August 2018 ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Thursday, 16 August 2018

[Audio] :- Karyarku 'Yan Shi'a Asirinku Ya Tonu - Sheikh Kabiru Haruna Gombe

Sheikh : _*MUHAMMAD KABIRU HARUNA GOMBE*_
( *Sakataren kungiyar Izala ta kasa*)


Asabar : *11 August 2018*


Wuri : *Masallacin Sultan Bello Kaduna*

DOMIN SAUKO DA WANNAN AUDIO SAUKU SHIGA WANNAN BLUE RUBUTU DAKE KASA 👇🏼👇🏼👇🏼

DOWNLOAD AUDIO NOW

_*Kar  Ku  Sake  A  Baku  Labari .........*_

Ayi Sauraro  Lafiya  👂🏻



Share:

Wednesday, 8 August 2018

HUKUNCIN WANDA YA SADU DA MATARSA ACIKIN HAILA

HUKUNCIN WANDA YA SADU DA MATARSA ACIKIN HAILA :

TAMBAYA TA 2547
*******************
SALAMUN ALAIKUM MALAM MENENE HUKUNCIN WANDA YASADU DA MATARSHI TANA HAILA AMMA ARASHIN SANI ?

NAGODE MALAM.

AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Allah Madaukakin Sarki ya haramta wa Mazaje saduwa da Matayensu alokacin da suke cikin jinin haila. Allah yace :

"SUNA TAMBAYARKA GAME DA JININ HAILA, KACE (MUSU) SHI NAJASA NE. KU NISANCI MATAYE ACIKIN FARJOJINSU KADA KU KUSANCESU (DA JIMA'I) HAR SAI SUNYI TSARKI".

(Suratul Baqarah ayah ta 223).

Kuma akwai hadisin da Manzon Allah (saww) yace Wanda yayi jima'i da matarsa alhali tana haila,  to sai yayi sadaqah da dinare guda (Kamanin naira dubu sittin ₦60,000).

Acikin Maluman Fiqhu akwai wadanda suka tafi bisa doron hadisin. Akwai kuma wadanda suka ce zai yi istighfari ne tunda ya aikata babban laifi. Amma babu kaffara akansa.

Imamun Nawawiy yace "Da ache mutum zai aikata haka (wato jima'i da mai haila) cikin Mantuwa ko rashin sanin cewa tana haila, ko rashin sanin haramcinsa to babu laifi akansa kuma babu kaffarah.

Amma idan mutum ya aikata hakan da gangan, tare da sanin cewa akwai hailar, da kuma sanin haramcinsa, to hakika ya dauki zunubi mai girma kuma wajibi ne gareshi ya tuba".

Kuma acikin maganar wajibcin yin kaffarar akwai zantuka guda biyu. Amma abinda yafi inganci shine babu kaffarah akansa".

WALLAHU A'ALAM.

DAGA ZAUREN FIQHU (30/07/2018  17/11/1439).
Share:

Tamabaya da Amsa :- Shin yana hallatta macce budurwa tashafa turaree Sannan tafito waje dashi??

*|```Assalamu alaikum*```
*```Malam ko ya hallatta macce budurwa tashafa turaree Sannan tafito waje dashi??*```



_*AMSA:*_
*******

وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ،


Haramun ne mace ta sanya turare ta fita inda wasu maza zasuji kamshinsa. Dalili kuwa shine:


ﺛﺒﺖ ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺃﻧﻪ ﻗﺎﻝ: ﺃَﻳُّﻤَﺎ ﺍﻣْﺮَﺃَﺓٍ ﺍﺳْﺘَﻌْﻄَﺮَﺕْ ﻓَﻤَﺮَّﺕْ ﻋَﻠَﻰ ﻗَﻮْﻡٍ ﻟِﻴَﺠِﺪُﻭﺍ ﻣِﻦْ ﺭِﻳﺤِﻬَﺎ ﻓَﻬِﻲَ ﺯَﺍﻧِﻴَﺔٌ.
ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺃﺣﻤﺪ‏(19212‏) ﻭﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲ ‏(5126‏) ﻭﺣﺴﻨﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ.

_Ya tabbata daga *Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam)* yace idan mace ta sanya turare ta wuce ta gaban mutane (Maza) domin suji kanshin turaren ta, toh ita mazinaciya ce._
*Imam Ahmad ya ruwaito shi a hadisi mai lamba 19212.* da *Nisaa'i hadisi mai lamba 5126.*
_Albani ya inganta shi Cikin sahihul jami'i._


ﻋَﻦْ ﺯَﻳْﻨَﺐَ ﺍﻣْﺮَﺃَﺓِ ﻋَﺒْﺪِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺑﻦ ﻣﺴﻌﻮﺩ، ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ﻭﻋﻦ ﺯﻭﺟﺎ، ﻗَﺎﻟَﺖْ: ﻗَﺎﻝَ ﻟَﻨَﺎ ﺭَﺳُﻮﻝُ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ: ﺇِﺫَﺍ ﺷَﻬِﺪَﺕْ ﺇِﺣْﺪَﺍﻛُﻦَّ ﺍﻟْﻤَﺴْﺠِﺪَ ﻓَﻠَﺎ ﺗَﻤَﺲَّ ﻃِﻴﺒًﺎ.
ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ ‏(443).

_An karbo daga *Zainab* matar *Abdullahi Ibn Mas'ud* (radiyallahu anha Wa zaujaha) tace: *Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam)* yace damu; Idan dayanku zata tafi masallaci kada a shafa turare._
*Muslim ya ruwaito shi a hadisi mai lamba 443.*



والله أعلم،

***********************************


سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.


_*🌙Tambayoyin*_ _*Musulunci🌙*_
            _*WhatsApp*_ _*Group*_
_*+2347068043652*_
_*+2348164884055*_
Share:

Tuesday, 7 August 2018

Hukunce-Hukuncen Mai Takaba ?? Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

*HUKUNCE-HUKUNCEN MAI TAKABA*


*Tambaya:*

Assalamu alaikum wa rahmatullaah. gafarta Malam pls ayi mana bayani koda a takaice ne dangane da hukunce - hukuncen takaba... Na shiga wajen mahaifiya dazu, take cewa in tambaya mata Malamai tanadin shari'a akan wannan al'amari. Nagode


*Amsa:*

Wa alaikum assalam.To dan'uwa ina rokon Allah ya jikan mahafinku, akwai hukunce-hukunce  da suka shafi takaba, ga muhimmai daga ciki:

*1.* Mai takaba za ta zauna a gidan mijinta ba za ta fita ba, har sai ta gama iddarta, wacce take wata hudu da kwana goma, kamar yadda aya ta: 234 a suratul Bakara take nuni zuwa hakan .

*2.* Ba za ta saka kaya masu kyau ba, don haka za ta guji ado, kamar yadda hadisin Abu-dawud mai lamba ta: 2304, ya yi bayanin hakan.

*3.* Shari'a ta hana mai takaba ta sanya turare, kamar yadda hadisin Bukhari mai lamba ta: 5343, ya tabbatar da hakan,

*4.* Malamai suna cewa mai takaba ba za ta sanya tozali ba , kamar yadda hadisin Nasa'i mai lamba ta: 3565 ya bayyana hakan.

*5.*  An hana mai takaba yin lalle,  kamar yadda hanin ya zo a hadisin Abu-dawud mai lamba ta: 2304.

*6.* Idan wata bukata ta kama za ta iya fita daga gida, ko da rana ne ko da dare.

*7.* Za ta iya yin Magana da mazan da ba muharramanta ba, idan bukatar hakan ta kama, saidai ta guji, sanyaya murya, kamar yadda aya ta 32 a suratul-ahzab ta hana sanyaya murya ga wadanda ba muharramai ba.

*8.* Babu wani launi na kaya na musamman da aka shar'anta mata ta sanya, don haka, duk kayan da ba kwalliya a jikinsu ya halatta ta sanya su .

*9.* Za ta iya yin wanka da sabulun da yake ba mai kanshi ba .

*10.* Za ta iya zama ta yi hira da makusantanta, har ma za ta iya bude gashin kanta, idan su duka muharramanta ne .

*11.*  Bai halatta wani ya nemi auranta ba, har sai ta gama idda, saidai za'a iya yin jirwaye mai kama da wanka, kamar yadda aya ta 235 ta yi nuni zuwa hakan.

*12.* Idan mai takaba tana da ciki, to iddarta ita ce:  haife abin da take dauke da shi, kamar yadda hadisin Subai'a mai lamba ta: 5014 a Sahihul Bukhari ya tabbatar da hakan.

Allah ne mafi sani.

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*

27\3\2015
Share:

Archive

Unordered List

Support