November 2018 ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Tuesday 20 November 2018

Zan Iya Auran Wanda Ba Shi Da Uba ? - Dr Jamilu Yusuf Zarewa

Tambaya

Assalamu Alaikum, Don Allah Malam, wata dalibata ce ke neman shawara kan auren wani mutumin kirki, amma baida uba !!!
Wane irin kalubale ku ke hange a kanta, a yanzu da nan gaba?
Me ye mafi alkhairi a gare ta?
Jazakumullahu bikhairin Malam. Bissalam

Amsa

Wa alaikum assalam
Mutukar ta yarda da addininsa da kuma dabi'unsa tana iya auransa kamar yadda hadisin Tirmizi ya tabbatar.

Kasancewar an haife shi ba ta hanyar aure ba, ba laifinsa ba ne, Allah ba ya dorawa wani laifin wani.

In dai shegantuwarsa ba ta shahara a tsakanin mutane ba, ta yadda nan gaba za'a dinga aibanta abin da kuka haifa tare, kina iya auransa, tun da mutumin kirki ne.

Duk da cewa ya halatta a shariance ki auri wanda ba'a san mahaifinsa ba, saidai idan kika ji tsoran tozarta zuriyarki, to ana barin halal don kunya, kamar yadda Hausawa suke fadi kuma dalilin sharia ya tabbatar.

Allah ne mafi sani

Dr. Jamilu Zarewa

17/11/2018
Share:

Monday 12 November 2018

Hukunci Kashe Kwadi Da Cin Namansu! - Dr Jamilu Yusuf Zarewa

Tambaya

  Assalamu alaikum Malam menene ingancin hadisin da yake cewa: "Annabi SAW ya hana kashe Kwadi saboda kukansu Tasbihi ne ga Allah"? 

 Amsa 

 Wa alaikum assalam, Tabbas ya tabbata a hadisin Abu-dawud mai lambata: (5269) da kuma Nas'i (2/202) cewa: wani likita ya tambayi Manzon Allah akan kashe kwadi saboda sanyawa a magani sai Annabi ya hana shi kashe su".  Baihaki ya rawaito daga maganar Abdullahi Bn Amri bn Al-Ass cewa "Kada Ku kashe kwadi saboda kukansu tasbihi ne ga Ubangijinsu". Duk da cewa hadisin zai iya daukar cewa ya ji ne daga Manzon Allah saidai Hafiz Bn Hajar yana cewa " Abdullahi bn Amr bn Ass ya shahara da yin riwaya daga malaman Yahudu da Nasara don haka ba dole ne ya zama daga Annabi SAW ya ji ba.  Kashe kwadi haramun ne saboda hadisin Abu-dawud da Nasa'i da ya gabata, kamar yadda cin su ma haramun ne, saboda ba zai yiwu a ci dabba ba sai bayan ranta ya fita.  Allah ne mafi sani  

 Amsawa
✍🏻  DR. JAMILU YUSUF ZAREWA 11/11/2018

Share:

Kakanta Ba Ta Iya Sallah Saboda Rudewa Ko Za Ta Fadi Akanta? - Dr Jamilu Yusuf Zarewa

Tambaya

Assalamu alaikum ina fatan Dr yana cikin koshin lafiya, Allah ya kara masa imani da fasaha Amin.Dr kakata ce tsufa ya kamata ga rashin lafiya, yaranta tara bata gane Ko daya daga cikin su gashi bata gane alwala balantana Sallah, Ko an mata alwala bazata gane Sallah ba, ga shi tana yini da pampas a jikinta ya zamuyi da sallanta???

Amsa

Wa alaikum assalam Ku yi iya ba-kin kokarinku wajan Ku ga ta kwatanta sallah, in bai yiwu ba ku kyale ta, saboda Allah ba ya dorawa rai abin da ba zai iya ba kamar yadda aya ta karshe a Suratul Bakara ta yi bayanin gamsashshe akan hakan.
A zahirin nassoshin sharia in har ba ta gane komai to za ta dau hukuncin Mahaukata ne, tun da ba ta cikin hayyacinta,
 mahaukaci  hadisi ya tabbatar da sarayuwar sallah daga kansa.

Sallah ba ta karbar wakilci, don haka ba Wanda zai rama mata a cikinku.

Allah ne mafi sani 

Amsawa✍🏻

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

11/11/2018

Sunday 11 November 2018

Fatawar Rabon Gado (188) - Dr Jamilu Yusuf Zarewa

*Tambaya*

Assalamu alaikum malam mutum ne ya mutu  yabar mahaifi, mahaifiya,  mata, yar mace daya , da yan uwa wanda suke uwa daya uba daya Maza uku mata buyi.

*Amsa*

Wa alaikum assalam Za'a raba kashi (24), a bawa matarshi kashi uku,  mahaifiyarshi kashi hudu, 'yar shi kashi sha biyu, mahaifinsa kashi biyar.

Allah ne mafi sani

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
06/11/2018

Share:

Fatawar Rabon Gado (187) - Dr Jamilu Yusuf Zarewa

*Tambaya*

Assalamu alaikum dafatan Malam Yatashi Lafiya.
dan Allah Malam Ya rabon gadon mutumin da ya bar mahaifi, mahaifiya,  mata, yara Maza biyu, da yan'uwa wanda suke uwa daya uba daya Maza uku mata biyu ?

*Amsa*

Wa alaikum assalam Za'a raba gida (24), a bawa matarsa kashi uku, mahaifiyarsa kashi hudu, babansa kashi hudu , ragowar sai a bawa yaransa su raba.

Allah ne mafi sani

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
06/11/2018

Share:

Fatawar Rabon Gado (186) - Dr Jamilu Yusuf Zarewa

*Tambaya*

ASSALAMU ALAIKUM MALAM MUTUM NE YA RASU YA BAR MAGADA KAMAR HAKA:
AKWAI UWA AKWAI MATAN AURE BIYU AKWAI DIYA (MAZA UKU) MATA (GOMA SHA BIYU) KUMA KUDI NE ZA A RABA MUSU NAIRA DUBU TALATIN DA UKU.

*Amsa*

Wa alaikum assalam Za'a bawa Mahaifiyarsa (5500) matansa biyu kuma za'a ba su (4125) su raba, ragowar (23375) sai a bawa Diyansa su rabe a tsakaninsu, duk namiji ya dau rabon mata biyu.

Allaha ne mafi sani

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF  ZAREWA*

05/10/2018

Share:

Babu Bambanci Tsakanin Dan Zina Da Dan Halal A Wajen Rabon Gado ! - Dr Jamilu Yusuf Zarewa

*Tambaya*

Assalamualaikum dan Allah tambaya nake yi mu biyar mamanmu ta haifa amma biyu daga cikinmu ta hanyan aure aka same su uku kuma ba tahanyar aure aka same su ba, shin sunada gadon ta ko,  ba su ? kuma ta mutu da bashi da yawa akanta kuma ba mu da hanyar biya mata shi domin kudin suna da yawa akalla yakai dubu dari biyu.
Dan Allah mafita muke nema, Mungode

*Amsa*

Wa alaikum assalam, idan mace ta yi cikin shege kuma ta haifi Da, daga baya ta mutu Dan zinar da ta haifa zai gaje ta, saboda Allah madaukakin sarki a cikin suratun Nisa'i aya ta : 10 ya yi wasiyya a bawa 'ya'yaye  gado, Dan zina kuma yana cikin jerin 'ya'yayen mahaifiyarsa, wannan yasa zai gaje ta.                                                                                                                                                               
Don haka babu Bambanci a cikinku tsakanin Wanda aka haifa ta hanyar aure da kuma Wanda aka samu ta hanyar Zina.
Ba'a raba gado sai an fara biyawa mamaci bashinsa, don haka ko da duk abin da ta bari zai kare dole Ku biya kafin a raba, kamar yadda Allah ya bayyana a cikin suratun Nisa'i aya ta (11).

Dan zina baya gadon mahaifinsa ko da kuwa mahaifin ya amince Dansa ne a wajan mafi yawan malamai.

Allah ne mafi sani.

*Dr. Jamilu Zarewa*

03/11/2018

Archive

Unordered List

Support