Dausayin iyali 003 - Dr.mansur ibrahim sokoto ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Thursday, 11 January 2018

Dausayin iyali 003 - Dr.mansur ibrahim sokoto


*DAUSAYIN IYALI 003*
Matsayin Mata da Hakkokinsu a Musulunci
Littafin *Dr. Mansur Sokoto*
*Macce 'Yar Gatan Musulunci*
Addinin Musulunci shi ne ya qwato ma Macce dukkan haqqoqinta, ya
hana a zalunce ta, ya tabbatar mata da mutuntaka da daraja, ya sanya
mata rabo a cikin gado, ya ce duk aikin lada idan ta yi shi tana da lada
kamar Namiji.
Har a mintunansa na qarshe a duniya, Manzon Allah Sallallahu Alaihi
wa Sallam ya kasance yana wasici ga al'ummarsa da su kula da
haqqen Mata. Yana cewa:

""استوصو"ا بالنساء خيرا"
“Ina umurnin ku da ku kyautata kula da mata”. Sahih Al-Bukhari
(5185).
A musulunci, da zaran ka haifi 'ya Macce to ka samu wani babban
dalilin shiga aljanna. To ballai kuma wanda ya samu biyu.
Hadisi ya zo a cikin Sahih Al-Bukhari daga uwar Mummunai A’isha
Radhiyallahu Anha tana ba da labarin wata baquwa da ta zo bara a
gidanta tana neman abin da za ta jefa a bakin salati. Tare da ita akwai
yara tagwaye guda biyu. Sai ta dauko dabino qwara daya ta ba ta. Sai
matar ta raba dabinon biyu ta ba ‘yan tagwayenta. Wannan abin ya ba
ni sha’awa, har na fada ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam. In
ji ta. Sai ya ce,”Ai duk wanda Allah ya jarabce shi da ‘ya’ya mata ko
kadan ne kuma ya kyautata ma su, za su zamo ma sa kariya daga
shiga wuta”. Sahih Al-Bukhari (1418) da Sahih Muslim (2629).
A daya Hadisin na cikin Sahihu Muslim daga Anas Radhiyallahu Anhu
Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallam cewa ya yi: “Wanda ya kula da
‘ya’ya mata biyu har suka balaga zai zo a ranar Alqiyama muna tare
da shi kamar haka”. Sai ya gwama yatsunsa wuri daya.
Wannan a matakin farko na haifuwar Macce da rainon ta kenan. Idan ta
girma aka yi ma ta aure Musulunci ya ce, ita ce ta kammala rabin addinin mijinta. Idan kuwa ta haifu sai aka ce aljannar ‘ya’yanta na
qarqashin qafafunta. A nan ba ina nuni ne da Hadisin da aka sani sosai
ba, shi ne: “Aljanna tana qarqashin qafafun iyaye Mata”.
Wannan Hadisi da'ifi ne, kuma ma babu shi a littafan Hadisi sai dai na
Tarihi irin su "Al-Kamil" na Ibnu Adiy, da na Uqaili. Amma akwai Hadisin
Mu'awiya bn Jaahimata wanda Imam An-Nasa'i da Hakim suka ruwaito
cewa, wani mutum ya zo wurin Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa
Sallam yana neman izininsa don ya tafi Jihadi. Sai Annabi Sallallahu
Alaihi wa Sallam ya tambaye shi, ko mahaifiyarka tana raye? Ya amsa
ma sa, eh. Sai ya ce:
"To, ka lizimce ta. Domin Aljanna na qarqashin qafafunta".
Wannan kam ingantaccen Hadisi ne babu tantama. Imam Nasa’i (2/54)
da Hakim (4/151) da dabarani (1/225) duk sun fitar da shi. Kuma
Hakim da Dhahabi da Mundhiri (3/214) duk sun inganta shi. A
ma’anarsa kuma ba shi da banbanci da wancan.
Hadisin da ya fi wannan inganci shi ne wanda ya ce, uwa Macce tana
da haqqoqi uku, a lokacin da uba Namiji yake da haqqi guda daya. Ga
yadda Hadisinyake: Wani mutum ya zo wurin Manzon Allah Sallallahu
Alaihi wa Sallam sai ya tambaye shi, wa ya fi dacewa a duniya in
kyautata ma? Sallallahu Alaihi wa Sallam ya ce,”Mahaifiyarka”. Ya ce,
sai kuma wa ye? Ya ce,”Mahaifiyarka”. Ya sake tambaya, sannan wa?
Ya ce, ”Mahaifiyarka”. Sai kuma wa? Sallallahu Alaihi wa Sallam ya ce,
“Sannan Mahaifinka”. Sahih Al-Bukhari (5626).
Kai, wace daraja muke nema ma Macce bayan abinda kowa ya sani a
tarihi ne, Macce guda daya ce ta yi sa’ayi tsakanin Safa da Marwa tana
nemar ma danta ruwan sha, amma Shari’ar Musulunci ta mayar da
wannan sa’ayin nata a matsayin wani rukuni daga cikin rukunan
Musulunci shi ne aikin Hajji? Tare da haka aka yafe wa Mata yin
Sa’ayin, aka ce Maza kawai za su yi. Kamar yadda aka yafe ma wani
mutum zuwa Jihadi saboda ya raka matarsa wurin aikin Hajji. Sahih Al￾Bukhari (3006) da Sahih Muslim (1344).
*Kusaurari cigaba da izinin Allah*
Gabatarwa a social media
*Ibrahim Nasidi Baban Ilham*
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support