Tufka da Warwara!!! Daga Dr.Muhammad Rabi'u R/lemo ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Sunday, 1 July 2018

Tufka da Warwara!!! Daga Dr.Muhammad Rabi'u R/lemo

*TUFKA DA WARWARA!!!*
Daga👇🏽
*Dr. Muhammad Rabi'u R/ Lemo*

Kullum ihu suke suna siffata malamai masu kira zuwa ga sunnah da bin tafarkin magabata da Yan Ikhwan, suna kira a nisance su, a nisanci majalisansu da wuraren karantarwarsu da wa'azinsu, amma su suna cikin jami'o'in da suke cike da yan Ikhwan din na hakika, kai! Har ma da wadanda suke zagin addinin da masu addinin, suna zama aji su karantar da su, amma su daidai suke yi, su ne salaf, alhali da yawa daga cikin malaman da suke suka da batawa suna sun yi karatu ne wurin manya-manya malaman sunnah, sun halacci majalisan su, sun zauna da su.
Haka nan da zaka dawo tarihin wadannan masu ihun ba a kan salafiyya malaman mu suke ba, zaka taras mafi yawancinsu ba su fahimci addini da ilimin addini ba, sai ta hanyar wadannan malamai ko almajiransu, su ne suka kama hannunsu zuwa ga ilimi da sunnah, amma yau su ne yan Ikhwan, wanda da zaka tambaye su tsakani da Allah, tunda kuke karatu wurinsu ko wurin almajiransu, sun taba kiranku ga wata kungiya wai ita Ikhwan, za su ce maka, a'a. To ta yaya yanzu suka zama yan Ikhwan.

Na rantse da Allah babu wani abu da suke sukan malaman mu da shi, suke siffata su da yan Ikhwan saboda shi, face sai ka samu, su da malaman da suke ganin su ne kadai yan salafiyya suna cikin irin wannan abun.

Dan uwa ka maida hankali ga karatunka, ka watsar da rudu da hayaniya.
Allah ka jikan malaman mu, wadanda suka kare rayuwarsu wajen yada sunnar Annabinka (S.A.W) irin su :  Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, sheikh Isma'il Idris, Sheikh Ja'afar, Sheikh Albani Zari'a, da sauran malaman Sunnah. Ameen.

Daga
*ZAUREN FIQHUS SUNNAN* / *MINBARIN SUNNAH*
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support