*WANDA YA RASA WANI BANGARE NA SALLAR JANAZA, YA ZAI YI?*
*TAMBAYA*
Assalamu alaikum, Allah ya karawa wannan zaure albarka inada tambaya kamar haka shin sallah Jana,iza Ana rama kabbarar da aka rasa, misali kamar idan ba,a Fara sallah da mutum ba har yayi missing din wani bangare daga cikin sallah idan liman ya sallame shima sai yarama.
*AMSA*
Wa alaikumus salaam, Dukkan wanda ya rasa wani bangare na sallan jana'iza zai dauki raka'ar da ya tarar a matsayin raka'ar shi ta farko, idan liman ya idar sai shi ya ciko.
Babban Malami, Sheikh Abdulaziz Bn Baaz, Rahimahullah, ya ce:
*_Sunna ga dukkan mutumin da ya rasa wani bangare na kabbarbari na sallan jana'iza, shi ne ya biya wadannan kabbarbari, saboda fadin Manzon Allah, sallallahu 'alaihi wa sallama: "Idan an tsayar da salla, to ku zo mata kuna tafiya kuma ku kasance masu natsuwa, duk abun da kuka riska ku sallata, abin da kuma ya kubuce muku to ku ciko"..._* A duba مجموع الفتاوى 13/149.
An tambayi Malaman لجنة الدائمة للإفتاء cewa:
Mene ne hukuncin mutumin da ya rasa kabbarori uku a sallan janaza sai ya riski kabbara daya?
Sai suka bayar da amsa da cewa:
*_Zai cike sallan janazan ta yanda zai yi kabbarori uku a matsayin ramuwa kafin a dauke janazar daga inda take..._* a duba fatawa ta 8/399.
Wallahu A'alam.
21/02/2018
Daga: *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*
0 comments:
Post a Comment