November 2016 ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Tuesday, 8 November 2016

Menene banbancin buhutani da allagwu ??

*MENENE BAMBANCIN BUHUTANI DA ALLAGWU??*

الحمد لله والصلاة على أشراف الأنبياء والمرسلين،

Amsa: Abun da ake cewa buhutani shine ka qagi e
wani mummunan abu, ka jinginawa dan,uwanka sawa'un maganace ko aiki, wanda bashi ya aikata ba kuma ba dabi'ar saba ce, kajingina masa danka batashi a idan wanda kake son batashi, ko karage masa wata daraja da yake da ita a tsakanin mutanen dasuke mutuntashi, shine Allah ya zargi masu aikatawa acikin alqur,ani, inda yace:
((ومن يكسب خطيئة او إثمًا ثم يرم به بريئا فقدا هتملوا وإثما مبيتا))،
duk Wanda yake kirkirar wani laifi ko kuskure sannan yajefi wanda yake kubutacce daka laifin, hakika yadaukarwa kansa laifin kirkirar karya da kuma zunubi mabaiyyani.

Shi kuwa lagwu shine wasa mara amfani wasa wanda bamai cema bari, yashashshe wanda bashi dawata fa'ida ko kadan aduniyarka da lahirarka, baida wani amfani akan kanka ma, kamar zance 'yan wasan kwaikwayo da musu akansu, da jayayya akan kwallo dan wasa kaza yafi na kaza, ba'abunda zancen  zai tsinanawa rayuwarka, shine ake cewa lagawu , kuma shine wanda Allah ya yabi bayinsa nagari cewa insun wuce ana yashashshen zance na lagawu basa zama ayi dasu, sai suwuce suna masu kubuta daka gareshi inda yace:

((والذين لا يشهدون الزورا وإذا مروا باللغو مروا كراما)).

Sune wadanda basa bada shaida kan karya abunda basu da masaniya akai, kuma insun wuce ana zance mara amfani sai suwuce suna masu mutunci.

والله أعلم،

***********************************

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.

_*��Tambayoyin*_ _*Musulunci��*_
            _*WhatsApp*_ _*Group*_

Share:

Aiki da hankali

AIKI DA HANKALI....

Kada ka tambayi maraya ina mahaifinka?

Kada kace wa bazawara me ya kashe aurenki?

Idan zaka taimaki talaka kada ka ce masa, ko kana da bukata?

Wadannan tambayoyi ba su dace da halin mutanen kirki ba...

Duniya makaranta ce. Mutane sune dalibanta...

Rayuwa ita ce dakin karatu, lokaci shi ne babban malami a cikin ta...

Muna haduwa a matsayin baki, sai
kuma mu watse da dai daya...

Kada kace mutane ba sa nema na sai idan suna da bukata. Fitila sai an shiga cikin duhu ake neman ta...

Duniya a tsakanin baka biyu take ( ). Baka ta farko ita ce haihuwa, ta biyu ita ce mutuwa. A tsakanin su kake rayuwa.

Idan ka wuce sai a nade aikinka a
aika maka da shi ya zama abokin jin dadinka ko shan wahalarka acikin rayuwar kabari data lahira...

Ruwan zafin da yake dafa kwai ya yi qwari shi yake dafa dankali ya yi laushi.

Ba ruwan zafin ba ne, dabi'ar
kowanensu. A'a haka mutane suke, wani yau da gobe ke sa ya yi laushi, wani kuma sai ta sa shi ya sandare...

Duk wanda ya ji tsoro zai samu damuwa a zuciyarsa. Amma ban da wanda ya ji tsoron Allah. Shi kam wanda ya ji tsoron Allah zai samu aminci da kwanciyar hankali a zuciyarsa...

Addu'a ba ta faduwa kasa. Ko a baka yau, ko a baka gobe, ko kuma a baka abin da ya fi wanda ka roka...

Idan ba a ba ka ba sam, to akwai wani sharri da za a tunkude maka...

Addu'a makamin mumini ce 'yan-uwa... Don haka muyi ruqo da Addu'a kuma mu dogara da Allah akoda yaushe...

Aikawa wasu da wannan sako domin ka/ki samu ladan tunatarwa daga Allah (SWT)Allah yasa mudace Amiin Amiin ������

Share:

Hukuncin ci ko sha da mantuwa alhali mutum yana azumin nafila

*HUKUNCIN CI KO SHA DA MANTUWA ALHALI MUTUM YANA AZUMIN NAFILA*

Mai azumin nafila ko da gangan yaci abinci ko ya sha abin sha ko yayi jima'i da matarsa to bai da laifi kuma ba zai rama azumin ba. Saboda Annabi (s.a.w.) yana cewa: "Mai azumin nafila sarkin kansa ne, in ya ga dama ya ci gaba da azumi, in ya ga dama kuma ya karya" Albani ya ingantarda shi a sahihul-jami'i hadisi mai lamba ta: 3854.

Haka kuma idan yaci ko ya sha ko yayi jima'i da matarsa da mantuwa alhali yana azumin nafila to yana da zabi guda biyu:

1. In yaga dama yaci gaba da azuminsa saboda duk wanda yaci abinci ko yasha abinsha cikin mantuwa, ko cikin kuskure, ko kuma aka tilasta masa, to babu kaffara ko ramuko akansa. Saboda Sahihin hadisin da Abu Huraira (r.a) ya ruwaito daga Manzon Allah (s.a.w) yana cewa:
"DUK WANDA YA MANTA CEWA YANA AZUMI, HAR YACI ABINCI KO YASHA WANI ABU, TO
YACI GABA DA AZUMINSA. HAKIKA ALLAH NE YA CIYAR DASHI KUMA YA SHAYAR DASHI"
(Jama'ar Maruwaitan hadisi ne suka ruwaito
shi).

Haka kuma Ibnu Maajah da Hakim daga Abdullahi bn Abbas (r.a) daga Manzon Allah (s.a.w) yana cewa:
"ALLAH YA DAUKE MA AL'UMMATA LAIFIN DA SUKAYI CIKIN KUSKURE, DA MANTUWA, DA KUMA ABINDA AKA TILASTA SU AKANSA".

Anan koda kuwa na farillah to zai ci gaba da azuminsa kawai Allah ne ya ciyar ko ya shayar dashi.

2. Ko kuma idan yaga dama sai yaci gaba da cin abincinsa wato ya karya azumin gaba daya saboda shine sarkin kansa kamar yadda hadisi yazo a sama. Anan ana nufin mai azumin nafila kenan, banda mai azumin farillah.

Wallahu a'alam

Share:

Falala da hukuncin kwanciya da tsarki (alwala)

*FALALA DA HUKUNCIN KWANCIYA DA TSARKI (ALWALA).*

A- *FALALAR KWANCIYA DA TSARKI*

@-Wanda ya kwana cikin tsarki,yana kwanane tare da Mala'ika a shinfidarsa, kuma mala'ika yana yimasa addua.

Manzon Allah s.a.w yana cewa:
"Ku tsarkake wannan jiki, sai Allah ya tsarkakeku, domin babu wani bawa da zai kwana cikin tsarki (alwala) face ya kwana tare da Mala'ika acikin mayafinsa,babu wani motsi da bawan zaiyi acikin wani lokaci na dare face yace:
Allah ka gafartawa wannan bawan naka,domin ya kwana cikin tsarki".
#Alban yace Hadisine mai kyau: Saheehut Targheeb

@-Allah yana amsa adduar wanda ya kwanta da tsarki (alwala).
Annabi s.a.w yana cewa:
"Babu wani musulmi da zai kwanta cikin tsarki(alwala) sannan ya tashi cikin dare ya roki Allah alkhairin duniya da na Lahira  cikin dare,face sai Allah ya biya masa buqatarsa".
#Abu Dauda, kuma albany ya ingantasa.
#Ahmad.

@Wanda ya kwanta da tsarki(alwala) kamar mai azumine mai tsayuwar dare.
Amru BN As R.A yana cewa
"Wanda ya kwanta yana mai tsarki kamar mai azumine kuma mai raya dare da ibada".
#Tirmizy da Hakim

B- *HUKUNCIN KWANCIYA DA TSARKI(alwala).*

Malamai suna cewa kwanciya da tsarki ba wajibi bane, Sunnace ta Annabi s.a.w mai hukuncin mustahabbi.
Annabi s.a.w ya kasance idan zai kwanta barci yana yin alwala sannan ya umarci wani daga cikin sahabbansa akan haka.
#Bukhari.

Abinda ake nufin tsarki lokacin kwanciya barci shine alwala saukakkiya wato wadda ba'a wanki uku ba,kuma alwala ba karyewa saboda wani hadasi kamar fitar da iska ko wasa da iyali,saboda alwalace ta barci bata sallaba.
#Duba Umdatul qary.

NB:
Kuma mutum zai yi wannan alwala ko yana da janaba.
Domin an tambayi nana Aisha R.A ya Annabi s.a.w kwanci idan yana da janaba sai tace yakanyi dayan abubuwa ukku:
-ko yayi wankan janaba sai yakwanta ko
-Yayi alwala ko kuma
-yayi Taimama.
#Saheehul Jami'I.

Allah ne mafi sani.

Allah ka bamu ikon kiyaye, amin

Share:

Shin ana ramawa wanda ya mutu azumi na ramadan ??

*SHIN ANA RAMAWA WANDA YA MUTU AZUMI NA RAMADAN??*

الحمد الله وكفى وصلى الله على محمد وآله وصحبه وسلم،

Amsa:An yiwa shaeik uthaimeen {Rahimahullah} irin wannan tambaya sai ya amsa dacewa,
Mara lafiya matukar yana cikin rashin lafiya a zumi bai wajaba akan saba, idan ya mutu kafin ya warke, ya mutu kafin yazama wajibi akansa, baza'a ciyar a madadin saba domin ciyarwa a matsayin azumi take, idan azumi bai zama wajibi ba, to mamadin sama bai zama wajibiba,Allah madaukakin sarki yace:
(ومن كان مريضا أو على سفر فعدة من أيام أخر، يريد الله بكم اليسر ولايريد بكم العسر ولتكملو العدة ولتكبر الله على ما هداكم ولعلكم تشكرون،)
Duk wanda yakasance mara lafiya acikinku ko yana halin tafiya, to ya rama awasu kwanakin daban bana ramazan ba, Allah yana nufin saukine a gareku, ba yana nufin quntatawa agareku bane, danku cika kwanakin dan kuma ku godewa Allah abisa abun da ya shiryar daku, ko zaku zamto masu yawan godewa,

Tabbatar  dalili da wananana aya shine idan bai samu dama ba babu komai akansa, saboda Allah ya sanya wajabcin ramuwar azumi a kwanaki nagaba, shikuwa bai kaiba sai yarasu, idan ya mutu kafin yakai zuwa garesu hakika ya mutu kafin lokacin wajabci yazo, sai yakasance kamar wanda ya mutu kafin shi gowar watan ramazan, bai wajaba aciyar masaba sobada watan ramazana da zaizo agaba, koda ya mutu ramazan yana gobe kamawa.

Amma a hadisi manzan Allah salallahu Alaihi wasallam yace, (Duk wanda ya mutu da azumi akansa to waliyyinsa sai yayi masa, bukhari da muslim,
Abunda hadisin ke magan akai shine wanda ya mutu yana da ramuwar azumi akansa, to waliyyinsa sai ya rama masa, ba wanda ya mutu acikin watan azumin ba, idan bazai masa azumi ba to ya ciyar kowacce rana miskini daya, iya adadin azumin dake kansa bai rama ba,

Abun nufi wanda ya mutu babu azumi a kansa baza ai masa azumi ba, mun sani cewa idan mara lafiya cuta taci gaba ajikin sa, azumi bai wajaba akansa ba, ko ramuwa a halin rashin lafiyarsa,

Amma wanda ya mutu ana cikin azumi, to waliyyinsa bazai karasa masa zumiba kuma bazai ciyar ba, domin mara lafiya idan ya mutu aiyukansa sun yanke, kamar yanda Annabi sallahu alaihi wasallam, yafada ( Idan mutum ya mutum ayyukansa sun yanke sai abubuwa uku sadaka mai gudana, ko ilmin daya bari ake amfana dashi, ko da nagari dazai dungai masa addu'a, abisa wannan baza,a rama masaba hatta na ranar daya mutu

والله أعلم،

***********************************

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.

_*��Tambayoyin*_ _*Musulunci��*_
            _*WhatsApp*_ _*Group*_

Share:

Shin meke sa mace tanayin al'adarta wata-wata amma wani lokaci sai bayan wata biyu ko uku kuma ba matar aure ba ??

*SHIN MEKE SA MACE TANAYIN AL'ADARTA WATA-WATA AMMA WANI LOKACI SAI BAYAN WATA BIYU KO UKU KUMA BA MATAR AURE BA*

الحمد لله الذي أنزل على عبده الكتابة ولم يجعله عواجا، والصلاة والسلام على أشراف الأنبياء والمرسلين، سيدنا محمد وعلى آله وصحبه ومن ولاه،

Allah madaukain sarki mai ikone akan komai, kuma yakanyi halitta yanda yaso kuma yakan saukarwa da bawansa jarrabawa akowane lokaci dayaso, wani lokacin dan yajarraba bawansa, wani lokacin danya kankarewa bawansa wani laifi da ya aikata asanadin wannan cutar, yakanyi hakanne tahanyoyi daban daban,

Alal hakika abunda yakesa mace canjawar lokacin ala'ada akwai ababe dasuke faruwa wanda suke sabbaba hakan musamman ga wacce ba matar aure ba, sune abubuwa guda biyu cikin su ake samun daya,

▪Shine akwai matan da haka Allah yayisu sukan yi wata uku ko biyu batare da sunyi al,ada ba kuma basu da aure, haka halittar su da Allah ya yisu da ita take, wannan kuma ba'abun damuwaneba.

▪Abu nabiyu dake kawo wannan shine rashin lafiya, ke sa mace tana al'ada wata sai ta koma wata uku wasu ma har shida, lallai yakamata ki tsananta bincike kiga likitoci, ko kuma masana akan abun da yashafi shafar shaidanu, ko masu aurar mace surike mata jini, lallai bazaki gane awane aji kikeba sai anyi bincike in rashin afiyace sai anemi magani dan samun lafiya Allah madaukakin sarki ya taimakemu.

والله أعلم،

***********************************

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.

_*��Tambayoyin*_ _*Musulunci��*_
            _*WhatsApp*_ _*Group*_

Share:

Monday, 7 November 2016

Yaya hukuncin sallar wanda yasha rake bai kuskure bakin saba ??

*YAYA HUKUNCIN SALLAR WANDA YASHA RAKE BAI KUSKURE BAKIN SABA*

الحمد لله الذي شرفنا بالإسلام وجعلنا خير أمة أخرجت للناس، صلى الله على محمد وآله وصحبه وسلم،

Amsa: cin wani abu ko sha, ko taba wani abu, ko sun batar mace, ko tabata dan sha'awa, baya karya alwala, balle yai tasiri a sallar mutum dan haka babu komai ga wanda yaci ko yasha yai sallah batare da ya kuskure bakin saba, saifa idan abunda yaci naman rakumine to wannan dole sai ka kuskure bakinka da nassin  hadisin Manzan Allah salallahu Alaihi wasallam wannan ya tabbata.

Amma kuma kuskure baki  bayan kaci ko kasha sunnah ne kuma abun sone, saboda dalilai da suka tabbatar da hakan,.

Daka Abdullahi dan Abbas Allah yakara musu yarda, Manzan Allah sallahu Alaihi wasallam ( ya sha nono sai yabukaci akawo masa ruwa ya kuskure bakinsa bayan yayi alwala, sai yace yana da naso, ma'ana ragowar dandanon nazama abaki,

Imamul nawawi yace: acikin wannan hadisin akwai mustahabbanci kuskure baki bayan anci ko an sha, bayan alwala, saboda abunda yaci ko yasha rogowarsa zai iya rage masa abaki,

Da kuma hadisin nu'uman wanda manzan Allah a yakin khaibar bayan sunje wani gari "suhaba'i" can wani garine dake gangaren khaibar, yai umarni akawo musu wani abunci ba,a samu ba sai assaweeq sai sukaci bayan la,asar sai sukazo yin sallar magriba, sai Annabi ya kuskure bakinsa sai sahabbai ma suka kuskure bakinsu,

acikin wannan hadisi akwai mustahabbanci kuskure baki idan akaci ko aka asha bayan alwala, duk cewa abuncin saweeq bashi da naso, amma dan ragowarsa dake tsakanin hakora da sauran guraren nabaki su zauna abakinsa.

والله أعلم،

***********************************

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.

_*��Tambayoyin*_ _*Musulunci��*_
            _*WhatsApp*_ _*Group*_

Share:

Menene hukuncin namiji mai biye biyen mata bayan yana da aure iyalinsa tana iya kokarinta wajan bashi hakkinsa ??

*MENENE HUKUNCIN NAMIJI MAI BIYE BIYEN MATA BAYAN YANA DA AURE IYALINSA TANA IYA KOKARINTA WAJAN BASHI HAKKINSA.?*

الحمد لله والصلاة والسلام على محمد وآله وصحبه وسلم،

Amsa: Lallai wannan mijin bai kyauta ba kuma abun da yake aikatawa hadarine mai girma agareshi anan duniya da kuma lahira, kuma abun bakin cikine yakamata yagane bashi kadai keda hakki akanki ba, kema kina da hakki akansa ya nuna kulawa da kishi dakuma barin abunda duk zaibata miki rai, kozai saki damuwa matukar wannan abun basabon Allah bane.

Shine wanda shari'ar musulunci take kira da dayyus, wato sakarai shasaha wanda baya kishin matarsa ko kannensa mata ya kyalesu sakaka suna abunda sukaga dama, ko kuma baya kishin matarsa kwata kwata, kawai yadauki matarsa amatsayin mai dafa masa abunci ba ruwansa, zaije yaita mu'amala da wasu matayen, wannan sharrine mai girma, domin irin wadannan matayen ne in ba,a samu mai tsoran Allah ba, itama sai tafada wasu dabi'u da ababe marasa kyau, akwai wadanda tsabar lalacewa sune suke baiwa matayan nasu dama cewa suma suna iya yin mu'amala da kowa, hakika matarka tanada daraja da mutunci domin itace suturarka kamar yanda kur'ani yanuna, ba daidai bane kabarta gida kaje kana biyewa wasu akwararo, kuma ya kamata kasani wadannan  wadanda kake biyewa bawani abu sukafi taka matarba, kai takama tafisu kawai saboda su sun tube rigar mutunci suna fito na fito da Allah ne har kake ganin wani abu atare dasu, domin sudin kamar shaddar kasuwa suke kowa zai hausu yaikashi, lallai wanna miji naki yakamata yaji tsoran Allah yatuba yadena, kuma kici gaba da rokon Allah Allah ya shiryar miki dashi, sannan kibi duk wasu hanyoyi na hikima da fasaha kinunar masa abunda yake yana matukar kona miki rai, kuma kitunatar dashi lallai wannan mugun aikine yake, inda hali kihada da abokansa iyayensa da duk wanda kikasan yanajin nauyinsa danya dena wannan dabi,a yadawo gareki, inkinbi duk wadannan hanyoyin bai daina ba, kinemi taimakon Allah kawai araba aurenku Allah ya musanya miki da mai kishinki mai kiyaye addinin Allah madaukakin sarki,

Hadisi yazo daka manzan Allah sallahu Alaihi wasallam, daka abdullahi dan umar Allah  yakara masa yarda yace manzan Allah yace, ( mutane uku Allah yaharamta musu aljannah, wanda ya dawwama yana shan giya har yamutu, dakuma maiyawan sabawa iyayensa, dakuma dayyus sakaran dayake tabbatar da barna acikin iyalinsa baya kishinsu, ) Imamu Ahmad.

Malam haisami yace: acikin mu'ujamul zawa'id acikin hadisin akwai rawin da ba,a ambataba, amma sauran mutanen dasuka ruwaito shi dukansu amintattu ne, Dabarani ya ruwaito daka Ammar bin yasir manzan Allah salallahu Alaihi wasallam yace:

(Mutane uku, bazasu shiga aljannaba har abada, Mace mai kamanceceniya da maza, dakuma wanda yake shan giya har yamutu, da dayyus sokwan da baya damuwa da wanda yake shiga wajan ahlinsa, baya kishinsu.

A bisa wannan duk wanda yai duba da hadisn farko duk da hadisi nabiyu akwai  rauni acikin ruwayarsa, zai fahimci dayyus shine wanda yake kyale barna acikin iyalinsa tana wakana kuma baidamu ba, ko yake bada kofar da kowacce irin barna zata iya faruwa akan iyalinsa, domin duk wanda bai damu da matarsa ba baya kishinta yana bin wasu awaje, hakika yakyale babbar kofa ta faruwar fitina acikin iyalinsa. Sa'annan kuma wadda keda miji irin wannan kuma ta tabbatarda yana wannan biye-biyen matan, ba zargi bane to sai ta fara masa nasiha cikin hikima da kuma rokon Allah ya shiryar mata da mijinta da ci gaba da gyara jikinta sosai ta hanyoyin da suka halatta ( maganar gaskiya da yawan matanmu na arewacin qasarnan suna wasa da gyaran jikinsu ) da yawan mazaje shi yasa shaidan ke samun galaba akansu sai na wajen suke basu sha'awa kuma alhali ba komai suka fi na auren ba kawai su na auren basa gyara jikinsu ne, to idan tabi duk wadannan matakan tayi-tayi yaqi dainawa to sai ta janyo magabata a cikin lamarin, idan yaqi bari to zata iya neman rabuwa dashi Allah ya musanya mata da wani nagari saboda yana iya dauko musu wani ciwo can wajen fasikancin nasa. Allah ya kiyaye!

والله أعلم،

***********************************

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.

_*��Tambayoyin*_ _*Musulunci��*_
            _*WhatsApp*_ _*Group*_

Share:

Ya halatta mutum ya auri matar da kanen babansa ya taba aura??

Assalamu alaikum
Malam Tambaya na shine ya halatta mutum ya auri matar da kanen babansa ya taba aura?
Kuma miye hukuncin sa.

_*AMSA:*_
*******

وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ،

Matar da kanen babanka ya taba Aure, bã ta cikin jerin mata 7 da Allah ya haramta aurensu ga namiji mai alãqa dasu.
Acikin suratun Nisaa'i, ayah ta 23, Allah yana cewa;

ﺣُﺮِّﻣَﺖْ ﻋَﻠَﻴْﻜُﻢْ ﺃُﻣَّﻬَﺎﺗُﻜُﻢْ ﻭَﺑَﻨَﺎﺗُﻜُﻢْ ﻭَﺃَﺧَﻮَﺍﺗُﻜُﻢْ ﻭَﻋَﻤَّﺎﺗُﻜُﻢْ ﻭَﺧَﺎﻻَﺗُﻜُﻢْ ﻭَﺑَﻨَﺎﺕُ ﺍﻷَﺥِ ﻭَﺑَﻨَﺎﺕُ ﺍﻷُﺧْﺖِ ﻭَﺃُﻣَّﻬَﺎﺗُﻜُﻢُ ﺍﻟﻼَّﺗِﻲ ﺃَﺭْﺿَﻌْﻨَﻜُﻢْ ﻭَﺃَﺧَﻮَﺍﺗُﻜُﻢ ﻣِّﻦَ ﺍﻟﺮَّﺿَﺎﻋَﺔِ ﻭَﺃُﻣَّﻬَﺎﺕُ ﻧِﺴَﺂﺋِﻜُﻢْ ﻭَﺭَﺑَﺎﺋِﺒُﻜُﻢُ ﺍﻟﻼَّﺗِﻲ ﻓِﻲ ﺣُﺠُﻮﺭِﻛُﻢ ﻣِّﻦ ﻧِّﺴَﺂﺋِﻜُﻢُ ﺍﻟﻼَّﺗِﻲ ﺩَﺧَﻠْﺘُﻢ ﺑِﻬِﻦَّ ﻓَﺈِﻥ ﻟَّﻢْ ﺗَﻜُﻮﻧُﻮﺍْ ﺩَﺧَﻠْﺘُﻢ ﺑِﻬِﻦَّ ﻓَﻼَ ﺟُﻨَﺎﺡَ ﻋَﻠَﻴْﻜُﻢْ ﻭَﺣَﻼَﺋِﻞُ ﺃَﺑْﻨَﺎﺋِﻜُﻢُ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻣِﻦْ ﺃَﺻْﻼَﺑِﻜُﻢْ ﻭَﺃَﻥ ﺗَﺠْﻤَﻌُﻮﺍْ ﺑَﻴْﻦَ ﺍﻷُﺧْﺘَﻴْﻦِ ﺇَﻻَّ ﻣَﺎ ﻗَﺪْ ﺳَﻠَﻒَ ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠّﻪَ ﻛَﺎﻥَ ﻏَﻔُﻮﺭﺍً ﺭَّﺣِﻴﻤﺎ.

*Fassarar Hausa.*
_An haramta muku uwãyenku da ´yã´yanku da ´yan uwanku mãtã da goggonninku da innoninku da ´yã´yan ɗan uwa da ´yã´yan ´yar uwa da uwãyenku waɗanan da suka shãyar da ku mãma da ´yan uwanku mãtã na shan mãma da uwãyen mãtanku da agõlolinku waɗanda suke cikin ɗãkunanku daga mãtanku waɗanda kuka yi duhũli (Jimã'i) da su, kuma idan ba ku yi duhũli da sũ ba, to, bãbu laifi a kanku, da mãtan ´yã´yanku waɗanda suke daga tsatsonku, kuma kada ku haɗa tsakanin ´yan´uwa biyu mãtã, fãce abin da ya shige. Lalle ne, Allah Yã kasance Mai gãfara ne Mai jinqai._

Anan, haramcin Aure ya shafi har da kishiyoyin mamarka da matar da ta shayar dakai mama, da wacce aka shayar daku tare, da kuma duk wata yarinyar da wannan matar ta shayar mama.

_*HUKUNCI*_
Amma ita waccan matar da kanen babanka ya saka, ya halatta agareka ka aureta idan kana so, babu haramci a hakan.

والله أعلم،

***********************************

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.

_*��Tambayoyin*_ _*Musulunci��*_
            _*WhatsApp*_ _*Group*_
_*+2347068043652*_
_*+2348164884055*_

Share:

Menene banbanci tsakanin girman kai da kuma jiji dakai meye matsayin maiyinsu a musulunci

*MENENE BANBANCI TSAKANIN GIRMAN KAI DA KUMA JIJI DAKAI MEYE MATSAYIN MAIYINSU A MUSULUNCI.*

الحمد الله الذي هدان للإسلام وما كنا لنهتدي لولا أن هدان الله، والصلاة والسلام على محمد وآله وصحبه وسلم.

Girman kai da kuma jiji dakai, dukansu dabi'une munana wanda musuluci ya yakesu, kuma dabi'u ne ababen zargi masu kai mutum ga halaka, cikin kankanin lokaci, banbaci dake tsakanin su kadanne shine:
Shi girman kai shine kadunga ganin fifiko akan wani, kadunga jin kafi wane kai abu kaza kafi karfin ko kawuce matsayin wane kafi karfin saurarensa dadai makamantan haka.

Shima jiji dakai shine kadunga  jin kana da wani abu da waninka bashi dashi.

Dukansu munane wadanda suke dauke bawa daka godewa Allah, zuwa godewa kai dajin wayanka ko iyawarka sukema abu, suna hanaka yaban Allah dagode masa ka koma yaban kanka, dakuma qin kankantar da kanka ga mahalicci, da ruduwa dakai dakin  girmama mutane da sanin matsayinsu izuwa hantarar su, da danne hakko qinsu.

yana daka illolin jiji dakai suke haifarwa akwai rusa ayyuka kyawawa da kuma boye masu kyau, dakuma janyo zarge zarge.

Hukuncin jiji dakai haramunne domin nau'ine na shirka,shaikul islam ibnu taimiyya yace : ( Sauda yawa riya tana kusanci da jiji dakai, ita riya tana babin shirka da halittu, shikuma jiji dakai yana babin shirka dakai, wannan shine halin mai girman kai, Mai riya bai tabbatar dafadin Allah madaukakin sarki ba
إياك نعبد،
Mai jiji dakai kuma bai tattabatar, da fadin Allah madaukin sarki,
وإياك نستعين،
duk wanda yatabbatar da fadin Allah إياك نعبد zaifita daka riya
wanda yatabbatar da fadin Allah
وإياك نستعين،
zai futa daka jiji dakai.

Jiji dakai abun zargine acikin alqur,ani da sunnah Allah madaukakin sarki yace: ( ويوم حنين إذ أعجبتم كثرتكم فلم تغن عنكم شيئا )
Daranar yakin hunaini lokacin dayawanku ya burgeku kuma bai tsinana muki komai ba yawan naku.

Abdullahi dan masu' ud yace halaka tana cikin ababe biyu, debe tsammani daka Allah dakuma jiji dakai.

jiji dakai yakan kai maiyinsa zuwa ga kafirci da futa daka musulunci kamar yanda shaidan yai alfahari da asalinsa da ibadar sa, yaiwa Allah girman kai.

Ibnu qudama yace: kasani jiji dakai yakan kawo girman kai domin yana cikin dalilan dake kawo girman kai, acikin girman kai kuma akwai masifu dayawa akwai tsakanin haittu da kuma tsakaninka da mahaliccinka

Ababen dazaka gane maijiji dakai sune

•Kin gaskiya mayar da ita da hantarar mutane
•Raina kowa
•Rashin shawartar masu hankali da manya acikin al'amura
•Rangwada atafiya ji da isa
•Ganin girman biyayyar da kakewa Allah dakuma ganin yawanta
•Alfahari da ilimi da gori dashi
•Alfahari da dukiya da dangi da kyawun halitta
•Raina kokarin maluma masu tsoran Allah
•Dawwama akan kuskure
•Karancin sauraron ilmi ko mika wuya ga masu shi dalazimtarsu
•Hantarar masu sabo
•Manta zunubai da rainasu ganin karancin su
•Sabawa mutane dagangan danjin isa

Abubuwan da suke janyo jiji dakai

√Jahilci
√karancin tsantseni da tsoran Allah
√Raunin jin cewa Allah yana tare dakai yana kallanka
√Karancin wadanda zasuyiwa mutum nasiha
√Mummunar niyya
√Yawan jindadin yabon mutane koyin abun dan samun yabonsu dakuma taimakon shaidan Akan haka
√Fitunwa dasan duniya dabin san zuciya
√Karancin tunani
√Karancin godewa Allah
√Karancin Ambaton Allah
√ Rashin tadabburin Alqur'ani da kuma hadisai
√Amintuwa da azabar Allah da dogara da Afuwarsa da gafarar sa kadai.

Maganin sa shine tuna ni'imomin Allah dakuma tuna yanda mutum yake abaya kafin yakai matsayin dayake na yanzu, dakuma tuna tarihin Al'ummatan da suka shude da karanta rayuwar manzan Allah salallahu Alaihi wasallam da sahanbansa.

والله أعلم،

***********************************

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.

_*��Tambayoyin*_ _*Musulunci��*_
            _*WhatsApp*_ _*Group*_

Share:

Me yakamata wanda yake tunanin ace yazama kirista??

*ME YAKAMATA WANDA YAKE TUNANIN ACE YAZAMA KIRISTA*

الحمد لله والصلاة والسلام على من لا نبي بعده.
Alal hakika raunin imani shine ke kawo wannna tunani dakuma shedan, abunda yakamata ka dunga yi shine neman tsarin Allah daka shaidan kamar yanda Allah madaukakin sarki yace:

(وإما ينزغنك من الشيطان نزغ فاستعذ بالله إن هو السميع العليم)
Duk lokacin da shaidan yakawo maka wata fizga hari na mummunan aiki ko tunani kanemi tsari da Allah

Yazo acikin hadisi ingantacce manzan Allah salallahu Alaihi wasallam yace: shaidan zai zowa da yanku yadunga rayamar azuciya cewa wanene yahalicci kassai yace Allah wanenene ya halicci sammai yace Allah wanene yahalicci kaza yace Allah karshe sai ya dunga kawo cewa shi Allah kuma waya halicce shi, Annabi yace da kaji haka kacanjawa zuciyarka wani abun daban kanemi tsari daka Allah.

Hakika ni'imar musulunci ni'imace mai girman gaske, dan haka bazai taba yiyuwa shaidan ya kyaleka haka kawai kazauna lafiya ba, sai ya dunga kawo maka hari dare darana

Amma kakiyaye karka sake ka furta hakan inka furta malamai sukace kazama kafirin.

Sannan ka yawaita tuba zuwa ga Allah idan kasan kana tare da mutanen banza ka gaggauta canzasu da mutane nagari, idan kuma gurine kake tasirantuwa dashi ka kaurace masa, ka yawaita karatun alqur'ani da sauraron sa dajin  wa'azuzzuka da halartar guraren da duk ake karantar da musulunci.

Sannan ka yawaita addu'ar manzan Allah salallahu Alaihi wasallam.

اللهم يا مقلب القلوب ثبت قلوبي على دينك،

Ya Allah mai jujjuya zukata ka tabbatar da zuciyata akan addininka

In sha'allahu zaka kubuta daka abunda kake ji na sha'war wani addini koma bayan musulunci.

والله أعلم،

***********************************

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.

_*Tambayoyin*_ _*Musulunci*_
            _*WhatsApp*_ _*Group*_

Share:

Nasha nonon matata, yaya auren mu??

*NA SHA NONON MATATA, YA YA AURENMU?*

*_Tambaya?_*

Don Allah Malam ya matsayin mutumin da ya sha nonon matarsa,  ya aurensu  yake?

*_Amsa:_*
Wa'alaykumussalam,

To dan uwa, Allah Madaukakin Sarki ya halatta maka jin dadi da dukkan bangarorin jikin matarka, in ban da dubura ko kuma saduwa da ita lokacin da take haila,  don haka  ya halatta ka tsotsi nononta mutukar babu ruwa a ciki, amma idan akwai ruwa a ciki, to Malamai sun yi sabani akan halaccin hakan zuwa  maganganu guda biyu :

1. Ya halatta, saboda kasancewar nonon da yake haramta aure shi ne wanda aka sha kafin yaro ya cika shakaru biyu,  saboda fadin Annabi s.a.w. "Shayarwar da take haramtawa, ita ce wacce yaro ya sha saboda yunwa" , Bukhari lamba ta : 5102.

Ma'ana lokacin da ba zai iya wadatuwa ba daga nono, saboda shi ne abincinsa, shi kuma wannan ya faru ne bayan mutum ya girma don haka ba zai yi tasiri ba wurin haramta aure,  wannan ita ce maganar mafi yawan Malamai.

2. Bai halatta ya sha ba, saboda ko da yaushe mutum ya sha nonon mace to ta haramta a gare shi, domin Annabi s.a.w. ya  umarci matar Abu-huzaifa da ta shayar da Salim,  don ta haramta a gare shi, kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 2636, tare da cewa a lokacin Salim ya riga ya girma,  wannan sai yake nuna cewa idan babba ya sha nono to zai yi tasiri wajan haramcin aure .

Zancen da ya fi karfi shi ne ya halatta miji ya sha nonon matarsa, sai dai rashin shan shi ne ya fi, saboda fita daga sabanin malamai yana da kyau, don neman Karin bayani duba : Bidayatul-mujtahid 2\67

Allah ne mafi sani.

31/10/2014

*_Dr Jamilu Yusuf Zarewa_*

Daga: *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*

Share:

Archive

Unordered List

Support