Shin yana halasta a nemawa dan bidi'a gafara da rahamar Allah?? ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Wednesday, 16 May 2018

Shin yana halasta a nemawa dan bidi'a gafara da rahamar Allah??

SHIN YA HALASTA A NEMAWA DAN BID'AH GAFARA DA RAHAMAR ALLAH?

Farko dai Aqeedar Al-Wala'u Wal Bara'u (Soyayya da kiyaya) ginshiki ne na Addini, wajibine Musulmi ya so 'yan uwanSa Musulmi kuma yaki kafirai kamar yadda wajibine Dan Salafiyyah yaso 'yan uwan sa kuma yaki 'yan bid'ah GWARGWADON ABINDA YAKE TARE DA SU NA BID'AH KAMAR YADDA ZAI SO SU GWARGWADON ABINDA YAKE TARE DA SU NA SUNNAH. Idan kuma bid'ar ta kafircine to wannan babu wani nau'i ko kaso na soyayya da yake da shi daga Musulmai.

Sai dai shi wannan kiyayyar ba a sake ake yin sa ba, akan yi dubi ne zuwa ga maslaha, wani lokaci bayyana shi kiyayyar shine Daidai, wani lokaci kuma kuskure ne sbd rashin maslaha dake ciki.

2- Nemawa dan bid'ar da bid'arSa ta kafircine gafara da rahamar Allah to, wannan kuskure ne kuma haramunne domin Allah Madaukaki ya hana.
Shaikhul Islam Ibnu Taimiyah yace:
من علم منه النفاق والزندقة فإنه لا يجوز لمن علم ذلك منه الصلاة عليه وإن كان مظهرا للإسلام.
الفتاوى الكبرى (3/18).
Wanda aka san Munafunci da Zindiqanci tattare da shi to, bai halasta ga wanda yasan hakan yayi masa sallah ba koda kuwa ya kasance yana bayyana Musulunci.

2- Dan bid'ar da bid'arSa bata kai ga kafirci ba to, ya halasta a nema masa gafara da rahamar Allah Madaukaki domin shi yana matsayin Musulmi mai sabo da zunubi ne.

Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah yace:
فكل مسلم لم يعلم أنه منافق جاز الاستغفار له، والصلاة عليه وإن كان فيه بدعة أو فسق لكن لا يجب على كل أحد أن يصلي عليه.
منهاح السنة (5/178).
Duk wani Musulmi da ba a san cewa shi Munafuki bane to nema masa gafara ya halasta, da kuma yi masa sallah koda kuwa akwai wani bid'ah ko fasikanci tattare da shi, sai dai bai wajaba akan kowa da yayi masa sallah ba.

Ina jin Sheik Rabee'i Almadkhaly yana da magana irin wannan yace:
أما الترحم على أهل البدع، فإنه يجوز الترحم عليهم، وهذا شيء عليه السلف الصالح ومنهم أحمد بن حنبل، ودل على ذلك نصوص من كتاب الله -تبارك وتعالى- ومن سنة رسول الله عليه الصلاة والسلام، والذي ينازع في هذا جاهل ضال، وصلى الله على نبينا محمد وعلى آله وصحبه وسلم.
شريط بعنوان: لقاء مع الشيخ في مسجد الخير.
Amma nemawa 'yan bid'ah rahama to, lalle ya halasta a nema musu rahama, wannan wani abune da magabata suke kansa, daga cikin su akwai Imam Ahmad dan Hanbal, kuma nassosa daga Littafin Allah da Sunnah sun yi nuni akan hakan, wanda yake jayayya a cikin hakan to shi JAHILI NE BATACCE".

Sbd haka duk wani nassi daga Magabata da yake nuna rashin halascin nemawa 'yan bid'ah gafara da rahama to, za a dauke su ne akan 'yan bid'ah din da bid'ar su ta kai ga kafirci.
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support