kankare muku miyãgun ayyukanku kuma Ya shigar da ku a gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu a rãnar da Allah bã Ya kunyatar da Annabi da wadanda suka yi ĩmãni tãre da shi. Haskensu yanã tafiya a gaba gare su da jihõhin dãmansu, sunã cẽwa, "Yã Ubangijiumu! Ka cika mana haskenmu, kuma Ka yi mana gãfara. Lalle Kai, a kan dukkan kõme, Yã kai Mai ikon yi ne).
التحريم (8) At-Tahrim
Zunubai da suke da Tasiri wajan taimakawa sihiri da aljanu wajan shiga jikin dan adam:-
-Jin Kade kade da wake wake.
-Halartar wajan sabon Allah.
-Rataya hotuna a gida ko abin hawa.
Annabi s.a.w yana:
(Mala'iku basu shiga gidan da yake da Hotuna ko kare).
-Yi da mutane wato giba.
-Zuwa wajan Masu sihiri da bokaye da malaman tsubbu.
5-Yin kwadayin kiyaye manyan Ibadun da Allah ya wajabtawa bawa.kamar:-
-Bada zakka akan lokacin
-Yawaita yin azumin nafila
-Yawaita sallar Nafila
-Yin aikin Hajji da Umara.
Mu hadu a darasi na gaba insha Allah.
Allah ya karemu daga Sharri mutane da aljannu .
Zaton ku Allah bazai jarabe mu ba??
*ZATON KU ALLAH BAZAI JARABE MU BA?*
*Dr. Isa Ali Pantami*
Akwai abun da 'Dan Adam baya magancewa Kansa balle ya magance maka. Amma maimakon mu duba laifin da muke wa Allah mu gyara, sai mu ce rayuwa ta yi kunci, shugaba wane ya gagara. Eh, kana iya cewa wani lokaci an gagara. Amma ka sani, akwai laifin da mu muke yiwa Allah, matukar kuma bamu gyara ba, ko duk Arzikin Jaziratul Arab za a tara mana, ba za mu fita cikin kuncin da muke ciki ba!
Ai yanzu, kuncin rayuwar ba wai babu kudin bane. Akwai, Albarkar Allah Ya debe. In ko ba mu tuba zuwa ga Allah ba, Allah ba zai dawo da shi ba.
Babu Al'ummar da ta sabawa Allah ta ji dadi a Duniya. Babu ita!
Mutanan Annabi Lut, Luwadi kadai suka yi Allah Ya dirkake su. Ba a Luwadi a yanzu?
Mutanan Annabi Shu'aibu, tauye mudu kadai sukayi, akan wannan Allah Ya halakar da su. Ba a tauye mudu a yanzu?
Mutanan Annabi Saleh, Dabba kadai suka kashe. Akan Taguwa Allah Ya halakar da su. A yau ana kashe mutane, kuma Allah ba zai jarrabe mu ba?
Duk laifin da 'Dai - 'Dai ake wa Allah Ya halakar da mutane, yau duk mun hada muna yin su.
Babu laifin da akai wa Allah a tarihin Duniya da yanzu bama yinsu. Kuma Allah ba zai Jarrabe mu ba?
Har muna zaton Akwai 'Dan Adam da zai cire mu in bamu koma ga Allah ba? Ba za mu duba abun da muke wa Allah mu gyara ba?
A duk Al-Qur'ani, Allah bai bamu tarihin wata al'umma da take yanke jikin mutum a yi sihiri ba. Amma mu a yau muna yi. Bai bamu labarin inda Namiji ke auren Namiji ba, sai dai ace suna luwadi. Amma a yau muna yi. Har a Nigeria anyi irin wannan auren.
Wallahi, ba za mu samu mafita ba har sai mun tuba mun koma ga Allah.
Domin Allah cewa yayi: "Lallai Allah baya canza halin da mutane suke ciki, (wallahi) sai dai in sun canza dakansu." Idan muka canza, Allah zai canza mana.
Kuma ai Al-Qur'ani ya fada mana, Mutanan Fir'auna ai Annabi Musa (as) suka karyata, Allah Ya saukar musu da fari, da bushewar 'ya'yan itatuwa.
Mutanan Saba', suna cikin jin dadi ko abinci ba sa saya, amma da suka kafircewa Ni'imar Allah, sai Ya janye dukkanin falalar da Ya musu na kayan marmari a Lambu. Ya canza musu da ta 'kaya! Allah Ya sanya su cikin 'kuncin rayuwa.
Idan za mu bi dokokin Allah, babu irin Ni'imar da ba zai mana ba. 'Dan Adam baya wa mutane maganin kuncin rayuwa. Wadannan al'amura da muke ciki, na kuncin rayuwa da tawayar tattalin Arziki, suna bukatar muyi wa kanmu wa'azi ne. Mu koma zuwa ga Allah Madaukakin Sarki.
Sheihk balalau yayi martani ga mal. Dahiru bauchi
SHEIKH BALA LAU YAYI MARTANI GA MAL DAHIRU BAUCHI
Sheikh Bala lau yace bayan godiya ga Allah da Salati ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W.
Yace ya saurari jawabin da sheikh dahiru bauchi yayi musamman akaina da kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa'iqamatis Sunnah yace da farko kalmar da sheikh yayi akaina nacewa ni dinnan azzalumi ne kuma makaryaci mai daukan mata ya saidasu a saudi arabia wannan kalma ta batanci da kuma zagi bazanyi raddi ga wannan dattijo ba inzage shi ko inci mutuncin sa kamar yadda yaci mutunci na
Ina lura da shekarun sa amatsayin sa na Uba kuma dattijo amma ina shaidawa sheikh da duk wanda ya saurari jawabin sa cewa niba makaryaci bane niba azzalumi bane kuma bantaba daukan wata mata naje na kaita kasar saudi Arabia ba Allah ya sheda
Kuma duk wanda yasan tarihi na abaya to ba haka nake ba idan sheikh dahir yayi amfani da wannan ne don yaci mutunci na to ni bazan mayar mishi da irin kalmar da yayi akaina ba lura da matsayin sa na malami don haka wannan kalma tashi ba haka nake ba
Sannan kuma kungiya ta da yace ta nemi hadin kai dasu 'yan dariku don mu yaki 'yan shi'a ina tabbatar da wannna babu inda muka taba yin haka da sheikh Dahiru Bauchi koda wani dan darika in akwai inda muka tabayin haka akawo shaida don a tabbatar
Kuma kungiya ta ta IZALA ba inda ta kaiwa kiristoci ko yan darika hari don kashe su ko don kaiwa 'yan shi'a hari babu wannan
Sannan haryanzu kungiya ta IZALA batada alaqa da boko haram .
'Yan'uwa musulmai wannan shine takaitaccen abinda zan'iya fadi ina fata ALLAH S.W.T. ya gafarta mana ALLAH ya tsare mu daga sharrin shaidan
Subhanakallahumma wabi hamdika ash hadu an la'ilaha illah anta astagfiruka wa'atubu ilaika .
Waazin kasa a jahar kano
WA'AZIN KASA A JIHAR KANO!!!
ShugabanKungiyar Izala ta kasa,
Ash'Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau
Shugaban Majalisar Malamai ta kasa, Sheikh
Dr. Ibrahim Jalo Jalingo
Daraktan 'Yan Agaji na kasa, Injiniya
Mustapha Imam Sitti
A madadin kungiyar Jama’atu Izalatil Bid'ah
Wa Iqamatis Sunna ta tarayyar Najeriya, Suna
gayyatar 'Yan uwa musulmi zuwa wajen
wa'azin kasa da za'a gabatar a garin Kano a
ranakun;
Asabar da Lahadi
22/23/10/2016
Malaman da Ake sa ran zasu gabatar da
wa'azi sune:
-Sheikh Usman Isah Taliyawa Gombe
-Sheikh Dr. Alhassan Sa'id Adam Jos
-Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina
-Sheikh Abbas Muhammad Jega
-Sheikh Habibu Yahaya Kaura
-Sheikh Rabi'u Aliyu Daura
-Sheikh Dr. Abdullahi Saleh Pakistan
-Sheikh Barr Ibrahim Sabi'u Jibia
-Sheikh Abubakar Giro Argungu
-Sheikh Khalid Usman Khalid Jos
-Sheikh Dr. Sani R/Lemo
-Sheikh Abdulwahhab Abdallah Kano
-Ustaz Albaniy Samaru Zariya
-Ustaz Imam Ibrahim Lawal Osama Abuja
-Ustaz Tajuddeen Ibadan
-Ustaz Dr. Ibrahim R/Lemo
-Ustaz Abubakar Baban Gwale
-Ustaz Dr. Rabi'u R/Lemo
-Ustaz Abdulmudallib
-Alaramma Abubakar Adam Katsina
-Alaramma Ahmad Suleiman Kano
-Alaramma Nasiru Salihu Gwandu
-Alaramma Isma'il Maiduguri
-Alaramma Bashir Abubakar Gombe
-Alaramma Suleiman Azare
-Alaramma Ilyasu Birnin Gwari
Sanarwan ta fito ne daga Jami'in ya'da
Labarai na kungiyar ta kasa, Malam Ali 'Dan
Abba.
Allah ya bada ikon Zuwa Amin.
Jibwis Nigeria
19/10/2016
Menene hukuncin yin salati ga annabi a tafiya ta farko??
*MENENE HUKUNCIN YIN SALATI GA ANNABI A TAHIYA TAFARKO.*
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ .
Amsa:Malamai sunyi sabani akan yin salati ga Annabi sallallahu Alaihi wasallam atahiya tafarko abisa zantuka guda biyu.
Maganata farko shine zaiyi salati ga Annabi sallallahu Alaihi wasallam wannan itace fatawar shafi'i rahimahullah yace wanda yabar salati ga Annabi atahiyar farko zaiyi sujjadar mantuwa asallah, ibnu hazam rahimahullah shima ya zabi wannan maganar acikin littfinsa almu hallah (2/302).
Al imamu shafi'i acikin littafinsa al'ummu (1/228) yace: " Tahiya da salati ga Annabi sallallahu Alaihi wasallam akowacce sallah banda ta asuba tahiya biyuce, tafarko data karshe, idan mutum yabar tahiya dayin salati ga Annabi sallallahu Alaihi wasallam atahiyar farko yana mai mantuwa bazai sake tahiyar ba da kuma salatin Amma zaiyi sujjadar rafkanwa saboda mantuwa.
Shaik Abdul'azeez bin baz rahimahullah yazabi wannan magana ta shafi'i acikin fatawa bin baz (11/201). Da sheik nasiruddeen Albany rahimahullah acikin littafinsa kitabul salati (145).
Magana ta biyu itace:mutum ya takaita tahiyarsa bazai karanta salati ga Annabi sallallahu Alaihi wasallam ba, wannan itace maganar jamhur din malamai shaik usaimin rahimahullah yazabi wannan magana.
Jamhur din malamai suna ganin mutum bazai karanta salati ga Annabi ba azaman tahiyarsa na farko, wannan itace maganar naka'i da saury, da ishaq,.
Mazhabar shafi'iyyah sun tafi akan mustahabbancin yin salati ga Annabi acikinta adaya daka ruwayoyinsu, sha'abi yana da ra'ayin wannan fatawa.
Amma yin salati ga Annabi sallallahu Alaihi wasallam atahiya takarshe babu sabani atsakanin malamai.
ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻋﻠﻢ ،
***********************************
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻧﺖ ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ .
A kowanne hali karka manta da abubuwan nan guda 9
A KOWANNE HALI KAR KA MANTA DA ABUBUWAN NAN GUDA TARA :
1. Duk lokacin da wata ni'ima ta sameka, ka gode ma Allah kafin ka gode ma kowa. Kace "ALHAMDULILLAH".
2. Duk lokacin da wata musibah ta sameka, Ka zargi kanka Kar ka zargi kowa. Kuma kace "INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN".
3. Duk lokacin da Qofofin samunk suka toshe, to lallai sai ka tuno da yawan zunubinka. Ka yawaita ASTAGHFIRULLAH".
4. Duk lokacin da al'amura suka rinchabe maka, ko kuma Makiya suka sawoka gaba, Komai girman abun bai fi Qarfin Allah ba. Don haka ka yawaita "LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BIL-LAAHIL ALIYYIL 'AZEEM".
5. Duk lokacin da Bakin ciki ya dameka, ko kuma bukatunka suka toshe, to ka yawaita Salati ga fiyayyen Halittu (S.A.W) domin salatinsa yana haskaka zuciya, yana yaye damuwa, yana kawar da bakin ciki.
6. Duk lokacin da kaji zuciyarka ta bushe ta kekashe, (Babu tsananin taushin nan na tsoron Allah) To ka yawaita karatun Alqur'ani. Domin shi karatun Alqur'ani tare da Tadabburi (zurfafa tunani) cikin Ma'anoninsa, shine fiyayyen Maganin chututtuka na fili da na boye.
7. Duk inda kaje zaka aikata Sa'bon Allah, to ka tuno da cewa yana nan tare dakai. Yana jin ka, yana kallonka. Kuma akwai ranar tsayuwarka agabansa domin karbar sakamako akan dukkan ayyukanka.
8. Duk lokacin da kazo yin addu'a, to kayi ma iyayenka kafin kayi ma kanka. Duk lokacin da ka samu wadata, to ka kyautata ma iyayenka kafin ka kyautata ma kanka. Domin su ma haka suka fifita bukatunka akan nasu bukatun lokacin kana Qarami.
9. Duk lokacin da zakayi magana da Malamai ko manyan mutane to ka sanya ladabi acikin furucinka. Duk da cewa kai baka riski Annabi ba, to sune magadan Annabawa (as). Wadannan su ke dauke da abinda aka aiko shi da shi. Allah ya datar da mu, Amin.
Shin zaka iya tsinewa azzalumin shugaba
SHIN ZAKA IYA TSINEWA AZZALUMIN SHUGABA.
الحمد لله رب العالمين ولا عدوان إلا على الظالمين، والصلاة والسلام على محمد وعلى آله وصحبه وسلم.
AMSA:La'anta tana nufin Allah yakori mutum daka rahmarsa, da nesantashi dashi, yana daka cikin la'anta zagi da cin mutunci da muguwar addu'a ga mutum.
Tsinuwa tana faruwane ta fuska biyu:
1-Mutum ya la'anci kafirai da masu sabo a dunkule, kamar mutum yace Allah yatsinewa kafirai, Allah yatsinewa mazinata, Allah yatsinewa barayi da fasikai, da azzalumai, irin wannan la'anta ta halatta, ibnu muflih yace: acikin adabul shari'a la'antar kafirai gaba daya ya halatta (1/203).
2-Tsinuwar takasance ka ayyana wani jinsi wajan la'antar taka, kamar kace Allah yatsinewa kafiri wane ko Allah yatsinewa wane ko Wane maiyin kaza Allah yatsine mar, wannan nau'i na tsinuwa shima kashi biyu ne
1-Yakasance ansamu nassi dayake nuni da la'antarsa kamar shaidan, ko kuma nassi ya tabbatar da cewa ya mutu akan kafirci, kamar fir'auna da Abu lahab, da abu jahal, la'antar wadannan ya halatta.
Ibnu muflih, yace: acikin adabul shari'a (1/214). ya halatta tsinewa kafirai wadanda nassi yatabbatar da la'antar su, babu laifi wajan kin tsine musu.
2-Tsinewa wanda nassi baizo akan la'antar saba, tahanyar ayyana shi shi kadai da sunansa kamar mai saida giya, da wanda yake la'antar iyayen sa, dawanda yake yanka ga wanin Allah, Wannan shikuma malamai sunyi sabani wajan halacci ko haramcin hakan, da maganganu guda uku.
1-Sukace bai halatta ayyana wani mai sabo ko kafiri shi kadai, ka tsinemar ba takowanne hali.
2-Sukace ya halatta akan kafiri amma banda musulmi mai sabo,
3-Sukace: yahalatta kai tsaye.
Adabul shari'a na ibnu muflih,(1/303).
Wadanda sukace ya halatta la'antar kafiri shi kadai sunkafa hujja da dalilai kamar haka.
1-Daka Abdullahi dan Umar yaji manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam idan yadago daka ruku'un sallar sa ta raka'ar karshe ta asuba yana cewa:Allah katsinewa wane da wane bayan yace Allah yaji mai gode masa, sai Allah yasaukar da yah
(ليس لك من الأمر شيء أو يتوب عليهم أو يعذبهم فإنهم ظالمون،)
Baka da wani al'amari na komi akansu, ko Allah yakarbi tubansu ko yai musu azaba lallaisu azzalumai ne, da wannan aya wasu malamai sukace bai halatta la'antar mutum shi kadai ba koda kafirine saboda da wannan aya ta sauka sai manzan Allah yadaina ambaton su daya bayan daya saidai a jam'i, saboda idan Allah yakaddara zai shiryu agaba kuma katsine mar to ka zalunceshi.
2-Daka umar wani mutum yakasance azamanin manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam ana masa lakabi da "Himaar" yanasa manzan Allah dariya, Annabi yanai masa bulala idan yasa giya sai wata rana akazo dashi yasha giya za ai masa bulala,sai wani daka cikin sahabbai yace: Allah ya tsinemar saboda yawan shan giya dayake anaimar bulala, sai manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam yace:(kada ku la'ance shi Na rantse da Allah ba'abunda nasani akansa face yanasan Allah da manzan sa.) Bukhary(6780)
Shaikul islam ibnu taimiyyah acikin majmu'ul fatwa (6/511)
Yace: la'anta ta halatta kai tsaye ga wanda Allah damanzan sa suka la'anta, amma la'antar wani ka ayyana shi ta halatta ne kadai ga wanda ya mutu kafiri, amma la'antar fasiki maisabo ka ayyana shi bata halatta ba, saboda hanin da manzan Allah yayi na la'antar Abdullahi bin himar, duk da cewa Manzan Allah yala'anci masu shan giya da mai taimakawa wajen kasuwancin ta adunkule, tare dacewa la'antar mai sabo ka ayyanashi akwai sabanin malamai.
Shaeik uthaimeen Rahimahullah acikin qaulul mufeed (1/226) yace:
Banbaci tsakanin la'antar masu sabo adunkule dakuma la'antar wani ka ayyana shi, nafarko la'antar wani ka ayyana shi anhana, nabiyu la'antar masu sabo adunkule ya halatta, idan kaga mai taimakawa barna bazakace Allah yatsine maka mabarnaci ba, a'a sai dai kace Allah yatsinewa mabarnata, dalili akan haka shine lokacin da manzan Allah yake tsinewa wasu mushirikai acikin qunuti, yana ambatarsu da sunayensu, Allah ya hana shi hakan da fadinsa madaukakin sarki
(ليس لك من الأمر شي ء أو يتوب عليهم أو يعذبهم فإنهم ظالمون)
Baka da wani al'amari na komai akansu kodai Allah yakarbi tubansu ko kuma yai musu azaba hakika su azzalumaine. Bukhary
Wallahu A'alam.
Saboda haka la'antar shugaba koda azzalumine kuma koda fasikine haramunne ba koyarwar musulunci bace, koda kafirine matukar bai hanaku yin addinin kuba tsinemar da zaginsa dayi masa muguwar addu'a haramunne, kamar yana hanaku azumi ko sallah ko wata ibada ko yada addininku, saboda hadisai dasukai hani da hakan.
Ankarbo daka Abu umamah daka Annabi sallallahu Alaihi wasallam yace: ( kada ku zagi shugabanni, ku roka musu shiriya da gyaruwa awajan Allah domin gyaruwarsu gyaruwarkuce.)
Kuma tsinuwa da aibantawa ba al'adar mutumin kirki bace wanda yakebin koyarwar Annabinsa sallallahu Alaihi wasallam, saboda hadisi ya inganta manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam yace: ba'asan musulmin kirki da tsinuwaba, ko sakin harshe yaita maganganu bakai bagindai, ko zancen banza,
Muna rokon Allah madaukakin sarki yatabbatar da dugadugnmu akan abunda yakeso kuma yayarda dashi.
Wallahu A'alamu.
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك.
*TAMBAYOYIN MUSULUNCI*
*WhatsApp Group*
Menene hukuncin magana a cikin bandaki
MENENE HUKUNCIN MAGANA ACIKIN BANDAKI
الحمد لله والصلاة والسلام على محمد وعلى آله وصحبه وسلم.
AMSA:Makaruhine ambaton Allah awajan biyan bukata, dan girmama sunan Allah madaukakin sarki bai kamata ka ambaceshi agurin najasaba, wanda kuma makwancin shaidanu ne.
Imamun nawawy rahimahullah yace: acikin littafin al'azkaar, [ makaruhine ambaton Allah alokacin da mutum yake biyan bukata, a sahara yake jeji kenan dajin Allah ko agurin da angina shi dan biyan bukata kawai, bawai Ambaton Allah kawai ba, dukkanin zikirai da zance na duniya inba da lalura ba, idan mutum yai attishawa abandaki bazai tahmidi ba kuma baza'a amsa masa ba, haka idan mutum yana biyan bukata bazai amsa sallama koya mayar ba, haka kuma bazai amsawa mai kiran sallah ba, zance a wadannan gurare makruhine, dan tsarkake sunan Allah madaukakin sarki amma ba haramun bane, idan mutum yai attishawa sai ya godewa Allah azuciyarsa, harshensa bai motsaba babu laifi, haka zai aikata ahalin dayake jima'i da matarsa.
Dalili shine hadisi daka Abdullahi dan umar Allah yakara yarda dasu yace: Wani mutum ya wuce manzan Allah yana fitsari sai yaiwa manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam sallama bai amsa masaba,) Muslim (370).
Sabida haka idan wajen alwala yakasance acikin bandaki ban dakin kuma bawajen wankane kawai ba, hukuncin karhancin ambaton Allah maganganun malamai sunci karo da juna awannan wajen tare da halaccin yin bismillah, wasu malaman suntafi akan zaiyi bismillar azuciyarsa batare daya furta da harshen saba.
Wasu malaman kuma sukace: zai yi bismillah da harshen sa ayayin alwala abandaki awannan lokacin babu karhancin.
Yazo afatawar lajnatul da'ima cewa:"makaruhine ambaton Allah agurin da ake biyan bukata dan tsarkake sunan Allah da girmama shi, amma ya halatta yayi bismillah yayin fara alwala domin wajibice awajen dayawa daka cikin malamai.
Idan wajen alwala yakasance wajen bandaki koda ajikin bandakin yake kamar katanga daya gurin yake data bandaki, yahalatta ga mai alwala yafurta bismillah awannan hali domin awajen bandaki ne.
Saboda haka zance abandaki makruhine koda ba ambaton Allah bane, amma idan bukata ta kama yahalatta kamar kana wanka ruwa yakare ma, zakai magana dakarfi akawo ma ruwa ka karasa, ko kana gidan wanka nakudi shaya tadauke ruwa zakai magana babu ruwa da makamantan uzuruka dazaka bukata aima kanada daka cikin bandaki, wallahu A'alam
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك.
Tambayoyin musulunci
Watsapp
Mu kyautatawa juna zato
*MU KYAUTATAWA JUNA ZATO*
*_WANI DAGA CIKIN SALAF (MAGABATAN FARKO NA KWARAI) YANA CEWA:_*
_*Idan naga ruwan giya suna diga daga gemun mutum, to zance wataqil giyar ta zubar masa ne*_ Wato abinda yake nufi anan tunda dai bai ganshi yana shan giyar ba a zahiri ba to lallai ba zaice ya ganshi yana shan giya ba.
*HAKA KUMA YA QARA DA CEWA:*
*_Haka kuma idan na ganshi a saman tsololuwar tsauni yana cewa_; " *NI NE UBANGIJINKU MAFI DAUKAKA* " ( *ANA RABBUKUMUL A'ALA* ). *_Anan kuma zance wannan yana karanta_* *AYA CE DAGA AL-QUR'ANI MAI GIRMA*
Kaji *swalihan* bayi kenan, duk fa wannan yana yine akan tsananin kyautatawa musulmi zato, yi masa uzuri da kuma gujewa yin shaidar zur.
Yanzu mutanen wannan zamanin wa zaiga giya na zuba daga gemun mutum yace wai ba giyar ce ya gama sha ba? Haka kuma wa zai ga mutum saman qololuwar tsauni yana kwala ihu yana fadar *_NI NE UBANGIJINKU MAFI DAUKAKA_* Har yace bawai kansa yake kira Allah ba, ai ayar qur'ani ce yake karantawa?
Kuma wannan itace dabi'ar da ake son musulmai su dabi'antu da ita ta kaucewa yin shaidar zur, kyautatawa juna zato da kuma gujewa munanawa musulmi zato kamar yanda dimbin ayoyin Al-qur'ani da ingantattun hadisai suka hore mu.
*Allah ya bamu ikon kyautatawa junanmu zato. Ameen*
*TAMBAYOYIN MUSULUNCI*
Wednesday, 19 October 2016
Hukuncin yin tsarki da ruwan wanka
HUKUNCIN YIN TSARKI DA RUWAN WANKA TAMBAYA TA 2002 ******************** Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah, Malam ya hidima da ake tayi damu dalibai, Allah ya saka da alkhairi. Allah ya albarkaci Zuri'a, Amin. Malam Nayi dahara da ruwan da nayi wanka dashi da niyyar idan na fito zan Kuma yi da wani ruwan daban. Dana fito sai na manta har nayi sallar azahar da laasar, Sai na tuna da magriba. Malam ya zanyi na gyara. Bissalam. AMSA ******* Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Hukuncin ya danganta da irin yanayin ruwan wankan. Idan ruwan wankan sabulu ne, Kuma ya riga ya chakude da sabulun, to lallai wannan tsarkin naka bai yiwu ba. Kuma zaka rama dukkan sallolin da kayi da wannan tsarkin. Amma idan wankan ibadah kayi, ko kuma wankan sanyaya jiki, to ya halatta kayi tsarki da irin ragowar ruwan wadannan wankan. Mutukar dai siffofinsa basu chanza ba. WALLAHU A'ALAM. DAGA ZAUREN FIQHU
Hukuncin amsa sallamar kifiri
HUKUNCIN AMSA SALLAMAR KAFIRI
TAMBAYA TA 2001
********************
Assalamu alaikum. Allah ya qarawa malam Eamani ya jiqan iyaye. Ameen, tambaya nake roqon a amsa min.
Yaya hukuncin Wanda ya shaaku da Wanda ba musulmi ba kuma ya dauke shi a matsayin aboki?
kuma shin ya kamata a mayar ma Wanda ba musulmi sallama idan yace ma Assalamu alaikum?.
Dafatan malam zai samu damar amsa tambayata.
daga dalibinka Ibraheem I g
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Allah Madaukakin Sarki ya umurcemu da cewa kada mu riki Yahudu da Nasaara amatsayin Masoya ko Majibinta garemu. Ba don komai ba, sai domin sharrin da irin hakan zai haifar ga rayuwarmu da addininmu.
Allah Madaukakin Sarki yace : "YA KU WADANDA SUKAYI IMANI! KADA KU RIKI YAHUDU DA NASAARA AMATSAYIN MAJIBINTA (WATO ABOKAI KO MASOYA) SASHENSU MAJIBINTA NE GA SASHE. DUK WANDA YA JIBINCESU DAGA CIKINKU TO HAKIKA SHIMA YANA CIKINSU. HAKIKA ALLAH BA YA SHIRIYAR DA MUTANE AZZALUMAI".
(Ma'idah ayah ta 51).
Ibnu Abi Hatam ya ruwaito cewa Watarana azamanin Khalifancin Sayyiduna Umar (rta) ya ce ma Sayyiduna Abu Musal Ash'ariy (rta) ya rubuto masa wani abu.
Shi kuma Abu Musal Ash'ariy sai ya sanya wani kirista (Nasaara) ya rubuta masa. Daga karshe da Sayyiduna Umar ya gane hakan sai da yayi masa fa'da sosai. Sannan ya tunasar dashi wannan ayar da muka kawo a sama.
Babu laifi ka kyautata alakar zamantakewa tare dasu awajen aiki ko kasuwa. Amma kar ka rikesu amatsayin abokai ko aminai gareka.
2. Dangane da amsa sallamarsu, akwai maganganun Malamai kala-kala. Amma magana mafi rinjaye ita ce wacce Ibnul Qayyim ya kawo acikin ZADUL MA'AD juzu'i na 2 shafi na 425-426, yace :
"Malamai sunyi sa'bani dangane da wajibcin amsa sallamar wanda ba Musulmi ba (idan yace maka Assalamau alaikum) amma Mafiya rinjayen Maluma sunce wajibi ne. Kuma wannan shine ra'ayi mafi Sahihanci.
Sannan Malaman sunce zaka mayar masa da cikakkiyar Sallama ne bisa gwargwadon yadda Allah yayi umurnin cewa :
"IDAN AKA GAISHEKU DA WATA GAISUWA, TO KU MAYAR DA IRIN WACCE TAFI KYAWU, KO KUMA KU MAYAR DA ITA (KAMAR YADDA AKA YI MUKU)".
WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU
Hukuncin hana daukar ciki wato family planning
الحمد لله والصلاة والسلام على محمد وعلى آله وصحبه وسلم.
AMSA:Abunda yakamata musani asali shine kowanne cikin ma'aurata yanada hakki wajan samuwar 'ya'ya, bai halatta ga miji yaiwa matarsa azlu ba, saida izininta, haka mata ma bata da iznin bin wata hanya dan hana daukar ciki saida iznin mijinta, Mausu'atul fiqhiyyah (3/156).
Yazo acikin baharul raã'uuq (3/215) ya kamata mace tasani kawar da abunda ke mahaifarta ko toshe samuwar ciki a mahaifarta haramunne inba da iznin mijin taba.
Ibnul muflih Alhambaly yace:" ya halatta ga mace tasha magani na halal danta yanke zuwan jini haila, Alqazy yace: " da izinin mijinta kamar azlu" yana karfafa maganar Ahmad bin hambal awani yanki na jawabinsa, mace zata nemi iznin mijinta, Alfuru'u (1/392) Marudy yace shine dai-dai.
Alqazy yace: bai halatta ba saida izinin miji domin yana da hakki akan dah, kashshaful qina'a (2/96).
Sai dai idan ansamu wani uzuri na bayyane akan mace cewar bazata iya daukar ciki ba, kamar daukan cikin yana sabbaba mata cuta bayyananniya tahanyar shaidar kwararrun likitoci, a wannan halin, hakkin miji yake gushewa wajen neman izninsa, domin maslahar mace wajen kiyaye lafiyarta itace abar gabatar wa, akan maslahar miji wajan samun cikin dah, Manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam yace: "Babu cuta ba cutarwa"" ibnu majah ya ruwaito shi (2340) Nawawy ya hassana shi acikin littafinsa Al'azkaar (502).
Balma malamai sun halatta zubda cikin dabai haura kwana arba'in ba matukar cigaba da zamansa zai shafi lafiyar mace.
Yazo afatawar sheik uthaimeen Rahimahullah Antambayeshi, Ni inada aure, mijina kuma bayasan na sha kwayoyin hana haihuwa, amma baisan wahalar danake haduwa da itaba, ina cutuwa akan hakan, nikuma nash kwayoyin hana haihuwa batare da snin miji naba, shin akwai laifi akan hakan?
Sai malam ya amsa: Idan zaki iya barin kwayoyin shi yafi,Amma idan cutar mai girma ce, kuma wahalar babba ce, babu laifi, amma barin kwayoyin shi yafi,sai idan cutar babbace, kuma yana wahalar dake, saboda fadin Allah madaukakin sarki (Kuji tsoran Allah dai-dai iyawarku)
Fatawa uthaimeen (21/184).
Shaeik uthaimeen yace : wajibine akan namiji yakula da matarsa idan yaga tana shan wahala, shan wahalar dabai saba ganin tanayi inta dau ciki abaya ba, yaimata izni wajan shan maganin dazai hana daukar cikin, koshi dakansa yai mata abunda dazata daina daukar cikin koya kawo mata, dan nuna tausasawa agareta, da jinkai agreta, harsai tasamu lafiya, ta kuma samu karfin jikinta. fatwa nurun alal darbi.
Amma munin halin miji, narashin iya zama da mace, da munanan dabi'unsa ba uzuri bane, ba hujja ba ce, ta hana daukar ciki, hakika Allah yana iya sanya canji da alkhairi mai yawa atare da dan, kamar yanda Allah madaukakin sarki yace:( Yana fitar da rayayye daka matacce yafitar da matacce daka rayayye).
Hakama yace:( Zaku iya kin wani abu, Alhalin alkhairine atare daku, haka kuma zaku iya san wani abu amma sharri ne atare daku).
Dan haka shan magani danyin family plannin haramunne, saida yardar dukkan bangarori biyu na ma'aurata kuma saida lalura babba wacce take barazana ga lafiyar mace, kuma da tabbatarwa likitoci amintattu kuma kwararru masana, duk da haka sai in cutar tagirmama tayanda daukar cikin na iya kaiwa ga halaka ga ita macen, duk dahaka dazarar wannan matsala ta wuce, babu wani dalili na yin family planning.
Wallahu a'alam
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك.
*🌙Tambayoyin Musulunci🌙*
*WhatsApp Group*





