2017 ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Friday 29 December 2017

TARIHIN MATAYEN GIDAN ANNABI (SAWW) - KASHI NA BIYU

TARIHIN MATAYEN GIDAN ANNABI (SAWW) - KASHI NA BIYU.

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

Salati da amincin Allah da albarkokinsa da rahamarsa su tabbata bisa Babban Masoyin Ubangijin Talikai. Annabin da Ubangijinsa ya tsarkake Garinsa da Nasabarsa da iyalan gidansa da Matayensa

Salatin ya hada da Sahabbansa da dukkan alayensa da mabiyansa har zuwa ranar da Qasa zata fitar da nauye-nauyen da take dauke dashi.

Idan Daliban ZAUREN FIQHU suna biye damu, awancan darasin mun kawo tarihin Babbar Uwargidan Manzon Allah (saww) wato Nana Khadeejah bintu Khuwailid (rta).

Yau kuma in sha Allah zamu dora da tarihin wacce take biye da ita wajen Shigowa wannan gidan Mai Albarka. wato Sayyidah Saudah (yardar Allah ta tabbata gareta).

NANA SAUDATU (RTA)

SUNANTA DA NASABARTA
*****************************
Nana Saudah (rta) ita ce mace ta farko wacce Ma'iki (saww) ya aura bayan rasuwar Nana Khadeejah (ra). Kuma nasabarta ita ce kamar haka :

Mahaifinta : Sunansa Zam'atu bn Qays, 'dan Abdu Shamsi, 'dan Abdu Wadd,  'dan Aamiru, 'dan Lu'ayyu 'dan Ghalibu.

Wato nasabarta ta hadu da ta Manzon Allah (saww) akan Kakansa Lu'ayyu bn Ghaalib.

MAHAIFIYARTA : Sunanta Ash-Shamoos bintu Qays bn Zayd. 'Yar Qabilar Banun Najjar ce daga garin Madina.

Wato Mahaifiyarta tana da kusancin nasaba da dangin Mahaifiyar Abdul Muttalib (Kakan Manzon Allah saww).

Nana Saudah tana daga cikin mata masu alfarma da girman Nasaba acikin Quraishawa. Kamar yadda Imam Zahabiy ya fada acikin littafinsa na tarihi.

Babban Malamin Tarihin Musuluncin nan wato Ibnu Sa'ad yace : Saudatu bintu Zam'ah da ita da Mijinta As-Sukraan bn 'Amru (ra) - 'dan Uwan babban Sahabin nan Suhaylu bn Amru (ra) suna daga cikin mutanen da suka fara karbar Musulunci. Kuma daga baya sukayi hijira tare zuwa Qasar Habasha.

(Aduba Tabaqat Alkubra na Ibnu Sa'ad, Juzu'i na takwas, Shafi na 57).

HIJIRARTA ZUWA HABASHA
*******************************
Kasancewar Nana Saudah tana daga cikin farko farkon shiga Musulunci, da ita da sauran Sahabban Manzon Allah (saww) sun fuskanci Tsanantawa da wulakantawa da chutarwa mai tsanani daga Kafiran Makkah.

Yayin da chutarwar ta tsananta, Sai Manzon Allah (saww) ya basu Umurnin cewa suyi hijira zuwa Qasar Habasha har sai abubuwa sun daidaita. Domin kuwa Sarkin Qasar yana da adalci kuma ba ya yarda da duk wani zalunci.

Don haka wasu daga cikin Sahabban sukayi Hijira zuwa chan Qasar Habasha din. Wasu sun tafi tare da iyalansu, wasu kuma su kadai suka tafi.

To ita Nana Saudah tayi hijirar tare da Mijinta As-Sukraan bn Amru tare da wasu mutum takwas daga Banu 'Amru.

Saboda Qarfin imani irin nata tun alokacin, ta kyale dukiyarta da iyayenta da dukkan abinda ta mallaka, ta tafi domin tseratar da Imaninta. Hakanan Allah yake jarrabar bayinsa Muminai domin ya Qarfafa imaninsu.

Suna chan suna zaune cikin aminci a Qasar Habasha, sai wani labari marar tushe ya iskesu cewar wai yanzu komai yayi kyau agarin Makkah, kafiran sun dena chutar da Muminai.

Jin haka yasa wasu da dama daga cikin masu hijirar suka dauko hanya suka dawo gida.

Suna shigowa garin Makkah sai suka tarar ashe labarin nan da aka basu ba haka abin yake ba.

Nan take suka fara fuskantar matsaloli fiye da da. Kuma kafiran suka Qara Qaimi wajen tsananta musu.

Shi kuwa Mijin Nana Saudatu tun akan hanyar dawowa gida ya kamu da rashin lafiya. Don haka basu jima sosai da komowa ba, sai Allah ya karbi ransa (Allah shi Qara masa yarda).

Shi kuma Manzon Allah (saww) babu dadewa Matarsa wacce yake ji da ita, wato Nana Khadeejah bintu Khuwaylid (ra) ta rasu. Acikin shekara guda tare da baffansa Abu Talib.

Wannan rasuwar tasu ta zamo babbar abin bakin ciki sosai agareshi. Domin kuwa Abu Talib shine yake kareshi daga maganganun da kafiran suka gaya masa. Kuma sun kasa tasowa gadan-gadan domin dukansa ko Kasheshi saboda albarkacin suna ganin girman Abu Talib din.

Ita kuma Nana Khadeejah ita ke kwantar masa da hankali duk lokacin da ya shiga cikin damuwa. Kuma tana Qarfafarsa akan duk abinda zai gudanar.

Saboda hakane su kansu Sahabbansa maza da Mata suka rika tayashi bakin cikin wadannan rasuwar.

Watarana Manzon Allah (saww) yana zaune sai ga wata daga cikin Mataye Sahabbai tazo wajensa. Sunanta Khaulatu bintu Hakeem (Matar Uthman bn Maz'un rta).

Tace masa "Ya Rasulallahi lallai kana cikin damuwa game da mutuwar Khadeejah".

Yace mata "Kwarai kuwa. Ita ce Mahaifiyar 'Ya'yana, kuma Uwargidan wannan gidan".

Sai tace "Ya Rasulallahi ko zaka yi aure?

Sai yace "Wa zan aura?".

Sai tace "Akwai Budurwa, akwai kuma Bazawara, Sai wacce kake so".

Sai yace "Shin wacece Budurwar?". Sai tace "A'ishatu bintu Abubakrin, 'Yar mafi soyuwar Mutane agareka".

Sai yace "To wacece Bazawarar?". Sai tace "Saudatu bintu Zam'ah.  Wacce tayi imani da Manzancinka, kuma tana bin Umurninka".

Daga nan sai Ma'aiki (saww) yayi farinciki  kuma yayi mata izinin taje ta nema masa duk guda biyun.

Da farko ta shiga ta gidan Sayyiduna Abubakrin, sannan ta fito ta nufi gidan su Saudah (ra).

Ta shiga wajen Saudah tayi mata albishir tana cewa : "Hakika Ubangiji ya sanya albarkarsa da falalarsa agareki Ya ke Saudatu!".

Sai Nana Saudah tace "Menene ya faru?" sai tace "Ai Manzon Allah ne (saww) ya turoni domin in gaya miki yana so zai aureki".

Daga jin wannan sai murna ta lullubeta, tace ma Khaulah "Kije wajen Mahaifina ki shaida masa".

Anan zamu tsaya, sai a darasi na uku zamu ci gaba in sha Allahu. Da fatan ALLAH shi albarkaci dukkan daliban Zauren Fiqhu, Allah ya saka ma kowa da alkhairi. Allah shi bamu ikon koyi da magabatanmu na kwarai.

An gudanar da karatun ne a ZAUREN FIQHU WHATSAPP (3) Ranar Juma'a 12 ga November 2015.
Share:

MAFI TSADAR ADDU'O'I (12) DA SUKA ZO A HADISAN MANZON ALLAH (S.A.W)

MAFI TSADAR ADDU'O I GUDA (12) DA SUKA ZO A HADISAN MANZON ALLAH (S.A.W)

1. LA'ILAHA ILLAHUWA WAHADAHU LA SHARIKA LAHU LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDA WA HUWA ALA KULLI SHAY'IN QADIR (10 ko 100)

Manzon Allah (S.A.W) yace wanda ya fadi wannan 100 za a kankare masa zunubai dari kuma za a rubuta masa kyawawan aiki dari Kuma a wannan rana bawani da zaizo da wani aikin alheri kamar nasa sai wanda ya fadi fiye da abinda ya fada kuma za tsareshi daga sharrin shaidan da duk wani abun qi Kuma yace babu wani zikiri ko addu'a kamar Hailala

2. LA'ILLA HA ILLAHUWA MALIKUL HAQQUL MUBIN. (100)

Manzon Allah(S.A.W) yace duk wanda ya fadi wanann sau dari a rana bashi ba talauci kuma za'a tsareshi daga fitinar kabari

3. BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM, LA HAULA WALA QUWATA ILLA BILLAHIL ALIYUL AZEEM. (100)

Manzon Allah(S.A.W) ya cewa da Sayyadina Aliyu ba wanda zai fadi wannan kalmomi duk wata masifa ko bala'i duk rintsi sai ya fita.

Annabi Alaihisalam yace wanda yake karanta Lahaula bashi ba talauci kuma kanzi ce daga kanzi na aljanna tana toshe kofofi saba'in na bala'i da cuta mafi kankanta ciki shine bacin rai da damuwa kuma yace: duk wanda samun arziki yayi masa wuya to ya yawaita yin LAHAULA...

Kuma duk wanda yake karanta BISMILLAH (21) bayan isha'i cutar annoba ko ta dauka bazata taba kamashi ba kuma bazai mutuwar fuju'a ba

4. SUBAHANALLAHI WA BI HAMDIHI. (100)

Shine Tasbihin Annabi Nuhu shi kuma mala'iku suke Allah yake arzuta dukkan halitta dashi.

5. HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL(450)

Shine Tasbihin da Annabi Ibrahima yayi lokacin da aka jefa shi wuta Allah ya mayar masa da ita sanyi itace Shabai sukayi lokacin yaqin Badar Annabi yayi nasara kuma basu ji tsoron kafirai ba duk da sunfisu yawa.

6.  LA ILA HA ILLA ANTA SUBAHANAKA INNI KUNTU MINAL ZALIMIN (sau 41 ko 100)

Manzon Allah(S.A.W)  yace: "Addu'a Annabi Yunusa lokacin da ke cikin kifi babu wani mumini da zai roki Allah wani abu dake damunsa face Allah ya maganata masa kuma yace Ismullahil Azeem sunan Allah da in Aka addu'a yake amsawa kuma idan aka rokeshi yake bayarwa itace addu'a Annabi Yunusa.

7. ASTAGFURULLAHA LAZI LA'ILA HA ILLAHUWAL HAYYUL QAYYUM WA ATUBU ILAIHI. (100)

Manzon Allah(S.A.W) yace: Ba wanda zai fadi haka fache an gafarta masa zunubansa koda sun kai kunfar kogi. kuma Alqawarin Allah ne a cikin Suratul hudu duk wanda ya lazumci Istigfari zai jiyar dashi da dadi kuma yabashi arziki kan arziki(zai samu budi)  kuma zai bashi girma akan girma Daukaka

8. SUBAHANALLAHI WABI HAMDIHI SUBAHANALLAHIL AZEEM ASTAGFRULLAH(100 kafin Asubah)

Wani Sahabi yazo wajen Manzon Allah Alaihisalam yayi masa kukan duniya ta juya masa baya(talauci)  yasanar dashi tasbihin Mala'iku sai Annabi yasanar dashi yace ya dingayi shi bayan raka'a tainul fajar kafin Asubah bai gushe ba sai da ya dawo wajen Annabi Alaihisalam yace Allah yabashi duniya (arziki)  har ya rasa inda zai kaita

9. YA HAYYU YA QAYYUM LA'ILA HA ILLA ANTA(sau41)

Imamu Shafi'i(Rahimahullah) yayita mafarki da Annabi sai watarana sai yace shin kasanar dani wani abu da Allah zai dinga haskaka mani kuma ya raya zuciyata akan imani(ibada)  sai Annabi ya sanar dashi wannan ya dingayi kafin Asubah ko bayan Asubah sau 41 (Saboda haka ba wanda zai lazumceta sai yazama mai maida hankali akan ibada kuma yazama wanda mutane zasu dinga jin maganarsa kuma abin so a cikinsu

10. SUBAHANALLAHI(33) WAL HAMDULLAHI(33) WAL LAHU AKBAR(34) da dare kafin bacci

Wannan shine Tasbihin da Annabi ya bawa Sayyada Fatimah lokacin da ta nemi Annabi ya bata hadimi sai ua snaar da ita wannan tasbihi da ta dingayi kullum kafin ta kwanta bacci shine mafi alkhairi gareta da yabata hadimi

11. SUBAHANALLAHI(10) WALHAMDULLAHI(10) WALLAHU AKBAR(10) bayan Salloli biyar

Watarana Ummu Sulaim tazo wajen Annabi Alaihisalam tace ya sanar da ita wani abu da zata dinga rokon Allah dashi sai yace tayi wannnan tasbihin sai ta roki Allah bukatarta za ace anzartar anzartar (wato an amsa mata abinda ta roka)

12. SALATIN ANNBI (10 ko 100 ko 500 ko 1000 har abinda yayi sama)

Manzon Allah(S.A.W)  yace: "wanda bukatarsa tayi masa wahalar samu to  ya yawaita salati gareni lalle yana tafiyar da damuwa da bakin ciki da kuncin rayuwa kuma yana yawaita arziki da kuma biyan bukatu.

Allah kasa mu dace, Amin.

DAGA ZAUREN TAFSIR DA SUNNAH

Share:

Thursday 21 December 2017

DAUSAYIN IYALI 002 - Dr. Mansur Ibrahim Sokoto


*DAUSAYIN IYALI 002*
Matsayin Mata da Hakkokinsu a Musulunci

Littafin *Dr. Mansur Sokoto*

 Matsayin Mata Kafin Zuwan Musulunci
Abu ne da tarihi ya tabbatar cewa, Macce ba a dauke ta a matsayin
kammalallen dan Adam ba kafin zuwan Musulunci. Domin kuwa an
mayar da ita kamar Haja wacce ake saye kuma ake sayarwa, ake kuma
gadon ta kamar yadda ake gadon gida ko gona ko duk wata kaddara
da Namiji ya mutu ya bar ta. Akan umurci Macce ta yi Zina don ta kawo
kudi, kuma ana aurar da ita ne yadda aka ga dama, ba tare da neman
zabinta ko ma shawartar ta ba.
A da Namiji yakan auri ko Mata nawa yake so kuma ya ga dama kamar
yadda yake iya mallakar riga da hula ko nawa yake so.
A wasu sassan duniya ba a yarda Macce mutum ce ba ma sam. Misali,
a qasar Rasha Malaman addini sun ba da fatawar cewa, Macce najasa
ce, matsayinta daya ne da na Kare.
A yankin Larabawa, zamanin Jahiliyya, uba yakan sayar da diyarsa.
Yakan kuma rufe ta cikin qasa babu gaira babu dalili. Kawai dai
haifuwar ta ba abin farin ciki ba ne balle ai alfahari. Budurwa tana goge
gumi daga fuskar babanta a lokacin da yake haqa ramin rufe ta, amma
ita ba ta sani ba.
Kashe Macce - kafin zuwan Musulunci - ba wani babban laifi ba ne da
har za ayi maganar Qisasi ko Diyya a kan sa.
A qasar Indiya akan qone Macce ne tare da mijinta idan ya mutu,
alhalin tana da ranta da lafiyarta. Wannan ya sa sau da yawa Macce
takan kashe kanta bayan mutuwar mijinta irin mutuwar da take ganin
ta fi mata sauqi, don kauce ma wannan baqar mutuwa da mummunan
bala'i.
Malaman addinai biyu da ake a da su a lokacin wadan da suka samo
koyarwarsu daga manyan Annabawa ba su tabuka komai a kan wannan

- Yahudawa - mabiyan Addinin Annabi Musa Alaihis Salam sun dauki
Macce a matsayin najasa duk lokacin da take Haila. Ba za su ci abincin
da ta dafa ba, ba kuma za su kusance ta ba. A maimakon haka sai su
kafa ma ta rumfa a bayan gida - kamar yadda ake turke Akuya - su riqa
ba ta ruwa da gurasa har sai lokacin da ta gama al'ada sannan ta dawo
cikin gida.
- Su kuma Kiristoci duk da ba su nuna qyamar ta a wannan lokaci.
Kuma ma har saduwa suke yi da ita a lokacin da take Haila. Amma ba
za mu dauka cewa sun mutunta ta ba tun da yake suna kallon ta a
matsayin ita ce ummul-haba'isin duk wani laifi da sharri da cuta da ake
yi a duniya. Kuma wai, ita ce qofar shiga wuta. Suna kafa hujja da
cewa, wai, ita ce ta bai wa Annabi Adam (Alaihis Salam) shawarar cin
bishiyar da Allah ya hana shi har ta jawo ma su uqubar fita daga gidan
aljanna.


*Kusaurari cigaba da izinin Allah*

Gabatarwa a social Media
*Ibrahim Nasidi Baban Ilham*
Share:

DAUSAYIN IYALI - Dr.mansur ibrahim sokoto



*DAUSAYIN IYALI*
Matsayin Mata da Hakkokinsu a Musulunci Fitowa ta 001
Littafin Dr. *Mansur Sokoto*
Gabatarwa
Addinin musulunci kammalallen addini ne, wayayye, kuma wanda ya
game duk sassan rayuwa, sannan ya dace da kowane zamani da
kowace al’umma. Ko kuma ma mu ce, kowane lokaci da kowane
zamani sun dace shi.
Babu wani tsari ko wata doka da suka kai kyan tsari da dokar Musulunci
ballatana su wuce shi. Addini ne da Allah mahaliccin bayi ya tsara
komai a cikin =ad a yadda bayin Allah za su samu nagartacciyar
rayuwa idan suka bi tafarkinsa.
Mata su ne rabin al’umma. Kuma rabi ne mai muhimmanci. Domin su
ne masu haifuwar Mazan da Matan duka. Amma kuma an dade ba a
gano daraja da matsayin wannan jinsi na Bil-Adama ba.
Kyakkyawan zatona shi ne wannan nazari zai ba da dogon haske, kuma
a taqaice kan wannan batu.
*Kusaurari cigaba da izinin Allah*
Gabatarwa a Social Madia *Ibrahim Nasidi Baban Ilham*
Share:

Monday 18 December 2017

Ba'a Yi Duniya Don Manzon Allah S. A. W Ba!!! Dr Jamilu Yusuf Zarewa



*_Tambaya_*

Assalamu alaykum Don  Allah Dr, shin ya Halatta ace anyi duniya don manxon Allah?

*_Amsa_*
Wa alaikum assalam,

Ba'a yi mutanan duniya don Manzon Allah ba, an yi mutanan duniya ne don su bautawa Allah.
Allah madaukakin sarki yana cewa a cikin suratu Azzariyat aya ta (56) "Ban halicci  mutum da Aljan ba sai dan su bauta min, bana bukatar wani arziki a wajansu kuma bana bukatar su azurta ni"
Ayar da ta gabata ta bayyana dalilin da yasa Allah ya halicci mutane da Aljanu, wato bautawa Allah da kuma tsayar da tauhidi.

Babu wani nassi ingantacce yankakke wanda ya nuna an yi duniya saboda Manzon Allah S.A.W. hakan kuma ba ya nuna an tauye manzon tsira.

Annabi S.A.W. bawa ne daga cikin bayin Allah kamar yadda tarin ayoyin Al'qur'ani suka tabbatar da hakan, sannan shugaban 'ya'yan Annabi Adam kamar yadda ya tabbata a hadisai ingantattu a kundayan musulunci.
Ajjiye shi a matsayinsa da Allah ya ajjiye shi, shi ne daidai kamar yadda yake cewa "Kada ku wuce gona-da-iri wajan yabona kamar yadda nasara suka wuce a lamarin Isa dan Maryam"

Allah ne mafi sani

*_Dr, Jamilu Zarewa_*

02/12/2017
Share:

ZAKKAR GIDAN HAYA DA MOTAR HAYA - Dr.jamilu yusuf zarewa

*_ZAKKAR GIDAN HAYA DA MOTAR HAYA_*


*_Tambaya_*

Assalamu alaikum
Malam Shin ko akwai zakka akan Gona, Fili ,Gidan haya da Motar Haya?


*_Amsa_*
Waalaikumussalam

To dan'uwa duk gonar da aka rika don ayi amfani da ita, to babu zakka a cikinta, haka nan fili, amma idan kasuwanci ake yi da su, kamar a siya a sayar to za'a fitar musu da zakka, idan sun cika nisabi kuma shekara ta zagayo musu, ko kuma ya zama  sun cika sharudan zakka idan ya hada su da abin da ke hannunsa .
Haka nan babu zakka a cikin gidan haya saidai idan aka tara kudin kuma shekara ta zagayo akan su, sun cika nisabi, to anan ne za'a fitar musu da zakka, ko kuma ya zama sun cika sharudan zakka idan ya hada su da abin da ke hannunsa .

Allah ne ma fi sani .

*_Dr. Jamilu Zarewa_*

18/12/2014

Gà dukkan mai son shiga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH* sai ya yi saving wannan number +2348122248585 sannan ya tura da sunansa da adireshinsa ta whatsApp.Duk abun da mutum ya turo matukar ba suna ba ne ba za a kula shi ba.
Share:

Saturday 9 December 2017

Goron Juma’a: Mutanen da Allah ba ya kauna a Duniya

- Mun kawo Mutane 4 da Allah ba ya kauna a Duniya

- Daga ciki akwai tsohon da ya tsufa ba ya gudun zina
- Akwai kuma Matalaucin mutum mai mugun girman kai
A Rana irin ta yau mun kawo maku wani Hadisi na Manzon Allah Annabi Muhammadu SAW inda ya bayyana wasu mutane 4 da Ubangiji Madaukaki ba ya kaunar su a Duniya saboda mugun halin su. Wadannan mutane dai su ne:-

1. Matalauci mai girman kai
Kamar yadda Marigayi Malam Ja’afar Mahmud Adam ya bayyana daga cikin wadannan mutane akwai wanda ke fama da mugun talauci amma kuma yake da dan-karen girman kai.

2. ‘Dan kasuwa mai yawan rantsuwa
Haka nan kuma akwai ‘dan kasuwar da yake yawan rantsuwa bini-bini a duk lokacin da zai saida kaya a kasuwa. Musamman kuma ace mutum karya yake yi wajen ratsuwar.

3. Dattijo mai yawan zina
Akwai kuma tsohon da ba ya gudun zina duk da shekarun sa sun yi nisa amma ba ya jin tsoron Allah. Ubangiji Madaukaki SWT ba ya son irin wannan mutumi.

4. Azzalumin mai mulki
Na karshen su dai a Hadisin shi ne kuma wanda ya samu mulki amma kuma yake kuma kuntatawa Jama’ar sa na Talakawa da damar da ya samu.

Share:

*'YAN SAMARI MINTI BIYU 03

*'YAN SAMARI MINTI BIYU 03*

Duk wanda ka gani da arziki tashi ya yi ya nema sai Allah Ta'ala Ya bashi domin sama ba ta ruwan zinariya.

Manzon Allah, sallallahu' alaihi wa sallama, Ya ce a cikin hadisin da Abi Hurairah ya riwaito: *"Ina rantsuwa da wanda Raina ke hannun Shi, dayan ku ya dauki igiya ya je ya yi itace ya dauko shi a bayansa, shi ya fi masa alheri fiye da ya je wurin wani mutum yana rokon shi koda kuwa wannan mutumin ya bashi abun da ya roka ko ya hana shi"*. Bukhari ya riwaito hadisi na 1412.

Don haka, Abokina ka tashi ka kama sana'a arziki a hannun Allah Yake kuma Zai iya baka fiye da tsammanin ka.

Mu hadu a fitowa ta 04 in sha Allahu Ta'ala.

✍🏼Dan uwanku a Musulunci:
*_Umar Shehu Zaria_*
05/12/2017.
Share:

*'YAN SAMARI MINTI BIYU 02*

*'YAN SAMARI MINTI BIYU 02*

Abokina, kar ka yaudari kanka ka kashe kuruciyarka ta hanyan zama a dakali ko wani wurin zama inda zallan labarin duniya ake yi ko cin naman mutane a irin wannan wuri.

Ibn al-Qayyim, Rahimahullah, ya ce: *"Wuraren zama inda  ake ambaton Allah, su ne wuraren da Mala'iku suke zama, amma wuraren da ake zama ana wasanni da shagala, wadannan wuraren zama ne na shaidanu. Don haka, bawa ya zaba ma kansa wanda ya fi burge shi daga cikin wadannan biyu, amma ya sani yana tare da duk wanda ya zaba a nan duniya da lahira"*. A duba littafin al-Waabilu al-Sayyib 65.

Don haka Abokina, yi kokari ka zauna da mutanen kirki kafin lokaci ya kure maka.

Mu hadu a fitowa ta 03, in sha Allahu Ta'ala.

✍🏼Dan uwanku a Musulunci:
*_Umar Shehu Zaria_*
04/12/2017.
Share:

Thursday 30 November 2017

MAFI DADIN ABINDA NA KARANTA A YAU

*MAFI DADIN ABINDA NA KARANTA A YAU*


تمنى إبراهيم الخليل أن يكون أبوه مسلماً ولم يشأ الله له رغم أنه أبو خليله ... !!!

Annabi Ibrahim yayi fatan mahaifinshi ya musulunta, amma Allah bai ga damar hakan ta kasance ba, duk da cewa baban babbanmasoyinshi (bada'dayin) ne....

وتمنى نوح العبد الشكور أن يكون ابنه مسلما  ويأبى الله رغم دعاء نوح ...!!!

Haka nan Annabi Nuhu bawa mai yawan godiya ga Allah, yayi fatan danshi ya musulunta, amma Allah ya'ki hakan ta kasance, duk da addu'ar da Annabi Nuhu yayi...

وتمنى محمد  صل الله عليه وسلم أن يسلم عمه ولم يكتب الله له هداية رغم أنه نصر الرسول في دعوته ...!!!

Haka nan Annabi Muhammad S.A.W yayi fatan Baffan shi (Abu 'dalib) ya musulunta, amma Allah bai rubuta mishi shiriya ba, duk da irin taimakon da ya bawa Annabi wajen ya' da da'awar shi....

وجعلني وجعلك مسلماً دون سؤال وأعطانا ما لم يعط إبراهيم في أبيه ونوحًا في ابنه ومحمدًا صل الله عليه وسلم في عمه ..

Amma Allah ya sanya ka ya sanya ni muka zamto musulmai ba tare da mun ro'ka ba, ya bamu abinda bai bawa Annabi Ibrahim ba dangane da mahaifinshi, bai bawa Annabi Nuhu ba dangane da 'danshi, bai bawa Annabi Muhammad S.A.W ba dangane da Baffan shi..!!!

أي فضل هذا ... !!!!! ؟
( إِنَّ اللَّهَ لَذو فَضلٍ عَلَى النّاسِ وَلكِنَّ أَكثَرَ النّاسِ لا يَشكُرونَ )
Wannan Wace irin falala ce....!!!!
"hakika Allah ma'abocin falala ne ga mutane, sai dai mafi yawan mutane basu da godiya "

نعمة اﻹسلام ترجح لو وزنتها بكل النعم ..
الحمد لله الذي هدانا لهذا وما كنا لنهتدي لولا ان هدانا الله ..


Ni'imar musulunci ta rinjayi dukkan wata ni'ima da za'a auna.....
Godiya ta tabbata ga Allah da ya shiryar damu da hakan, kuma bamu kasance masu shiryuwa ba, ba don Allah ya shiryar damu ba.

الحمد لله حتى يبلغ الحمد منتهاه
Godiya Ta tabbata ga Allah, iya matu'kar kurewar godiya.

*Fassara* :
*Malam Anas Assalafy Fagge*

Daga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*


Share:

Saturday 25 November 2017

Audio :- Muhimmancin Amana A Wajen Musulmi - Dr. Muhammad Sani Umar R/Lemo

Muhadara

Mai taken: Muhimmancin Amana A Wajen Musulmi

Tare da: Dr. Muhammad Sani Umar R/Lemo

30/2/1439
19/10/2017​



Download Audio Now

Share:

Naga Wandona A Jike Da Maniyyi Bayan Na Kammala Sallar La'asar? Dr Jamilu Yusuf Zarewa


Tambaya

 Aslamualaikum MALAM na tashi da janaba nayi salar asuba da azahar da kuma laasar, duk nayi sallah sai bayen naje wanka da yemma naga wando na da alamun manniyi shin ya ingancin sallolina na baya ? nagode

Amsa

Wa alaikum assalam, mutukar ka tabbatar a baccin asuba maniyyin ya fito, to ya wajaba ka sake asuba da azahar da la'asar din.

In har ka yi wani baccin bayan azahar to za ka danganta janabar ne zuwa ga baccin karshe da ka yi, ta yadda sallar da ka yi bayan baccin karshe ita za ka sake, kamar yadda Imamu Malik ya rawaito a Muwadda daga Sayyady Umar.
Allah ne mafi sani 

Amsawa

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
13/11/2017
Share:

Siffofin Aboki Nagari !!! Dr Jamilu Yusuf Zarewa

*Tambaya:*

Assslamu alaikum Malam ina da abokai da yawa, amma ina so ka ba ni shawara?

*Amsa:*

Wa alaikum assalam, To dan'uwa Aboki yana da mutukar mahimmanci a rayuwar mutum, idan ya zama abokinka mutum ne mai himma, sai kai ma ka samu himma kamar yadda ake cewa zama da madaukin kanwa yana kawo farin kai, haka nan idan ya zama mutumin banza sai ya yi maka tasiri, Abu Musa Al’ash’ari ya rawaito hadisi daga Annabi ((s.aw.)) yana cewa (misalin aboki na gari da abokin banza, kamar misalin mai daukar turare ne da mai hura zuga-zugi, mai daukar turare ko dai ya shafa maka ko ka sayi turare a wurinsa ko kuma ka ji kamshi mai dadi a wurinsa, mai hura zuga- zugi kuma ko ya kona maka kaya ko ka ji wari a wurinsa) Bukhari ne ya rawaito
Kuma wani malami yana cewa:
• idan ka kasance a cikin mutane, to ka yi abota da zababbensu, kada ka yi abota da halakakke saiku halaka tare.
• Idan kana so ka san waye mutum, to ka tambayi abokinsa, saboda kowanne aboki da abokinsa yake koyi .
Wani kuma yana cewa:
• Kar ka aboci malalaci a kowanne hali, da yawa mutumin kirki yana lalacewa ne idan ya hadu da mara kirki.
• Dakiki yana saurin tasiri akan mai kokari, ba ka ganin garwashe idan aka saka shi a toka shi ma sai ya zama toka.
Da fatan za ka kula da abin da ya gabata.
Allah na mafi sani

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
11/11/2017
Share:

Wanda Ya Zage Ka, Yafi Wanda Ya Yabe Ka !!!Dr Jamilu Yusuf Zarewa



salamu alaikum Malam wani yana ta zagina ba abin da na yi masa, ina neman shawara ?

*Amsa:*

Wa alaikum assalam To dan'uwa Ibnuhazm Azzahiry (456) yana cewa a cikin littafinsa Assiyar Wal-aklaak : "Wanda ya zage ka yafi wanda ya yabe ka, saboda wanda ya yabe ka ko dai ya fadi abin da kake da shi, ko kuma ya fadi abin da ba ka da shi.
idan ya fadi abin da kake da shi bai kare ka da komai ba, idan kuma ya fadi abin da baka da shi to ya cutar da kai.

Wanda ya zage ka kuwa : ko dai ya aibantaka da wani hali da kake da shi ka ga hakan sai ya sa ka gyara, ko kuma ya aibanta ka da halin da baka da shi , sai ya zama ya maka tanaji a lahira."

Daya daga cikin magabata ya hadu da wani sai ya ci mutuncinsa, sai ya ce masa dan jira kadan, ya shiga gida ya tuba ga Allah kankan da kai zuwa gare shi.
Bayan ya fito mutumin ya kasa zaginsa sai ya ce me ya faru da kai ? sai ya ce: Na tuba ga Allan da ya dora ka a kaina.
Da yawa zagin da mutane suke maka wani zunubi da ka aikata ya jawo maka.
Allah ne mafi sani

 *Amsawa* ✍🏻 

                                                                               *DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
11/11/2017
Share:

Zan Iya Rantsuwa Da Al-Qur'ani ? Dr Jamilu Yusuf Zarewa


*TAMBAYA*
Salamun alaikum Dr. Don Allah mene ne hukuncin rantsuwa da Al-Qur'ani?, kamar ka ce: Alquran.

Allah Ya kara ma Dr. Lfy Amin.

*AMSA*
Wa alaukum assalam, Ya halatta mana tun da qur'ani sifa ne daga cikin sifofin Allah .

Annabi S.A.W. Yana cewa: "Duk wanda zai yi rantsuwa, to ya rantse da Allah ko kuma ya yi shiru" kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: (6270).

Rantsuwa da Allah ya kunshi rantsewa da daya daga cikin sunayanSa ko daya daga cikin sifofinSa, kamar yadda malamai suka yi bayani.

 kasancewar daga cikin sifofin Allah akwai zance,  kuma Al-Qur'ani maganar Allah ce ba halittarsa ba, kamar yadda aya ta: (6) a suratu Attaubah ta yi bayani, hakan sai ya halatta rantsuwa da shi.

Allah mafi sani.

✍🏼Amsawa:
*_Dr Jamilu Yusuf Zarewa_*
09/11/2017.
Share:

kada Tufar Musulmi Ta Wuce Idon Sawu Dr Ibrahim Jalo Jalingo



Duk inda Musulmi yake wajibi ne ya daure ya bi Allah a cikin suturar da yake sanyawa; watau wajibi ne ya tabbatar da cewa wandonsa, ko rigarsa, ko alkebbarsa ba su kasance kasa da idanun sawunsa ba. Wannan shi ne abin da Allah Ya wajabta masa a wannan babin.

Lalle ba daidai ba ne mutum musulmi a bisa zabinsa, da ganin damarsa, saboda kawai neman ado ya je ya biya tela kudi ya dinka masa Zunubi da Bala'I; watau: wandon da ya zarce idon sawunsa, ko rigar da ta zarce idon sawunsa, ko alkebbar da ta zarce idon sawunsa. Lalle wannan Bala'I ne babba cikin wannan Al'ummah Muhammadiyyah.

Imam Malik ya ruwaito Hadithi na 1,631 cikin Muwataa, da Imam Ahmad Hadithi na 11,023 cikin Musnad, da Abu Dawud Hadithi na 4,095 cikin Sunan, da Nasaa'iy Hadithi na 9,633 cikin Sunan, da Ibnu Majah Hadithi na 3,573 cikin Sunan, da Ibnu Hibban Hadithi na 5,447 cikin Sahih, da Dabaraaniy Hadithi na 13,113 cikin Muujam, da Ibnu Abi Shaibah Hadithi na 25,318 cikin Musannaf da isnadi sahihi daga Abu Sa'id Al-Khudriy ya ce: Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce:-
((ازرة المسلم الى نصف الساق، ولا حرج فيما بينه وبين الكعبين، ما كان أسفل من الكعبين فهو في النار، من جر إزاره بطرا لم ينظر الله اليه)).
Ma'ana: ((Suturar Musulmi zuwa tsakiyar kwabri ne, amma babu laifi cikin abin da ya kasance tsakaninsa da idanun sawu, abin da kuma ya kasance kasa da idanun sawu wannan shi yana cikin Wuta, wanda kuma suturarsa ta ja kasa saboda nuna ado sam Allah ba zai dube shi ba)).

Sayyidina Abubakar Allah Ya kara masa yarda ya kasance Idan ya dan gafala mayafinsa na jan kasa, Sannan nan da nan sai ya daga shi; kamar yadda Imam Ahmad da Baihaqiy suka ruwaito.

Saboda fa'idah ga wasu ayyuka da maganganun Sahabbai game da isbaalin sutura:-
روى الامام النسائي في السنن: ٩٦٢٠ عن ابن عباس رضي الله عنه قال: ((ان الله لا ينظر الى مسبل)).
وروى الدارمي في السنن: ٢٨١٠ عن عبادة بن قرط قال: ((إنكم لتأتون أمورا هي ادق في اعينكم من الشعر كنّا نعدها على عهد رسول الله صلى الله عليه وسلم من الموبقات. فذكر لمحمد يعني ابن سيرين فقال: صدق فارى جر الإزار من ذلك)).
وروى ابن ابي شيبة في المصنف: ٢٥٣٢٤ عن أنس بن مالك قال: ((الإزار الى نصف الساق أو الى الكعبين، لا خير فيما هو أسفل من ذلك)).
وروى ابن ابي شيبة في المصنف: ٢٥٣٢٦ ان عمر دعا بشفرة فرفع ازار رجل عن كعبيه ثم قطع ما كان أسفل من ذلك)).
وروى ابن ابي شيبة في المصنف: ٢٥٣٢٧ عن ابي إسحاق قال: ((رأيت ناسا من اصحاب رسول الله صلى الله عليه وسلم ياتزرون على أنصاف سوقهم؛ فذكر اسامة بن زيد، وابن عمر، وزيد بن أرقم، والبراء بن عازب)).
وروى ابن ابي شيبة في المصنف: ٢٥٣٣١ ان عثمان بن عفان كان إزاره الى نصف ساقيه، قال: فقيل له في ذلك؟ فقال: هذه ازرة حبيبي، يعني النبي صلى الله عليه وسلم)).

Allah Ka tausaya wa wannan Al'ummah Ka cusa mata ganin kyawun abin da duk yake sunna ce ta ManzonKa. Ameen.
Share:

Hadarin Zama Da Mace Daya!!! Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa


Zama da mace daya yana kawo illoli da dama ga magidanci da su mata kansu da kuma
al`umma.
****
ILLOLI GA MAGIDANCI.

1:-Yana rage masa nishadin aure.
2:-Yana kawo tsufa da wuri.
3:-Yana saka maigida cikin damuwa
4:-Yana saka wa mace ta rika daga masa kai, tayi masa yadda taso saboda ta san ba shi da yadda zai yi.
5:-Yana rage masa samun soyayya da tarairaya da kulawa da ya cancanta a matsayinsa na maigida. 
6:-Yakan hana shi tantance so na gaskiya daga bangaren matarsa ko wanin haka.
****
ILLOLI GA SU MATAN.

1:-Yana hana wadansu samun mazajen aure.
2:-Yana dorawa matar gida aiyukan da suka shige misali kamar, kulawa da maigida,  yaran gida da ita ma kanta. 
3:-Yakan hana mace samun isasshen hutu da kuma lokacin kulawa da kanta.
4:-Yana rage wa mace kuzarin nuna soyayya ga maigidanta.
5:-Yana saka matar gida cikin tsoro da fargaba maras yankewa na ko za ai mata kishiya.
6:-Yana haifar da rashin amincewarta ga maigidanta da dauwamar da tuhuma ta har abada.
7:-Yana saka mace cikin shirin yaki da dawainiyar dakon makamai marasa ranar yankewa na nuna kin ayi mata kishiya. 
8:-Yana saka mata yawan zargi ga dukkan matan da suke da alaka da maigidanta ko ma wace iri ce koda ma yar uwa ce ko abokiyar kasuwancinsa. 
9:-Yana kara mata zafin kishi da rashin nutsuwa marasa ranar yankewa.

****
ILLOLIN GA AL`UMMA
1:-Yana haifar da karuwai mata marasa aure.
2:-Yana bunkasa yawan zawarawa acikin al`umma.
3:-Yana dorawa al`umma karin nauyin kulawa da mata iyayen marayu da marayun kansu. 
4:-Yana bunkasa zinace-zinace a cikin
al`umma.
5:-Yana rage tausayi da son bada taimako da agaji daga zukatan al`umma. 
6:-Yana kara saka fargaba da tsoro a zukatan iyaye wadanda suke da `ya`ya mata a gaba. 
7:-Yana bunkasa kasuwar malaman tsibbu da bokaye.

WADAN NAN SU NE KADAN DAGA ILLOLIN ZAMA DA MACE DAYA, 
DA FATAN MAGIDANTA ZASU GANE, 
SU KUMA MATA ZA SU TAIMAKAWA JUNANSU WAJEN TUNAWA MAI GIDA YA QARA AURE.
Share:

Archive

Unordered List

Support