Hukuncin MMM Business
An dade ana tambayata hukuncin MMM Business daga ciki akwai tambayar da akayimin a July da ya shude a A.B.U Zaria bayan na kamala wata public lecture, kuma yanzu haka akwai tambayoyi da yawa acikin inbox dina. Ko nace ban saniba ko na kyale saboda bani da cikakken bincike akai, amma yanzu nayi bincike akai. Abubuwan da na bincika kafin wannan fatwa sune:
i) Website din MMM
ii) Website din Securities and Exchange Commission, Nigeria, domin jin ra’ayinsu gameda MMM
iii) Online Videos da documentaries gameda MMM Business ciki harda 41 mins video na kaddamar da business din a Nigeira
iv) Tattaunawar da wasu ‘yanuwa sukayi gameda Bussiness din.
Bayan haka nafito da natija kamar haka:
1) MMM Business kamar yadda matar da tayi presentation din shi a Nigeria ta bada definition shine: “MMM is a platform that links [a] giver to the receiver… and when I give I get rewarded for it.” [ Mai bayarwa ya baiwa mai nema domin wanda yabayar ya samu fa’ida] Wannan shine definition din da kowa yake bayarwa koda yake wani lokacin kalimomin sukan sha ban ban amma ma’anar daya ce.
2) Wannan business din baya halasta domin shine ainihin ﺭﺑﺎ ﺍﻟﻔﻀﻞ ” wanda Musulunci ya hana. Ka bada kudi ga mai nema domin a mayarma ka da fiye da abinda ka bayar. Ko kafin ka bayar za’a baka faidar ko bayan ka bayar duka dayane, ko wanda ka baiwa bashi zai baka ko ta wata hanya za'a karbo maka duka daya ne. Ba dole bane sai lokacin da za’a mayar maka ne za’ayi Karin ba, ko wane lokaci Karin zai shiga haram ne, don wannan aka haramta ﺑﻴﻊ ﺍﻟﻌﻴﻨﺔ ” a Musulunci. A MMM za’a baka faidar 30% tun kafin a karbi kudinka.
3) Wannan Business din yana da hadarin gaske domin haramtaccen business ne a Nigeria da kasashe da yawa. Securities and Exchange Commission, Nigeria sun yi gargadi da hana jama’a shiga wanna business da kiransa illegal kamar yadda suka fada a wani article da sukayi publishing a website din su a ranar 30/08/2016 sukace: “The general public is hereby advised to distance themselves from this online scheme. Please note that anyone that subscribe to this illegal activity does so at his/her own risk.” Irin wanna kadai ya isa ya hana wanna Business din
4) Kasashe dayawa sun haramta wannan Business ga jama'ar su domin ganin cewa ba tabbas akwai rudi aciki. Cikin kasashen da suka hana akwai China da South Africa. Samun rudi ﻏﺮﺭ a business zai iya zama dalilin haramcin sa a musulunci.
5) Duk mai hankali ya dibi Business din yasan akwai rudu ciki maiyawan gaske, kuma yasan karshensa jama’a da yawa zasu rasa dukiyar su. A musulunci idan mutun zai bada bashi saida shaidu guda biyu sai idan ya amince da wanda zaibaiwa, a MMM zaka bayarda dukuyarka ga wanda baka sani ba. Saboda hakane ma hukumomi suke yaki dashi. Duk abinda masana sukace karshen sa akwai hadari mai girma to wanna ma ya isa ya haramtashi a Musulunci.
Allah yayi man jaogora.
Jabir Sani Maihula, Nottingham, UK.
15/11/2016