Ramadhaniyyat@1439H [3] - Sheikh Dr. Muhd Sani Umar R/lemo ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Sunday, 20 May 2018

Ramadhaniyyat@1439H [3] - Sheikh Dr. Muhd Sani Umar R/lemo

*Ramadhaniyyat@1439H [3]*

*Daga Sheikh Dr. Muhd Sani Umar R/lemo*

Tahajjudi

Allah Ta'ala yana cewa:
(Da daddare kuwa sai ka yi tsayuwar dare da shi (Alqur’anin) qarin (daraja) ne gare ka, tare da qaunar Ubangijinka ya tashe ka a matsayin sha-yabo ("watau matsayin mai ceto"). Isra'i, aya ta 79.

A Makka ne Allah ya shar'ata wa Annabinsa (S.A.W) tsayuwar dare watau sallar "Tahajjudi". Wannan dalili ne da yake nuna falalar wannan salla. Domin Allah ya shar'anta Annabi (S.A.W) mafi girma kuma mafi falalar ayyuka a Makka. Shar'anta wani aiki tun a farkon Musulunci dalili ne dake nuna girmansa da falalarsa, saboda haka ne ma aka shar'anta Tauhidi tun a Makka, hakanan aka kuma shar'anta wasu daga cikin rukunan Musulunci tun a farko-farkon Musuluncin.
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support