June 2018 ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Thursday 28 June 2018

Tambaya da Amsa :- Shin yana halatta ga Mutum bayan yayi zina da mace, kuma ya Aureta ??

*```Assalamu alaikum Malam yana halatta ga mutum bayan yayi zina da mace, yana halatta ya aure ta?*```


_*AMSA:*_
*******

وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ


A shari'ance baya halatta ga mutum ya auri wacce yayi Zina da ita har sai sun tuba _*(Taubatan Nasuuhan)*_ su biyun.

*TUBA* yana tabbatuwa ne idan mutum yayi nadama akan abinda ya aikata da yin kyakkyawar niyyar bazai sake aikatawa ba.

Saboda haka idan sun tuba kuma sunyi nadamar abinda sukayi kuma sunyi alwashin bazasu sake aikatawa ba, to yana halatta agaresu suyi aure abisa ra'ayin mafi yawan malamai.

*Ibn Qudaamah (rahimahullah)* yace: Idan mace tayi Zina, to baya halatta ga Wanda yasani ya aureta har sai an cika sharudda biyu;
*1.* Ta gama iddarta.
*2.* Ta tuba daga Zinar da ta aikata
      Idan wadannan sharuddan sun cika, to ya halatta a aureta abisa ra'ayin lafiya yawan malamai, wannan shine ra'ayin Abubakar Al-siddiqu, Umar ibn Khaddab, Ibn Umar, Ibn Abbaas, Jaabir, Sa‘eed ibn Al-Musayyab, Tawoos, Jaabir Ibn Zayd, Ata’, al-Hasan, Ikrimah, Az-Zuhri, ath- Thawri, Ash-Shaafa‘i, Ibn Al- Mundhir da Ashaab ar-ra’y.
_*(All-Mughni , 7/108.)*_


والله أعلم،

***********************************


سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.


_*🌙Tambayoyin*_ _*Musulunci🌙*_
            _*WhatsApp*_ _*Group*_
_*+2347068043652*_
_*+2348164884055*_
Share:

Tambaya da Amsa:- Menene Hukuncin mata masu huda Hanci ??

*```ASSALAMU ALAIKUM!!!*```
*```MENENE HUKUNCIN MATA MASU HUDA HANCI??*```



_*AMSA:*_
********


وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ


An tambayi _*Shaykh Muhammad Saalih Al-Uthaymeen (Rahimahullah)*_ gameda Huda Hanci da Huda kunnuwa da ake yiwa yara mata saboda suyi kyau? Sai yace:
Ra'ayin da yake daidai shine babu laifi akan Huda kunne, saboda daya daga cikin dalilan huda kunne shine sanya halatattun kayan ado (Yan Kunne). An san cewa mata sahabbai sunada yan kunne da suke sanyawa a kunnuwansu.

Zafin ciwon hudawar mai sauki ne, kuma idan anyi huduwar ne a lokacin da yarinya tana karama, yafi saurin warkewa.


Abinda ya shafi *HUDA HANCI* kuma bazan iya tina cewa malamai sunce wani abu akan Huda Hanci ba, amma dai wani nau'in ne na canza halitta da gurguntawa idan muka kalli fuskar daga wajenta, duk dayake wasu basa kallonsa ta wannan fuska.

Idan mace tana acikin kasa ko gari Wanda sanya kayan ado a Hanci ana kallonsa wani nau'i ne na kwalliya da ado, to, babu wani abin laifi ga huda Hanci.
_*(Majmu'ul Fataawa Ibn Uthaymeen, shafi na 11, tambaya ta 69).*_



والله أعلم،

***********************************


سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.


_*🌙Tambayoyin*_ _*Musulunci🌙*_
            _*WhatsApp*_ _*Group*_
_*+2347068043652*_
_*+2348164884055*_
Share:

Wednesday 27 June 2018

Maganin Fitsarin Kwance daga Zauren Fiqhu

MAGANIN FITSARIN KWANCE :

TAMBAYA TA 2161
****************
Assalamu'alaikum Malam muna lafia, ya aiyuka ya Dalibai? Allah yayi mana jagoranci na alheri. Amin.

Malam Dan Allah a taimaka mana da maganin fitsarin kwance, wata  diyar yar'uwata ce ta kusa shekara 10 take fama dashi.

Sannan kuma ina barar addu'arka data dalibanka akan Allah ya kawo mani mijin aure mafi alheri. Amin. Jazakallahu Khair. Pls hide my I. D.


AMSA
***
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Ita wannan matsalar ana iya shawo kanta ne ta hanyoyi guda biyu kamar haka :

MAGANI : A nemi kwayoyin habbatus sauda, a rika yiwa yaro hayaki dasu. Kuma yana dan tsugunawa akan hayakin. Sannan kuma a rika gauraya masa habbatus sauda din yana shan cokali guda tare da zuma. Ko kuma ya shafe jikinsa da man Habbatus sauda din wanda akayi tofi acikinsa. In sha Allahu zai dena.

2. ADDU'A : Arika tofa masa wannan addu'ar, ko kuma akoya masa ya rika yinta da kansa, ko kuma a rubuta masa ajikin takarda ya sanya ajikinsa yayin da zai kwanta.

Kamar yadda aka ruwaito daga Abdullahi bn Amru bn Al-As Sahabin Manzon Allah (saww) yana rataya ma 'ya'yansa Qanana wannan addu'ar. Gata nan kamar haka :

"أعوذ بكلمات الله التامات من غضبه وعقابه ومن شر عباده و من همزات الشياطين و أن يحضرون".

'A'udhu bi kalimatil Laahit tammati min ghadhabihee wa 'iqabihee wa min sharri ibadihee wa min hamazatish shayateen wa an yahdhurooni.

FASSARA : Ina neman tsari da cikakkun kalmomin nan na Allah daga fushinsa da Uqubarsa, kuma daga sharrin bayinsa, kuma daga sharrin fizge-fizgen shaitanu, kuma (ina neman tsarinsa) kada su halartoni.

In sha Allahu koda babban mutum ne yake fama da matsalar fitsarin kwance, in dai ya lazimci wadannan abubuwan tare da gaskatawa zai ga biyan bukatarsa.

WALLAHU A'ALAM.

Muna rokon Allah da albarkar sunayensa da siffofinsa da kalmominsa, ya baki Miji nagari. Ya tsare miki mutuncinki da imaninki dake da dukkan dalibanmu da 'yan uwanmu Mata marassa aure. Ameeen.

DAGA ZAUREN FIQHU.
Share:

Tambaya da Amsa :-Hukuncin yin sallar jam'i A Gida !!! Dr. Jamilu yusuf zarewa

*_HUKUNCIN YIN SALLAR JAM'I A GIDA !!!_*

*_Tambaya_*

Assalamu alaikum.  Malam mene hukuncin sallar  namiji da ba ya son zuwa masallaci  jam'i saidai ya tara iyalinsa a gida ayi sallah tare?


*_Amsa_*
Wa alaikum assalam

To 'yar'uwa Malamai sun yi sabani game da sallar jam'i a masallaci.

1. A wajan malaman Malikiyya zuwa sallar jam'i sunna ne saboda fadin Annabi S. A.W. "Sallar jama'a tafi sallar mutum daya da lada ashirin da bakwai" hadisin yana nuna ingancin sallar wanda ya yi sallah shi kadai, tun da an tabbatar masa da lada daya.

2. Ya wajaba yin sallah a masallatai a cikin jama'a saboda fadin Annabi (SAW)  "Na yi niyyar na yi umarni a tsayar da sallar jam'i, ni kuma na je na kona gidajan wadanda ba Sa halarta sallah a masallaci" wannan ita ce maganar Malamai da yawa.
Ibnu-Mas'ud yana cewa: "Babu wanda yake kin zuwa sallar jam'i sai munafiki, wanda aka san  shi da munafunci,  akan kawo mutum ranga-ranga ba shi da lafiya a tsayar da shi a tsakanin Sahu".
Wani Makaho ya zo wajan Annabi (SAW)  ya nemi ya yi masa izni ya yi sallah a gida saboda ba shi  da Jagora, ya ba shi izni,  bayan ya tafi sai ya Kira shi ya ce masa kana jin kiran sallah? sai ya ce E, sai ya ce to ka amsa".

Allah yana cewa a Suratul Bakara aya ta (43): "Kuma ku yi sallah tare da masu yin sallah"

A bisa dalilan da suka gabata za mu fahimci cewa: Yin sallar jam'i a masallaci shi ne abin da Shari'a ta zo da shi, kuma wajibi ne ga wanda yake da iko, tun da ga shi har Annabi (SAW) ya yi niyyar zai kona gidan wadanda ba sa halarta.
Idan akwai nisa tsakaninsa da masallaci ko kuma yana da lalura ba za'a ce ya aikata haramun ba in ya yi sallah a gida tare da iyalansa saboda fatawar Malikiyya da ta gabata da kuma aya ta karshe a suratul Hajj wacce take nuna sauki da rashin kunci a addinin musulunci.

Allah ne mafi sani.

*_Dr. Jamilu Zarewa_*

27/06/2018

Daga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*
Share:

Tuesday 26 June 2018

Tambaya da Amsa :- Idan mutum ya rasu ya bar Mata guda daya1 da 'ya'ya maza guda uku 3 da 'ya mace guda daya1, kuma ya bar dukiya ta miliyan takwas da dubu 'dari biyar (8.5million). Ya Kason kowa zai kasance?

*```Assalamu alaikum*```
*```Tambaya na shine:*```
*```Idan mutum ya rasu ya bar Mata guda daya1 da 'ya'ya maza guda uku 3 da 'ya mace guda daya1, kuma ya bar dukiya ta miliyan takwas da dubu 'dari biyar (8.5million). Ya Kason kowa zai kasance?*```




_*AMSA:*_
*******

وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ،



Abu Na farko daza'a aiwatar akan dukiyar mamaci shine biyan bashi da wasiyya, kafin a shiga gundumar rabon gado.


Idan namiji ya rasu yabar mata daya da yara maza uku (3) da 'ya mace daya.
Idan wadannan sune magadansa kadai wadanda ya bari.

To anan kason matar zai kasance 1/8 (Sumuni) Na dukiyar da yabari, 'yarsa daya mace za'a bata Rabin kason namiji daya.
Kamar yadda Allah ya fada acikin Suratun Nisaa'i ayah ta 11 da 12.

ﻳُﻮﺻِﻴﻜُﻢُ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻓِﻲ ﺃَﻭْﻟَﺎﺩِﻛُﻢْ ۖ ﻟِﻠﺬَّﻛَﺮِ ﻣِﺜْﻞُ ﺣَﻆِّ ﺍﻟْﺄُﻧْﺜَﻴَﻴْﻦ

Allah yana yimuku wasiyyah acikin 'ya'yanku, namiji yanada rabon mata biyu.........(Nisaa'i 11)


ﻭَﻟَﻬُﻦَّ ﺍﻟﺮُّﺑُﻊُ ﻣِﻤَّﺎ ﺗَﺮَﻛْﺘُﻢْ ﺇِﻥْ ﻟَﻢْ ﻳَﻜُﻦْ ﻟَﻜُﻢْ ﻭَﻟَﺪٌ ﻓَﺈِﻥْ ﻛَﺎﻥَ ﻟَﻜُﻢْ ﻭَﻟَﺪٌ ﻓَﻠَﻬُﻦَّ ﺍﻟﺜُّﻤُﻦُ ﻣِﻤَّﺎ ﺗَﺮَﻛْﺘُﻢْ ﻣِﻦْ ﺑَﻌْﺪِ ﻭَﺻِﻴَّﺔٍ ﺗُﻮﺻُﻮﻥَ ﺑِﻬَﺎ ﺃَﻭْ ﺩَﻳْﻦ

........Kuma (Su Matan) sunada rubu'i daga abinda kuka bari (Na dukiya) idan reshe ('ya'ya) bai kasance ba gareku, to, idan kuwa reshe ya kasance gareku, to sunada sumuni (1/8) daga abinda kuka bari, daga bayan wasiyya wanda kukayi ko kuma bashi (debt)............(Nisaa'i 12).

Reshe acikin ayah ta 12 yana nufin 'ya'ya. Idan miji ya mutu yabar mata ita kadai babu 'ya'ya, to rabon ta shine 1/4.

Idan kuma akwai 'ya'ya to rabonta shine 1/8 kamar yadda ya tabbata a ayar.

A tambayar mu ta sama. Namiji ya rasu yabar masu gadonsa kamar haka:
1. Mata daya
2. Yara Maza uku (3)
3. Yarinya daya

Sannan yabar kudi naira miliyan takwas da dubu dari biyar:
N8,500,000

Ga yadda kason kowa zai kasance:

MATA
******
Za'a bata 1/8 Na N8,500,000
Shine ya kama miliyan daya da dubu sittin da biyu da naira dari biyar.

====N1062500


Idan an cire rabon matarsa, za'a bar N7,437,500.

Anan maza uku ne, kowanne kashi biyu za'a bashi, mace kuma kashi daya.

Idan ka hada kashi biyu sau uku zai baka kashi shida.
       (2×3)=6

Sannan a tara da kashi daya Na mace zai bamu kashi bakwai
6+1=7

Yanzu zamu raba N7,437,500 zuwa gida bakwai

(N7,437,500/7)==N1062500.

Mace kashi daya
Kowanne namiji kashi biyu.

Kashi biyu zai bamu
1062500+1062500
      ==N2,125,000


YARA MAZA
**************
Kowannensu zai samu " Naira Miliyan biyu da dubu dari da ashirin da biyar"

======N2,125,000


'YARSA MACE
***************
Zata samu "Naira miliyan daya da dubu sittin da biyu da naira dari biyar"

======N1,062,500.




والله أعلم،

***********************************


سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.


_*🌙Tambayoyin*_ _*Musulunci🌙*_
            _*WhatsApp*_ _*Group*_
_*+2347068043652*_
_*+2348164884055*_
Share:

Archive

Unordered List

Support