HUKUNCIN WANDA YA SADU DA MATARSA ACIKIN HAILA ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Wednesday 8 August 2018

HUKUNCIN WANDA YA SADU DA MATARSA ACIKIN HAILA

HUKUNCIN WANDA YA SADU DA MATARSA ACIKIN HAILA :

TAMBAYA TA 2547
*******************
SALAMUN ALAIKUM MALAM MENENE HUKUNCIN WANDA YASADU DA MATARSHI TANA HAILA AMMA ARASHIN SANI ?

NAGODE MALAM.

AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Allah Madaukakin Sarki ya haramta wa Mazaje saduwa da Matayensu alokacin da suke cikin jinin haila. Allah yace :

"SUNA TAMBAYARKA GAME DA JININ HAILA, KACE (MUSU) SHI NAJASA NE. KU NISANCI MATAYE ACIKIN FARJOJINSU KADA KU KUSANCESU (DA JIMA'I) HAR SAI SUNYI TSARKI".

(Suratul Baqarah ayah ta 223).

Kuma akwai hadisin da Manzon Allah (saww) yace Wanda yayi jima'i da matarsa alhali tana haila,  to sai yayi sadaqah da dinare guda (Kamanin naira dubu sittin ₦60,000).

Acikin Maluman Fiqhu akwai wadanda suka tafi bisa doron hadisin. Akwai kuma wadanda suka ce zai yi istighfari ne tunda ya aikata babban laifi. Amma babu kaffara akansa.

Imamun Nawawiy yace "Da ache mutum zai aikata haka (wato jima'i da mai haila) cikin Mantuwa ko rashin sanin cewa tana haila, ko rashin sanin haramcinsa to babu laifi akansa kuma babu kaffarah.

Amma idan mutum ya aikata hakan da gangan, tare da sanin cewa akwai hailar, da kuma sanin haramcinsa, to hakika ya dauki zunubi mai girma kuma wajibi ne gareshi ya tuba".

Kuma acikin maganar wajibcin yin kaffarar akwai zantuka guda biyu. Amma abinda yafi inganci shine babu kaffarah akansa".

WALLAHU A'ALAM.

DAGA ZAUREN FIQHU (30/07/2018  17/11/1439).
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support