Shin ko kunsan Cewa Sallar Jana'Iza kabbarorinta suna wuce 4 ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Sunday 23 September 2018

Shin ko kunsan Cewa Sallar Jana'Iza kabbarorinta suna wuce 4

*JANA'IZA A MAHANGAR SUNNAH??-07!!*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ*
📓📔
Watsaps
08036222795
09031200070
.
.
...
Yau 09-04-1439 wacce tayi dai dai da, 27-12-2017, Cigaban Lekca mai taken *JANA'IZA A MAHANGAR SUNNAH:*
...
=
Wannan shine bayani na Bakwai:
=
=
*«ﺇِﻥَّ ﺍﻟْﺤَﻤْﺪَ ﻟِﻠَّﻪِ، ﻧَﺤْﻤَﺪُﻩُ ﻭَﻧَﺴْﺘَﻌِﻴﻨُﻪُ، ﻣَﻦْ ﻳَﻬْﺪِﻩِ ﺍﻟﻠﻪُ ﻓَﻠَﺎ ﻣُﻀِﻞَّ ﻟَﻪُ، ﻭَﻣَﻦْ ﻳُﻀْﻠِﻞْ ﻓَﻠَﺎ ﻫَﺎﺩِﻱَ ﻟَﻪُ، ﻭَﺃَﺷْﻬَﺪُ ﺃَﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻟَّﺎ ﺍﻟﻠﻪُ ﻭَﺣْﺪَﻩُ ﻟَﺎ ﺷَﺮِﻳﻚَ ﻟَﻪُ، ﻭَﺃَﻥَّ ﻣُﺤَﻤَّﺪًﺍ ﻋَﺒْﺪُﻩُ ﻭَﺭَﺳُﻮﻟُﻪُ*
_Bayan haka yanzu kuma kai tsaye zamu shiga bayanine gameda Sallar jana'iza, Ita sallar gawa fardu kifaya ce wato wasu suna dauke ma wasu, idan akayi mutuwa a gari ko unguwa sai wasu jama'a koda 'yan kadanne daga cikin mutanen wannan unguwar suka tsayu sukaima wannan gawar sallah to shikenan babu zunubi ko laifi akan sauran jama'a wadanda basuzo akayi wannan sallar dasu ba, Amma mutane guda biyu sukuma ba dole bane sai anyi musu sallar gawa. Nafarko shine yaro qarami wanda bai balaga ba, idan yaro karami ya rasu to ba dole bane sai kunyi mishi sallah, kuna iya rungumar gawar kawai kuje ku birneta ba tareda kunyi mata sallah ba, amma dai babu laifi idan kunyi sallar saboda akwai gagarumin lada wanda ake samu idan akayiwa gawa sallah kunga sai ku rabauta da wannan ladan, na biyu kuma shine shahidi wanda ya mutu a fagen jihadi shima wannan ba dole bane akanku sekunyi masa sallah, amma dai shima din kuna iya yin masa sallan dan ku samu ladanda ake samu bawai saboda yin sallar wajibi bane****_
      _Sannan kuma wannan sallar anso yazama ansamu a qalla sahu uku koda kuwa mutanen basuda yawa koda basu wuce mutane gomaba inso samune arabasu zuwa sahu uku, inkuma sunyi yawa to ana iya qara yawan sahun yafi uku*****_
      _Kuma ya halasta ayima gawa sallah acikin masallaci, amma bai halasta ayi sallar a tsakanin qaburbura ba, wato qabarine guda biyu ko sama da haka sai a ajjiye gawa a tsakaninsu sai ayimata sallah anan wajan wannan bai halastaba kenan dai zamuce baya halasta ayima gawa sallah acikin maqabarta****_
     _Sannan kuma idan gawar namijine to limamin zai tsayane saitin kansa idan kuma mace ce liman zai tsaya tsakiyarta daidai saitin qugunta****_
      _Yadda akeyin sallar kuwa shine: Anayin kabbara hudu, ko biyar ko shida ko bakwai ko takwas ko tara, amma anfi yin guda hudu sedai ana duba darajar mamacin da irin gwagwarmayar da yayi wajen cigaban addini sai ayi masa kabbarorin gwargwadon yadda akaga ya kamata walau biyar ko shidan har zuwa tara****_
       _Amma yanada kyau shi liman kafin afara sallah ya gayawa mutane cewa kabbara kaza zamuyi, sedai kuma fadin hakan ba dole bane akan liman amma dai kyautatawace dan susan abinda zakayi, sannan kuma yanada kyau kagaya musu bayan kowacce kabbara ga abinda ake karantawa saboda mafiya yawan mutane sallar kawai sukeyi amma basusan mene ake fadi abayan kowacce kabbara ba, wannan kuma yafarune saboda irin yadda mutane mukayi sakaci da karatu muka kauracewa malamai babu ruwanmu da yin sallah kamar yadda Annabi (s.a.w) ya koyar kawai dai munayin sallah ne kamar yadda mukaga wadansu mutane sunayi, wanda kuma hakan babu shakka kuskure ne yazama wajibi akanmu lallaine mutashi munemi ilimin addininmu saboda yazama duk ibadarda zamu aikata to munayintane akan basira dakuma haske na ilimi****_
        _Hujja kuwa akan cewa ana yin kabbarori sama da hudu a sallar gawa daga ciki akwai hadisi wanda Imamu Muslim ya ruwaito acikin littafinsa hadisi mai lamba 957, Abu Dawuda 3181, Tirmizi 1028, Ibnu Majahi 1505****_
       _Hujjarmu kuma akan cewa anayin  kabbarbari masu yawane da gwargwadon irin gudun muwarda mamacin yaba addini, Akwai hadisin Sallar gawar Imrana Dan Hussaini wanda Aliyu dan Aby Dalib ne yayi masa kabbarori tara, gakuma sallar gawar Sahlu dan Hanif wanda shima dai Aliyu dinne yayi masa sallah da kabbarori shida, sannan ya fuskanci mutane yace aishi Sahlu ya halarci yaqin badar, wannan hadisin yana cikin Ahkamul Jana'iz shafi na 113, Har ila yau kuma akwai sallar gawar Abu Qatada wadda itama dai Sayyidina Ali ne yayi kuma yaimasa kabbara bakwai shima Abu qatada ya halarci yaqin badar****_
      _Hakadai sayyidina Aliyu yakasance yanayin kabbarori shida zuwa sama akan duk sahabinda ya halarci yakin badar, amma sahabinda baije badar ba Aliyu yanayin masa kabbara biyar ne, Tabi'i kuma wanda ba sahabi ba Aliyu yanayi masa kabbara hudu****_
      _Kankat kuma idan muka duba hadisin Sallar gawar Sayyidina Hamza Annabi (s.a.w) yaimasa kabbarori guda tara shima, Imamu Dahawi ya ruwaito wannan acikin Sharhu Ma'anil Athar mujallad na farko shafi na 290*****_
=
=
_Zan tsaya anan saikuma darasi nagaba idan Allah yakaimu***_
.
_Almajirinku ne kamar kullun_
.
```Jameel Alhassan Haruna kabo```
.
_(Abu khausar)_
.
 .
Allah ta,ala ya tsaremu
.
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook tawannan hanyar
https:/t/m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.

Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illa h anta astagfiruka  Wa,atubu ilaika
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support