FATAWAN RABON GADO (192) - Dr Jamilu Yusuf Zarewa ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Sunday 13 January 2019

FATAWAN RABON GADO (192) - Dr Jamilu Yusuf Zarewa



*Tambaya*

Assalamu alaikum.malam mutum ne ya rasu ya bar mata daya bai taba haihuwa ba, kuma iyayen shi duk sun rasu, sai kannan shi maza da mata wadanda suke uwa daya uba daya da kuma wadanda suke uba daya kawai, yaya rabon gadon zai kasance?

*Amsa*

Wa alaikum assalam, Za'a raba abin da ya bari gida hudu, a bawa matarsa kashi daya, ragowar sai a bawa 'yan'uwansa wadanda suke uwa daya uba daya su raba, duk namiji ya dau rabon mata biyu.

'Yan uba ba sa gado mutukar akwai namiji shakiki.

Allah ne mafi sani

*Dr. Jamilu Zarewa*

14/12/2018

Daga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*

Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support