*_Tambaya_*
Assalamu alaykum Don Allah Dr, shin ya Halatta ace anyi duniya don manxon Allah?
*_Amsa_*
Wa alaikum assalam,
Ba'a yi mutanan duniya don Manzon Allah ba, an yi mutanan duniya ne don su bautawa Allah.
Allah madaukakin sarki yana cewa a cikin suratu Azzariyat aya ta (56) "Ban halicci mutum da Aljan ba sai dan su bauta min, bana bukatar wani arziki a wajansu kuma bana bukatar su azurta ni"
Ayar da ta gabata ta bayyana dalilin da yasa Allah ya halicci mutane da Aljanu, wato bautawa Allah da kuma tsayar da tauhidi.
Babu wani nassi ingantacce yankakke wanda ya nuna an yi duniya saboda Manzon Allah S.A.W. hakan kuma ba ya nuna an tauye manzon tsira.
Annabi S.A.W. bawa ne daga cikin bayin Allah kamar yadda tarin ayoyin Al'qur'ani suka tabbatar da hakan, sannan shugaban 'ya'yan Annabi Adam kamar yadda ya tabbata a hadisai ingantattu a kundayan musulunci.
Ajjiye shi a matsayinsa da Allah ya ajjiye shi, shi ne daidai kamar yadda yake cewa "Kada ku wuce gona-da-iri wajan yabona kamar yadda nasara suka wuce a lamarin Isa dan Maryam"
Allah ne mafi sani
*_Dr, Jamilu Zarewa_*
02/12/2017
0 comments:
Post a Comment