*'YAN SAMARI MINTI BIYU 02*
Abokina, kar ka yaudari kanka ka kashe kuruciyarka ta hanyan zama a dakali ko wani wurin zama inda zallan labarin duniya ake yi ko cin naman mutane a irin wannan wuri.
Ibn al-Qayyim, Rahimahullah, ya ce: *"Wuraren zama inda ake ambaton Allah, su ne wuraren da Mala'iku suke zama, amma wuraren da ake zama ana wasanni da shagala, wadannan wuraren zama ne na shaidanu. Don haka, bawa ya zaba ma kansa wanda ya fi burge shi daga cikin wadannan biyu, amma ya sani yana tare da duk wanda ya zaba a nan duniya da lahira"*. A duba littafin al-Waabilu al-Sayyib 65.
Don haka Abokina, yi kokari ka zauna da mutanen kirki kafin lokaci ya kure maka.
Mu hadu a fitowa ta 03, in sha Allahu Ta'ala.
✍🏼Dan uwanku a Musulunci:
*_Umar Shehu Zaria_*
04/12/2017.

0 comments:
Post a Comment