DAUSAYIN IYALI 002 - Dr. Mansur Ibrahim Sokoto ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Thursday, 21 December 2017

DAUSAYIN IYALI 002 - Dr. Mansur Ibrahim Sokoto


*DAUSAYIN IYALI 002*
Matsayin Mata da Hakkokinsu a Musulunci

Littafin *Dr. Mansur Sokoto*

 Matsayin Mata Kafin Zuwan Musulunci
Abu ne da tarihi ya tabbatar cewa, Macce ba a dauke ta a matsayin
kammalallen dan Adam ba kafin zuwan Musulunci. Domin kuwa an
mayar da ita kamar Haja wacce ake saye kuma ake sayarwa, ake kuma
gadon ta kamar yadda ake gadon gida ko gona ko duk wata kaddara
da Namiji ya mutu ya bar ta. Akan umurci Macce ta yi Zina don ta kawo
kudi, kuma ana aurar da ita ne yadda aka ga dama, ba tare da neman
zabinta ko ma shawartar ta ba.
A da Namiji yakan auri ko Mata nawa yake so kuma ya ga dama kamar
yadda yake iya mallakar riga da hula ko nawa yake so.
A wasu sassan duniya ba a yarda Macce mutum ce ba ma sam. Misali,
a qasar Rasha Malaman addini sun ba da fatawar cewa, Macce najasa
ce, matsayinta daya ne da na Kare.
A yankin Larabawa, zamanin Jahiliyya, uba yakan sayar da diyarsa.
Yakan kuma rufe ta cikin qasa babu gaira babu dalili. Kawai dai
haifuwar ta ba abin farin ciki ba ne balle ai alfahari. Budurwa tana goge
gumi daga fuskar babanta a lokacin da yake haqa ramin rufe ta, amma
ita ba ta sani ba.
Kashe Macce - kafin zuwan Musulunci - ba wani babban laifi ba ne da
har za ayi maganar Qisasi ko Diyya a kan sa.
A qasar Indiya akan qone Macce ne tare da mijinta idan ya mutu,
alhalin tana da ranta da lafiyarta. Wannan ya sa sau da yawa Macce
takan kashe kanta bayan mutuwar mijinta irin mutuwar da take ganin
ta fi mata sauqi, don kauce ma wannan baqar mutuwa da mummunan
bala'i.
Malaman addinai biyu da ake a da su a lokacin wadan da suka samo
koyarwarsu daga manyan Annabawa ba su tabuka komai a kan wannan

- Yahudawa - mabiyan Addinin Annabi Musa Alaihis Salam sun dauki
Macce a matsayin najasa duk lokacin da take Haila. Ba za su ci abincin
da ta dafa ba, ba kuma za su kusance ta ba. A maimakon haka sai su
kafa ma ta rumfa a bayan gida - kamar yadda ake turke Akuya - su riqa
ba ta ruwa da gurasa har sai lokacin da ta gama al'ada sannan ta dawo
cikin gida.
- Su kuma Kiristoci duk da ba su nuna qyamar ta a wannan lokaci.
Kuma ma har saduwa suke yi da ita a lokacin da take Haila. Amma ba
za mu dauka cewa sun mutunta ta ba tun da yake suna kallon ta a
matsayin ita ce ummul-haba'isin duk wani laifi da sharri da cuta da ake
yi a duniya. Kuma wai, ita ce qofar shiga wuta. Suna kafa hujja da
cewa, wai, ita ce ta bai wa Annabi Adam (Alaihis Salam) shawarar cin
bishiyar da Allah ya hana shi har ta jawo ma su uqubar fita daga gidan
aljanna.


*Kusaurari cigaba da izinin Allah*

Gabatarwa a social Media
*Ibrahim Nasidi Baban Ilham*
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support